Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF
Published: 1st, April 2025 GMT
Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar ficewa daga Rundunar haɗin Kan Sojojin Kasashe Tafkin Chadi (MNJTF) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chad. Sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin na gwamnati kuma Reuters ta ruwaito, ta zo ne a lokacin da Nijar ke mai da hankali kan tsaron man fetur a cikin ƙasar, sakamakon tashin hankali na cikin gida.
Rundunar MNJTF, wadda ta ƙunshi Sojoji daga Najeriya, da Chadi, da Kamaru, da Nijar (a baya), an kafa ta ne a shekarar 1994 don magance barazanar tsaro a yankin. An sake farfaɗo da rundunar ne a shekarar 2014 domin yaki da Boko Haram, kuma ta taka muhimmiyar rawa a yaƙi da ta’addanci. Ficewar Nijar, wadda ta kasance muhimmiyar mamba, ya haifar da damuwa game da tasirin aikin rundunar, musamman yayin da ƙungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da yin barazana.
Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da Faransanci Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A NijarShugabannin Soja na Nijar, waɗanda suka karbi mulki a shekarar 2023, sun ƙara nuna sabon tsarin tsaro na Kaɗaitaka bayan sun fice daga ECOWAS a shekarar 2024 tare da Burkina Faso da Mali. Ko da yake gwamnatin Nijar ta yi alƙawarin ƙarfafa tsaron cikin gida, har yanzu tana fuskantar ƙalubale, ciki har da hare-haren ‘yan ta’adda da barazana ga kayayyakin more rayuwa kamar bututun man fetur na Agadem.
Kawo yanzu, MNJTF ba ta yi magana kan ficewar Nijar ba, amma wannan yunƙuri na iya haifar da tasiri mai yawa kan yadda ake gudanar da yaƙi da ta’addanci a yankin Tekun Chad.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Nijar
এছাড়াও পড়ুন:
Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.
Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali ya jaddada hakan ne a yayin jawabinsa a wajen wani taron tuntuɓa tsakanin ’yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a Jihar Kaduna.
Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasaA cewar ministan, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala.
Wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labarai ta fitar ta ambato ministan yana cewa “amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100.”
A 2024 Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau ɗin.
Kazalika, ministan ya ce Gwamnatin Tarayyar ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na Jihar Borno zuwa garin Aba na Jihar Abiya.
“Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai,” in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba.
Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.