Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF
Published: 2nd, April 2025 GMT
Alƙaluman Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce Isra’ila ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 cikin kwanaki 10 da suka gabata a hare-haren da suke ci gaba da kai wa sassan Gaza.
Alƙaluman da UNICEF ta fitar ta ce a jimilla ƙananan yara fiye da dubu 15 ne Isra’ilan ta kashe cikin kusan watanni 18 da ta shafe tana yiwa yankin na Gaza luguden wuta, kuma daga lokacin da ƙasar ta katse yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninta da Hamas ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 tare da jikkata 609.
A cewar UNICEF galibin ƙananan yaran da Isra’ila ta kashe, na rayuwa ne a sansanonin wucin gadi bayan da hare-haren ƙasar ya rusa gidajensu tare da tilasta musu barin muhallansu.
Cikin adadin yaran har da tarin waɗanda Isra’ilan ta kashe suna tsaka da bukukuwan Sallah wato a ranar idi da washegari, galibinsu sanye da tufafi da kuma adon sallah kamar yadda hotuna suka nuna.
A cewar UNICEF yanzu haka akwai jumullar ƙananan yara fiye da dubu 34 da Isra’ilan ta jikkata, cikinsu har da waɗanda yanayi ke nuna yiwuwar sai an yanke musu wani sashe na jikinsu, a dai dai lokacin da ake fuskantar ƙarancin alluran kashe raɗaɗin ciwo a zirin na Gaza mai fuskantar ƙawanya.
Wannan alƙaluma na WHO na zuwa a daidai lokacin da Isra’ila ke amsa laifin cewa tabbas sojojinta ne suka buɗe wuta kan motar jami’an agaji kodayake Amurka ta ce laifin Hamas ne.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ƙananan yara da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu.
A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu.
Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da:
Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ”samar da ƙasashe biyu” Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba
Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun da Birtaniya ke da su kan Hamas da suka haɗa da:
Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Sakin duka sauran Isra’ilawan da take riƙe da su Amincewa ba za ta saka hannu a tafiyar da gwamnatin Gaza ba Miƙa duka makamantaBBC/Hausa