2025-10-13@20:16:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8037
«da wannan cuta»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Wasan Kalankuwa A Nijeriya, 1977 A gwamnatance a wannan kasa, an fara shirya manyan bukukuwan nuna fasahohinmu da aladunmu na-dauri, cikin Shekarar 1977 a Legas. Wanda aka fara gudanar da taron, daga 15 ga Watan Janairu, zuwa 12 ga Watan Farairun Shekarar 1977. A farkon lamari, an niyyaci ci gaba da shirya bikin na baje-kolin al’ada ne a duk Shekara, da niyyar samar da hadin-kai a tsakanin jama’ar Kasa bakidaya. Da farko an kira bikin ne da FESTAC ’77, daga baya aka koma kiransa da NAFEST (National Festibal of Arts and Culture). Saboda muhimmancin irin wadannan bukukuwa, lokacin da aka fara shirya shi a wannan kasa, an sami mahalarta taron ne daga mabanbantan kasashe har kimanin hamsin da biyar (55)....
Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya kaddamar da wasu sabbin motocin alfarma masu kujeru 18 guda 50, domin inganta ayyukan zirga-zirgar jama’a na jihar. Da yake jawabi a wajen kaddamar da bikin a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Lawal ya bayyana ci gaban a matsayin wani sabon babi a tarihin sufuri na Zamfara. A cewar Gwamnan, motocin bas din suna da kayan kariya na zamani da na jin dadi, wadanda suka hada da na’urorin sanyaya waje da sauran kayyakin jin dadin matafiya. Dokta Lawal ya bayyana cewa, da gangan aka samu jinkirin tura motocin bas din bayan isowarsu, inda ya ce gwamnati ta fara samar da tsare-tsare na sa ido da kuma bin diddigi don...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan. A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu. Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci. Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi. A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo...
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar. Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan. Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala...

Shugaban Gidauniyar Malala, ya jaddada kudirin gidauniyar na bunkasa ilimin yara mata a fadin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya. Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da manufofin Gidauniyar gaba. Ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da cibiyoyin gargajiya domin bunkasa samun ilimi da karfafawa ‘ya’ya mata samun damar da suke da ita. A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yabawa gidauniyar Malala bisa ci gaba da tallafawa wajen inganta ilimin yara mata, musamman a Arewacin Najeriya. Sarkin ya yi...
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ofishin Kano, ta gudanar da wani taron kara wa masu yi wa kasa hidima na NYSC aiki a karkashin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (EMVs). An zabo mahalarta taron ne daga kungiyoyin ci gaban al’umma (CDS) a kananan hukumomin Tarauni da Dawakin Kudu Kano. An tsara horon don ƙarfafa ilimin membobin ƙungiyar a matsayin wakilai na gaba na rage haɗarin bala’i da amincin al’umma. Da yake jawabi a lokacin bada horon, shugaban ayyuka na hukumar NEMA Kano reshen jihar Jigawa, Dakta Nura Abdullahi, ya bukaci jami’an tsaro da su ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da koyo. Mahalarta taron sun nuna haɗin kai mai ƙarfi a duk...
Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar. Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce an boye magungunan ne a cikin fakiti 35 na Polyglycine da kuma allunan Tramadol 28. Yayin da yake mika haramtattun magungunan ga wakilin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, Konturola Dalhatu Abubakar, ya ce abubuwan na da illa ga lafiya da suka hada da lalata gabobi, jaraba, da rashin natsuwa, musamman a tsakanin matasa. Abubakar yayi gargadi game da illolin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Muna tabbatar da inganta tsarin na PCS domin a kara tabbatar da karfafa gasa a fadin diniya a fannin na sufurin Jiragen Ruwa na NPA wanda hakan zai kuma kara samar da damar janyo masu zuba hannun jari daga waje na kai tsaye da kuma kara karfafa tattalin arzikin kasar, a nan gaba,”. A cewarsa, za mu ci gaba da kulla hadaka domin mu cimma burin da aka sanya a gaba, na kara inganta ayyukan Hukumar ta NPA. Ya ci gaba da cewa, a rabin zangon farko na shekarar 2025, ingancin da aka samar a bangarorin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar sun bayar da gudunmawar da ta karu, zuwa kaso 19.6 a fannin fitar da kaya waje, da ba su shafi...
Ƴan ƙasar Congo sun fara mayar da martani kan hukuncin kisa da Babbar Kotun Sojin Ƙasar ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila ranar Talata a bayan idonsa, sakamakon samunsa da laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa. Joseph Kabila mai shekaru 54, ya mulki jamhuriyar Demokradiyar Congo tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019 lokacin da ya mika mulki ga shugaba Felix Tshisekedi da ya gaje shi. Baya nan cikin kotu, lokacin yanke hukucin a ranar 30 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki, saboda yana can makwabciyarsu Rwanda inda yake zaman gudun hijirar siyasa shekaru biyu da suka gabata. Yayinda magoya bayan shugaba Tshisekedi ke yabawa matakin, wasu masana siyasa da ƴan adawa na kira da a yi taka-tsan-tsan. Jam’iyyar PPRD...
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
Lamidon Akko da ke jihar Gombe, Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya nada Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu, sarautar Sarauniyar Yaki a masarautar. Basaraken dai ya karrama uwargidan shugaban ƙasar ce a ranar Alhamis a wani biki na musamman da ya gudana a fadarsa. An gudanar da zangar-zangar goyon bayan Kwamishinan ’Yan Sanda a Kano Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku A cewar basaraken, ya ba ta sarautar ce domin yabawa da gudummawar da take bayarwa wajen kare marasa ƙarfi tare da tallafawa mata da yara a fadin ƙasar nan A yayin ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar Gombe, Remi Tinubu ta kuma ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative Flow With Confidence, wani muhimmin shiri na...
Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin yau. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”. Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya. Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar. “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka kyale mana CP.” Mun kama wani mahaifi kan yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa Iraƙi — NAPTIP Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku Zanga-zangar na zuwa ne dai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya caccaki Kwamishinan ’Yan Sandan kan ƙaurace wa farerin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata. Yayin da yake jawabi a bikin da...
Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama wani mahaifi yana yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Mai magana da yawun hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi Sanarwar ta ce mahaifin na daga cikin aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane waɗanda aka cafke a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. TRT ya ruwaito Adekoye na cewa an kuɓutar da mutum 24 a yayin aikin bisa jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello wanda...
A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa. Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance cikin kwanciyar hankali da bin doka da oda, inda masu zanga-zangar ke jaddada muradin su na CP Bakori ya ci gaba da rike mukaminsa da kuma ci gaba da aikinsa ba tare da cikas na siyasa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya musanta cewa yana son ya janyewa wani takara saboda matashin ɗan takara kafin zaɓen 2027. A baya dai tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban Ƙasa a 2027. An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar Atiku dai ya fice daga Jam’iyyar PDP bayan ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen da ya gabata. A watan Agusta, Atiku Abubakar da wasu ’yan siyasa na adawa da suka haɗa da: tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon Gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi da dai sauransu, sun koma jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da aikata sabbin kura-kurai tare da jaddada cewa duk wani hari da za a kai wa Iran zai fuskanci martani mai tsauri fiye da martanin Alkawarin Gaskiya na baya. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki matakin soji da na siyasa bai daya dangane da tunkarar barazanar da take fuskanta da kuma matakin da ya biyo bayan sake maido da takunkumin da kare kan kasarta, a daidai...
Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa da yake hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar da cewa, da sanyin safiyar ranar Larabar nan, sun kai hari kan jirgin (MINERVAGRACHT) da makami mai linzami a mashigin tekun Aden. Sanarwar da Rundunar Sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Sojojin ruwan kasar sun kai wani samame na soji kan jirgin Ruwan na (MINERVAGRACHT) saboda kamfanin ya keta dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye. Sanarwar ta bayyana cewa an kai harin ne a mashigin tekun Aden tare da wani makami mai linzami, wanda ya yi sanadin harbo jirgin kai tsaye tare da kama jirgin. Yanzu yana cikin...
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza. Lazzarini ya ce ta hanyar dandalin X, “A takaice ana kashe mutane 100 a kowace rana a Gaza, sakamakon farmakin da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa ko kuma harbe-harbe a wuraren rarraba abinci da gidauniyar agaji ta Gaza ke gudanarwa.” Ya ci gaba da cewa, “A lokaci guda kuma, wasu na mutuwa saboda yunwa ko kuma rashin kula da lafiya”. Lazzarini ya kara da cewa...
Jami’ar Tianjin wadda aka kafa a shekarar 1895 a matsayin jami’ar Peiyang, ita ce jami’ar zamani ta farko ta kasar Sin kuma ta yi na’am tare da amsa sunanta na yanzu ne a shekarar 1951. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani da ‘Akuskura.’ Ko wanne buhu na dauke da kwalabe 350, adadinsu ya kai kwalabe 2,450, wanda kudinsu ya kai ₦2,450,000. SP Kiyawa ya kara da cewa, bisa hadin gwiwar hukumomin tsaro, “Rundunar ta mika wadanda aka cafken da kayayyakin su da darajarsu ta kai N120,000,000 ga hukumar NDLEA, ta jihar Kano, domin ci gaba da bincike.” Hakazalika, jami’an rundunar sun kama wasu fitattun...
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Sin tana matukar bayyana takaicinta da kuma nadama a kan matakin da kasar Amurka ta dauka a baya, kan daftarin kudirin kwamitin sulhun MDD da aka tsara da nufin magance matsalar jin kai a zirin Gaza. A jawabin da ya yi kan amfani da hawan kujerar na ki a wajen muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Fu ya ce, kasashen duniya sun dade suna yin gagarumin kira na tsagaita bude wuta da dakatar da yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula da haddasa masifar tabarbarewar jin kai, inda hakan ke dakushe lamiri da tausayin bil’adama da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta yi wata babbar nasarar kama masu baiwa ’yan bindiga makamai da kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi da kuma dillalan makamai ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban a faɗin jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, jami’an ’yan sanda da ke aiki da sashen bayanan sirri sun kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Franklin Ozo a Zariya. Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa An kama shi da ƙunshin ƙwayoyin Exol guda 500, na miliyoyin Naira. “Bincike na farko ya nuna cewa,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ganau sun ƙara da cewa a lokacin da aka shaida wa matar cewa Yelwa ba ta nan, sai ta koma mashigar gidan ta kwarara wa kanta man fetur tare cinna ashana wanda hakan ya janyo wuta ta tashi. Nan take lamarin ya janyo hankalin mutanen da suke kusa da wurin inda suka yi ƙoƙarin kashe wutar amma lamarin ya ƙazanta. Daga baya kuma aka kwasheta zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda daga bisani ta rasu sakamakon ƙonewar da ta yi. An kuma ce marigayiyar ɗiyar tsohon wani alkalin kotun Shari’a a Bauchi ce, wacce ta taɓa yin aure har da ‘ya’ya. Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil a ranar Alhamis...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin...
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja. Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta. Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja. Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu....
Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Kungiyoyin Falasdinawa, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Turai sun bi sahu inda sukayi tir da harin baya bayan nan da aka kai wa jirgin ruwan Global Sumud Flotilla a cikin ruwan kasa da kasa. Hamas ma ta yi Allah wadai da farmakin kan Global Sumud Flotilla a iyaka da Gaza wanda ta danganta a matsayin “laifi na fashin teku da ta’addanci kan fararen hula”, tana mai kira ga “dukkan masu kare ‘yanci a duniya” da su yi Allah wadai da harin. Kungiyar Jihadin Islamic ta Falasdinu...
Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23. An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya, cin amanar kasa, azabtarwa, da kuma laifukan yaki, a cewar hukuncin da kotu ta yanke a Kinshasa, babban birnin kasar. An fara shari’ar tasa ne a watan Yuli, bayan da majalisar dattawa ta tsige masa rigar kariya a watan Mayu, bisa zarginsa da hannu a ta’asar da ‘yan tawayen M23 suka aikata a lardunan gabashin Congo. Kotun ta ce Mista Kabila “ya gudanar da tarurrukan...
Akalla Falasdinawa 44 ne sukayi shahada a yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Laraba a wasu jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, a cewar shaidu da majiyoyin lafiya. Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan wasu gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke birnin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 5 tare da jikkata wasu da dama, wasu ma sun makalle a karkashin baraguzan gine-gine. Wasu mutane 11 kuma sun yi shahada, sannan wasu da dama sun jikkata a harin bam din da aka kai a makarantar Al-Falah da ke unguwar Al-Zeitoun a kudu maso gabashin wannan birni. Makarantar tana dauke da iyalai da suka yi gudun hijira. A...
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya. Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba. NAPTIP ta kama mahaifin da ke ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi ci-rani Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027, sai ya ce lokacin tattauna hakan bai yi ba. Ya ce, “Lokacin hakan bai yi ba tukuna. Idan lokaci ya yi, zan yanke shawara. Abin da muke yi yana da amfani ga kasa....
Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar. “Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi. Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba. Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi. Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji,...
Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan. Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60 a birnin Geneva, wakilin kasar Iran Ali Bahreini ya yi ishara da rahoton da kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan yankin Falasdinu da ta mamaye a watan Satumba, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukumar, wacce ke binciken abubuwan da suka faru tun ranar 7 ga Oktoba 2023, ta gano...
Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama akalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja. Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar diyarsa zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraq. Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar safarar...
Kungiyoyin Kare Muradun Arewa, wato Arewa Defence League, sun fitar da sanarwar da suka kira October Declaration, wadda ta tanadi matakai na gaggawa don magance matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kalubalen rayuwa a Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar, ya bayyana hakan a taron dabarun da aka gudanar a Arewa House Kaduna, inda ya ce “lokacin alkawura marasa amfani ya wuce, wannan sanarwa kuwa ita ce alkawarinmu ga mutanen Arewa.” Ya yi gargadi kan karuwar ta’addanci da ‘yan bindiga, rashin aikin yi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ya danganta da gazawar shugabanci da kuma rashin wakilci nagari. A cewarsa, kungiyar ba ta da manufar ballewa daga kasa, amma akwai gaggawar bukatar sabuwar...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. “Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar...
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mai da jihar Gombe ta zama cibiyar zuba jari da ci gaba mai dorewa, wanda aka dora a kan shirin ci gaban jihar na shekaru 10 (DEVAGOM). Alh Inuwa Yahaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin sa, da suka hada da inganta harkokin...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar. A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata. “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa. Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su. ...

‘Yan siyasa a Nijar sun nemi da su yi aiki tare domin tabbatar da ba a samu cikas a zaben kananan hukumomi ba
An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe. Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da wata tangarda ba, tare da shirye-shiryen da tuni aka yi nisa. Mai ba Gwamnan Jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin siyasa Alh Mohammed Nma Kolo ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna. Alh Nma Kolo ya kuma tunatar da su cewa a kowace gasa dole ne a samu wanda ya yi nasara...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa. Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...

Kwara ta bukaci a sanya ido sosai, yayin da jami’an tsaro ke kara kai hare-hare a maboyar masu garkuwa da mutane
Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman. A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su. “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata. Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya. Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja. Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu. Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa. Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu. Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Ya rasu bayan a ranar Laraba, bayan fama da ciwon ƙoda. Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar marigayin. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan ya ce Julius Ishaya, mutum ne nagari mai basira da jajircewa. Hakazalika, ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jam’iyyar APC a jihar, musamman kafin kafa gwamnatinsa. Ya ce a lokacin da Ishaya yake Kwamishinan...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya. Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki? Wannan shine batun...
Aƙalla mutum huɗu suka rasu yayin da aka sace wasu tara a wani hari da ’yan bindiga suka kai a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Magama; ciki har da garin Ibeto a Jihar Neja. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa mutum huɗu aka kashe, an jikkata wasu 11, sannan an yi garkuwa da mutum tara. Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Daga cikin waɗanda aka sace har da wanda ya wallafa rubutu a Facebook kan hare-haren ’yan bindiga a yankin, Barista Isyaku Muhammad Danjuma. Rahotanni sun nuna cewa wasu masu bai wa ’yan bindiga bayanai ne suka sanar da...
Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki a kan jiragenta da ke kan hanyar isa Gaza domin kai kayan agaji, inda suka lalata kamarori da kuma sauran kayan ayyukan fasaha da suke cikin wasu daga cikin jiragen Ruwan, sannan kuma suka killace su. Baya ga haka kuma sun kama dukkanin mutanen da suke cikin wasu jiragen sun tafi da su. Sanarwar ta ce, kyamarorin da ke cikin jirgin sun samu matsala, sannan sojojin Isra’ila sun shiga jiragen ruwa da dama, inda suka umurci jiragen da su karkata zuwa tashar jiragen ruwa ta Asdod da ke karkashin ikon su. Rahotanni sun tabbatar da...
Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun bayan da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka koma yakin kisan kare dangi a ranar 18 ga watan Maris ya kai 13,280, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 56,675. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 51 ne suka yi shahada wasu 180 kuma suka jikkata a zirin Gaza. A halin da ake ciki dai, wani adadi mai yaw ana wadanda abin ya shafa...
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku: Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys. Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya farkewa baƙin ƙwallonsu, yayin da Goncalo Ramos ya ci ƙwallon ƙarshe kuma wacce ta bai wa PSG nasara a mintin ƙarshe na wasan. Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi Li Qiang Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Algeria Da wannan nasarar da PSG ta samu ya sa ta koma matsayi na 3 a teburin gasar Zakarun Turai yayin...
Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.” Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki. A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya...
A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba. An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...

A yau sharhin namu zai yi muku Magana ne game amincewa da falasdinu a matsayin kasa da wasu kasashen turai suka yi a baya bayan nan ciki har da birtaniya da kasar Faransa, sai dai amincewa da kasar falasdinu ci gaba ne babba mai cike da tarihi amma haka
A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai, hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi, wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani, makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari, Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4,...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
“Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima. Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba. Ya ce wannan lamari babban rashi ne, kuma gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Ibaji gaba ɗaya. Gwamna Ahmed Usman Ododo, ya aike ta’aziyyarsa, inda ya ce gwamnatin jihar na tare da al’ummar Ibaji a wannan lokaci...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025. Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sanarwar ta ce matakin na cikin tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya a lokacin kakar bana, wanda manoma ke girbe amfanin gonarsu. Daga cikin ƙa’idojin da aka kafa akwai hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe...
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa na sojojin kasar da kuma na rundunar IRGC a lardin Hurmuzgan. Musawi ya ganewa idanunsa makamai na kariya da kuma na kai hare-hare kan makiya wadanda rundunonin ruwa a bangarorin biyu suke da shi da kuma lafiyar sojojin, inda ya bayyana amincewar sa da shirye-shiryen nasu. Musawi ya kara da cewa daga karshen kallafeffen yakin kwanaki 12 wanda HKI da kuma Amurka suka dorawa kasar...
Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza, duk tare da wadannan hattsurran. Labarin ya kara da cewa, jirgin Alman, ya gamu da hare-hare daga yahudawan wanda ya tilasta masa jada baya zuwa wani waje. Banda ya an yanke dukkan kafafen sadarwa da waje. Gwamnatin yahudawan dai sun sha alwashin hana dukkan jiragen Ustura isa gaza, kuma ta bayyana cewa ta tura jiragen ruwan yaki, wadanda suka kama dukka mutanen da suke cikin...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa. Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka gudanar a jihar. A bisa al’ada dai Gwamna kan jagoranci hukumomin tsaro wajen gudanar da faretin bikin ranar a duk ranar daya ga watan Oktoba. To sai dai a bana, ba a ga Kwamishinan ’Yan Sandan na Kano ba, sannan babu ko dan sanda daya a wajen bikin. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sojoji sun kama ’yan sandan bogi da motoci...
Dakarun sojin Najeriya sun kama wasu mutum biyu da ke sanye da kayan ’yan sanda dauke da motoci biyu kirar Hilux da ke makare da tabar wiwi a jihar Taraba. Dakarun rundunar sojojin ta shida tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ne suka sami nasarar cafke mutanen bayan samun sahihin bayanan sirri. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya An haifi jariri da ‘fuska biyu’ a Bauchi An cafke su ne a tashar Takum da ke karamar hukumar Wukari, suna sanye da kayan jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma. An gano cewa motocin biyu kirar Toyota Hilux da ake tuhuma cike suke da kayan da ake zargin tabar wiwi ce. ‘Yan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayya ta ce Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta amince da janye yajin aikin da take yi, bayan zaman sulhun kwanaki biyu da aka gudanar tare da shugabannin matatar man Dangote. Zaman sulhun da aka gudanar a ranakun 29 da 30 ga Satumba, 2025, ya gudana ne a karkashin jagorancin Ministan Kwadago da samar da Ayyukan Yi, Dr. Mohammed Maigari Dingyadi, tare da halartar manyan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, da wakilan kungiyoyin kwadago. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Abin da ya faru a zaman sulhun PENGASSAN da Matatar Ɗangote A cikin sanarwar da aka fitar bayan kammala zaman, Minista Dingyadi ya ce yajin aikin na PENGASSAN ya biyo bayan sallamar...
Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi shahada a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba, 2024, a wani hari da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a yankin Dahiyeh da ke kudancin birnin Beirut. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Pars Today cewa, Shahid Hasan Nasrallah ya jagoranci kungiyar Hizbullah tun a farkon shekarun 1990, kuma...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar ta shiga sabon salo na gyaran tattalin arziki, kuma matsin da ake ciki na dab da wucewa su zama tarihi. A cikin jawabinsa ga ’yan kasa don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce gwamnatinsa ta damu da radadin da mutane ke ciki sakamakon gyare-gyaren da ake aiwatarwa. Sai dai ya jaddada cewa da Najeriya ba ta dauki matakan da ta dauka ba, da tuni ta shiga halin karyewar tattalin arziki. Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Tinubu ya tuna da jaruman da suka...
A wani lamari da ba kasafai ake samu ba, wata mata mai suna Hannatu ta haifi jariri mai fuska biyu da kai daya a babban asibitin gwamnatin jihar Bauchi da ke garin Azare. Mahaifin jaririn, Malam Bala Sa’idu wanda yake a kauyen Magonshi, ya bayyana wa Aminiya cewa wannan haihuwar wata alama ce ta ikon Allah da ke tabbatar da cewa babu abin da Allah ba zai iya ba. Ya ce duk da cewa lamarin ya bambanta da yadda aka saba, amma bai zo masa da mamaki ba. Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya A cewarsa, goyon cikin da matarsa ta yi ya...
Sauran matakan sun haɗa da haramta sayar da amfanin gona kafin makota su kammala girbi da hana girbi da fitar da amfanin gona da dare, kana ya da umarci manoma da makiyaya da su guji ɗaukar doka a hannunsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.” Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun na Kassam sun watsa sanarwar a shafinsa na “Telegram’ da a ciki ya kunshi cewa, sun kai hare-haren ne akan ‘yan mamaya a kusa asibitin Jordan da kudancin unguwar “Tal Hawa” a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma rundunar ta Kassam ta ce ta kai wani harin akan motar soja da ta shiga cikin wata makaranta ta ” Rahibatul-Wurdiyyah” dake Tallul-Hawa.”. Har ila yau dakarun...
Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai linzami, ya kuwa shafi jirgin ruwan kai tsaye, yana kuma Shirin nutsewa. Kakakin sojojin Yemen din ya bayyana harin da cewa an kai shi ne saboda taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta da yi wa kisan kiyashi. Haka nan kuma ya ce za su ci gaba da kai hare-hare akan duk wani jirgin ruwa wanda ya yi kokarin zuwa HKI ta hanyoyin ruwan tekun “Red-Sea”...
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yaba wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira ‘hakurinsu, juriya da kwazo’ duk da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da suke fama da shi. A cikin sakonsa na murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da ya aike ga ’yan kasa, Atiku ya zargi gwamnatin jam’iyyar APC da watsi da al’umma, yana mai cewa sun bar ’yan Najeriya su fama da rayuwa mai cike da kalubale ba tare da kulawa ba. An tura wani mutum kurkuku saboda dabge da naman Dawisu Ina jinjina wa ‘yan Najeriya bisa juriyar ƙuncin rayuwa da suke fuskanta — Atiku Atiku ya ce “’yan Najeriya na fama da tsananin rashin tsaro, karancin abinci,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa. Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ana iya cewa bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar, amma kuma sun bar gibi a fannin haɗin kai da kwanciyar hankali da samar...
A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda game da rahoton ci gaban Sin na 2025 da cibiyar nazarin samar da ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, Guo ya ce ci gaban Sin mai inganci ya samar da damammaki ga duniya. Dangane da furucin Amurka na cewa za ta kara haraji kan katako, da kayan da ake sarrafawa daga gare shi, da ake shigarwa kasar daga ketare, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ba za a samu nasara a yakin ciniki da yakin haraji ba, kuma babu wata hanya ta fita daga ra’ayin ba da kariya ga kasuwa. Game da shawarar da Amurka ta gabatar...
Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su. Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya aikata, wanda ya ta da hankalin maƙwabta da ya shaida musu cewa ya yanka tsuntsayen kuma ya soya har ya ɗebi dabgen. An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya amince da laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda ɓacin ran...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta. A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65 da suka gabata, madugun adawar ya yi zargin cewa, gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da halin ƙaƙanikayi da ’yan ƙasar suka tsinci kansu a halin yanzu. A gaggauta binciko makasan ’yar jaridar Arise TV —Tinubu ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe Wazirin Adamawan ya bayyana damuwa kan yadda ’yan Najeriya ke rayuwa cikin ƙangin talauci, da yunwa, da rashin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida. ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Tinubu...
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan aiki daya tilo na karamci da adalci ya sake farfado da fatan ma’aikatan jinya da yawa a cikin gwamnatin ku da kuma a cikin ajandar sabunta fata na Shugaban kasa,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi. Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu. A cewarta, shirin zai taimaka...
Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da aka kakaba mata zuwa ga damammaki da bunkasa ci gabanta. Ya yi bayanin cewa: “Yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahayoniyya da Amurka suka kakaba wa Iran, wani gwaji ne kan karfin kimiyya da fasaharta. Ya ce: Iran ta fi karfi tare da mai da hankali a bangarorin kimiyya da fasaha.” Arif ya jaddada cewa: Al’ummar Iran suna bin tafarkin shahidai da kuma ci gaba da...