2025-10-31@06:05:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1145

«kasar Rasha»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025Daga Birnin SinKasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata October 7, 2025
    Kasashen Iran, Rasha, Azerbaijan, da kuma Kazakistan sun rattaba hannu kan yarjeniyar samar da tsaro a ruwayen tekun Caspian wadanda suke tarayya a mallakarsu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kwamandojin sojojin ruwa na wadannan kasashe sun rattaba hannu a kan yarjeniyar a yau Laraba a birnin St. Petersburg na kasar Rasha. Kuma sun kara jaddada cewa ba zasu taba amincewa wata kasa a duniya ta shiga yankin da sunan tsaro ruwan tekun ba. Rear Admiral Shahram Irani, babban kwamandan sojojin ruwa na JMI ne ya wakilci JMI a bikin rattabawa yarjeniyar hannu. Ya kuma bayyanawa kafafen ya da labarai kan cewa manufar yarjeniyar ita ce takaita tsaron ruwan tekun Caspian a tsakanin kasashen da suke...
    Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne...
    Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
     Takardar mai kwanan watan Oktoba 6, ta samu sa hannun Prince Peters Adeyemi, babban sakataren NASU, da Comrade Mohammed Ibrahim, shugaban SSANU na kasa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiƁatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci October 7, 2025LabaraiTinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk  October 7, 2025Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025
    Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mai barin gado ya mika ragamar shugabancin hukumar a hukumance ga Misis May Agbamuche-Mbu, wacce za ta zama shugabar riko.Taron ya gudana ne a ranar Talata yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kwamishinonin zabe a hedikwatar INEC da ke Abuja.Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta ArewaMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A NijeriyaAgbamuche-Mbu, wacce itace kwamishina mafi dadewa a hukumar zabe ta kasa INEC, za ta ci gaba da kula da harkokin hukumar zabe har sai an nada sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta.Da yake sanar da ajiye aikin, Farfesa...
    A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
    Tsohon magajin garin Bacelona Ada collaou da sauran masu rajin kare hakkin dan adam yan kasar spaniya dake cikin jiragen ruwan agaji na Sumud Flotilla da Isra’ila ta kama a baya bayan nan, sun yi tir da irin azabartar da su da isra’ila ta yi kuma sun sha alwashin daukar matakin shari’a a kanta, Shi ma shugaban bangaren hagu na jam’iyar podemos ya sanar da shirye shiryen maka prime minister Isra’ila Benjamen na tanyaho a gaban kuliya manta sabo, Matakin shariya da kungiyoyinn farar hula  da sauran jam’iyun siyasa a kasar Spaina ta dauka  yana kara nuna yadda duniya ke yin matsin lamba kan gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma zai sanya bangaren sharia na kasar spain ya gudanar da bincike na...
    Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni da a sake duba farashin kuɗin aikin Hajjin 2026, domin rage nauyin da zai rataya kan alhazai, sakamakon yadda Naira ke kara karfafa kan Dalar Amurka a kasuwa. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya mika umarnin Shugaban kasan ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), inda ya ce a cikin kwanaki biyu hukumar ta fitar da sabon tsarin farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin Kasar a yanzu. Da yake jawabi a fadar shugaban kasa bayan taro da shugabannin NAHCON, Shettima ya ce ya zama dole a samu hadin kai tsakanin gwamnoni da jami’an hukumar alhazai domin tabbatar da tsarin farashi mai sauki da adalci ga maniyyata. Shi ma Sakataren...
    Tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, 2023, da mayaƙan Hamas suka kai wa Isra’ila wanda ya hallaka sojoji sama da 60 , Isra’ila ta fara luguden wuta a Gaza.Tun daga wannan lokacin, yankin ya zama wurin tashin hankali da yunwa, inda mutane da dama ke mutuwa a kowace rana.Tags: FalasɗinawaGazaHamasIsra'ilayaƙiShareTweetSendShare Sadiq Related Kasashen KetareMe Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa? 3 days agoKasashen KetareWadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? 1 week agoKasashen KetareBirtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa 2 weeks ago
    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu.   Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin.   Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana.   Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na...
    Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.   Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar.   Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare.   Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
    Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon  ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya “WFP” ta bayyana cewa: Rage agajin jin kai na barazana ga miliyoyin mutane da suke fama da yunwa a Somaliya Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta yi gargadin cewa: Miliyoyin mutane a Somaliya na cikin hadarin fuskantar yunwa da rashin abinci mai gina jiki, saboda tsananin karancin kudade da ya tilastawa kungiyar ta WFP rage yawan mutanen da take tallafawa da taimakon abinci na ceton rai da sama da kashi biyu bisa uku. A watan Nuwamba, za a tilastawa Hukumar WFP ta rage adadin mutanen da ke samarwa tallafin abinci na gaggawa zuwa 350,000 kawai, wanda ya ragu da miliyan 1.1 a watan Agustan da ya gabata. Wannan...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar da wani sabon rahoto kan cikar shekaru biyu da fara kaddamar da munanan hare-haren Isra’ila a kan al’ummar zirin, inda rahoton ya bayyana cewa har yanzu ayyukan kisan kare dangi na ci gaba da gudana a kan mutanen Gaza. A cewar sanarwar da aka fitar a wannan Lahadi, Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a kan al’ummar Gaza, snnan kuma sama da mutane 76,600 ne aka kashe ko kuma suka bata ba a san makomarsu ba tun lokacin da aka fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. A cikin shekaru biyu, an tabbatar da kashe mutane 67,139, yayin da kusan mutane 9,500 kuma ba a san makomarsu ba, amma...
    Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun.   Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an...
    A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
    Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa: “A cikin baƙin ciki muke alhinin rasuwar Ambasada Muhammad Jabbi Maradun, fitaccen dattijon jiha kuma ɗan jiharmu ta Zamfara na gaskiya.   “An haifi Jakada Jabbi ne a ranar 12 ga Nuwamba a shakrar 1943, a Ƙaramar Hukumar Maradun.   “Ambasada Maradun ya taba zama jakadan Nijeriya a ƙasar Tunisia daga 1999 zuwa 2003.   “Ya yi fice a yunƙurin samar da jihar Zamfara.   “Bayan kafuwar jihar Zamfara, Ambasada Jabbi ya shiga gwamnatin soja ta farko a ƙarƙashin Kanar Jibril Bala Yakubu, inda ya riƙe muƙamin kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido.   “Ayyukan sa na siyasa sun haɗa da jam’iyyun GNPP, NPN, da NRC, kuma ya kasance mai ruwa da tsaki a...
      Mahaifiyar Yilwatda ta rasu a watan Agustan 2025, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, tana da shekaru 83.   Da yake mayar da martani, Atiku ya ce shugaban kasar ya zaɓi ya yi ziyarar jana’izar siyasa maimakon ziyarar jama’ar da taɓarɓarewa tsaro ta shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma  duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
    A ranar 3 ga watan ne hukumar ciniki ta duniya (WTO) ta gudanar da taron shekara-shekara na majalisar kula da harkokin cinikayya karo na uku a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin ta yi amfani da wannan dama domin daidaita wannan batu, inda ta fallasa tare da sukar matakin “harajin ramuwa” na Amurka daga bangare guda da gitta kariyar cinikayya, inda ta yi nuni da cewa, matakan kakaba harajin da Amurka ta dauka sun haifar da illa ga harkokin cinikayyar duniya, kana ta bukaci Amurka ta mutunta ka’idojin WTO, tare da yin aiki da dukkan bangarori don karfafa gudanar da harkokin kasuwancin duniya cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba. Membobi irinsu Indiya, Brazil, Masar da Pakistan sun...
    Turkiyya ta mayar da martani ga shugaban Amurka cewa: Ba za ta daina sayen iskar gas daga kasar Rasha ba Ministan makamashi da albarkatun kasa na kasar Turkiyya Alparslan Bayraktar ya tabbatar a wata hira da yayi da gidan talabijin a jiya alhamis cewa: Kasarsa ba ta da niyyar yin watsi da sayen iskar gas da take daga Rasha. “Ministan a wata zantawa da tashar CNN Turk ya bayyana cewa: Game da Turkiyya ba za ta iya ce wa ‘yan kasarta ku yi hakuri, iskar gas ta kare ba. Ya kara da cewa: “An tabbatar da tsaron iskar gas tana tabbata ne ta  hanyar yin amfani tilas da wadannan hanyoyin, ba tare da nuna bambanci ba a lokacin hunturu mai...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.   Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta.   Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa.    ...
    Shugaban Madagaska Andry Rajoelina ya bayyana cewa gagarumar zanga-zangar da akeyi a kasar, na da nufin “yi masa juyin mulki,” ne. A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Rajaolina, ya yi ikirarin cewa matasan da suka yi gangami a kan tituna, da tun farko suke yin Allah-wadai da katsewar wutar lantarki da ruwan sha, wasu ’yan siyasa ne ke amfani da su. A jawabi na tsawon mintuna ashirin da aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook, wanda shi ne na farko tun soma fara zanga-zangar, Shugaban kasar ta Madagaska ya tabbatar da cewa matasan da ake wa lakabi da ‘’G Z’’, ‘yan adawa” ne ke amfani da su wajen neman kawar da shi daga mulki....
    Firai ministan kasar Beljium Bart De Wever ya fadawa sauran tokororinsa na kasashen turai kan cewa bai amince a yi amfani da kudaden Rasha da aka kwace a kasashen turai don yakar kasar a Ukraine ba, sai tare da wasu sharudda. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wever ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa dokokin kasa da kasa sun hana a kwace kudaden wata kasa mai cikekken yenci, don wata bukata. Kafin haka dai kasashen turai da dama sun gabatar da shawarar kwace dalar Amurka bil;iyon $229 na kudaden ruwan da kadarorin kasar Rasha da ke turai suka samar don yakarta a kasar Ukraine, wannan duk da cewa dokokin kasa da kasa sun haramta...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.   Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.   Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi.   A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo...
    Ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta fadi cewa akalla sama da falasdinawa 66225  ne suka rasa rayukansu, yayin da 168938 kuma suka jikkata a aci gaba da kiran kare dangi da HKI ke yi a yankin gaza tun daga watan oktoban shekarar bara da ta gabata. Akalla fararen hula 77 ne ake kaashewa 222 kuma suke jikkata a duk rana sakamakon hare hare da sojojin Isra’ila ke kawai kan fararen hula marasa karia a yankin Gaza. Fararen hula da dama ne ciki har da mata da yara kanana suka dimauce bayan da HKI ta harba hayaki mai sa hawaye da kuma bomb na hayaki da jirgi mara matuki na HKI ya kai a makarantu da gidaje domin tarwatsa alumma dake...
    A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya. Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake...
    Gwamnatin Rasha ta jaddada cewa: Yarjejeniyar dabarun da kulla da Iran dole ne a aiwatar da ita Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar a yau Alhamis a cikin wata sanarwa cewa: Yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara aiki, tare da tabbatar da cewa kasashen biyu bisa tsarin yarjejeniyar suna fuskantar kalubale da barazana amma ba zasu yi wani tasiri ba. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar ta bayyana cewa: A ranar 2 ga watan Oktoba ne yarjajjeniyar huldar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Iran Masoud Peskov suka sanya wa hannu a ranar 17 ga watan Janairun shekara...
    Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza. Lazzarini ya ce ta hanyar dandalin X, “A takaice ana kashe mutane 100 a kowace rana a Gaza, sakamakon farmakin da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa ko kuma harbe-harbe a wuraren rarraba abinci da gidauniyar agaji ta Gaza ke gudanarwa.” Ya ci gaba da cewa, “A lokaci guda kuma, wasu na mutuwa saboda yunwa ko kuma rashin kula da lafiya”. Lazzarini ya kara da cewa...
    Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai.   Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa.   Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata.   Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya.   Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
    Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya. Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus. Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin  dawo da takunkumai a...
    Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
    A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba.   An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
    Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya.   Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
    Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma isra’ila takai kai hari kan tawagar ta Flotilla , wannan ya zo ne bayan da matukan jiragen ruwa guda biyu suka fitar da bayani cewa Isra’ila ta kai harin kan jiragen ruwansu guda biyu, inda avila yace sojojin Isra’ila sun yi amfani da yakin kwakwalwa ga wasu daga cikin tawagar flotilla inda suka yi musu kawanya Agefe daya mataimakin ministan harkokin wajen kasar Austreliya ya...
      Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.”  Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
    Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].” Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960. A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
     A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato.  Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa; Manyan jami’an diplomasiyyar kasashen uku na turai sun yi wani taron sirri a birnin Moscow, inda su ka gargadi Rasha akan keta hurumin samaniyar kasashen mambobi,suna masu cewa za su iya kai wa jiragen Rashan hari. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” din ya ambato jami’an kasashen na turai da su ka halarci taron suna nakalto wannan gargadin, bisa cewa cikin ganganci ne jiragen na Rasha su...
    Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahkuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja. Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a ranar Asabar din da ta gabata. Sakamakon kuri’ar raba gardamar da ak ayi a ranar 21 ga watan nan na Satumba, ta nuna cewa kaso 89% na wadanda su ka kada kuri’ar, sun nuna amincewa da sabon tsarin mulkin. Har ila yau, wata kididdiga ta nuna cea kaso 86% na wadanda su ka cancanci yin zabe ne su ka kada kuri’a. Jam’iyyun hamayyar kasar ta...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi barazanar rufe Mahautar Akwanga saboda matsalar rashin tsafta. Kwamishinar Muhalli da Albarkatu ta jihar, Magret Elayo, ce ta bayyana hakan a yayin ziyar da ta kai mahautar, bisa wakilcin Babban Sakataren  ma’aikatar, Husseini Babayayi. Elayo ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da ayyuka a mahautar cikin rashin tsafta, lamarin da ta ce yana barazana ga lafiyar al’umma. “Wurin ba shi da tsafta, kuma yana shafar lafiyar al’ummarmu. Gwamnati za ta ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuwar al’ummarmu a Akwanga saboda yanayin wurin bai dace ba da yankan dabbobi,” in ji ta. Ta ce idan ba a gyara ba nan da wata guda, to gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wajen rufe mahautar gaba...
    Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasar, tare da wakilai daga sassa daban-daban, za su ajiye furanni don jinjinawa jarumai da suka sadaukar da rayukansu saboda kasa a filin Tian’anmen. A lokacin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG zai watsa wannan biki kai tsaye.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu ne da za a amince da su ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwar mayar da martani ga ikirarin da kasashen Turai uku da Amurka suka yi na maido da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran. Ma’aikatar ta yi la’akari da yin amfani da hanyar warware takaddama da aka tanada a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa game da...
    Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne daga zargin karya da ake yi wa Iran na karya yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Amurka, da Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da China da kuma Jamus. Wannan shawarar dai ta zo ne duk da irin jajircewar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kan yarjejeniyar, da ficewar Amurka daga cikinta a shekara ta 2018, da kuma kasashen Turai uku,...
    Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
    A cewarsa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya.   Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna, shugabannin addini, da ‘yan jarida saboda muhimmancin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban.   “Gwamnati na matuƙar damuwa wajen tabbatar da ƙarin shiga cikin wannan aikin daga al’umma. Wannan ba game da son ɓangare ba ne; yana game da ƙarfafa dukkan ɓangarorin al’umma Kama daga matasa, mata, manya, da kowane rukuni na jinsi su shiga cikin tsarin dimokiradiyya,” in ji Maiyaki.   Kwamishinan...
    Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda  ruftawar ramin hako ma’adanai. Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, an kuma ci gaba da aikin ceto na fito da mutanen har zuwa jiya juma’a. Wani mazaunin yankin ya ce, an ceto da mutane 13 daga karkashin baraguzai, ana kuma jin cewa da akwai wasu mutane fiye da 100 da suke karkashin kasa. Wani shaidar ganin ido kuwa cewa ya yi, a tsakanin mutanen da sun kai 100 da...
    Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
    Kasashen China da Rasha sun yi kira da a jinkirta mayar da takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kasashen China da Rasha sun bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya kada kuri’a kan tsawaita lokacin sake kakaba takunkumi kan Iran zuwa tsawon watanni shida nan gaba a yau Juma’a. Kasashen China da Rasha sun gabatar da wani daftarin kudiri na hadin gwiwa da ke neman tsawaita dage takunkumin har zuwa ranar 18 ga Afrilun shekara ta 2026. Kasashen China da Rasha sun tabbatar da “ci gaba da hadin gwiwa” tsakanin kasar Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, inda suka yi kira ga bangarorin da ke cikin shirin hadin gwiwa na JCPOA da su gaggauta dawo...
    Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a bangaren na TTP tun lokacin da aka faro sun hada da, sanya ido kan sama da manyan motocin miliyan uku da ke shiga cikin Tashoshin musamman bisa nufin rage cunkoson da kuma sake fitarsu, daga cikin Tashoshin a kan lokaci Ya sanar da cewa, kirkiro da tsarin biyan kudade kan lokaci na shigar motocin cikin Tashoshin hakan ya taimaka matuka, wanda kuma bisa hadakar da...
    Daga karshe,mahalarta taron sun meni a samar da wata kungiya da za ta jagoranci isar da sakon akidojin Bala Usman ga al’umma domin bai kamata a bar irin wannan kyawawan fata na Bala Usman su tafi a banza ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ƴansandan Jihar Delta ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da wani matashi, inda suka karɓi kuɗin fansa na Naira miliyan biyu (₦2m) amma duk da haka suka harbe shi saboda rashin isassun kuɗi a asusun bankinsa. Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka (25), da Uche Okechukwu da Somto Chukwuma, waɗanda suka yi garkuwa da wanda abin ya shafa daga gidansa da ke Ogwashi-Uku. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya bayyana cewa an gano wanda aka sace a cikin daji da ke yankin tare da raunin harbin bindiga a ƙafarsa. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Bayan Sulhu  Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da...
    Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da labarin rasuwar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Barista Solomon Aku Ewuga.   Kakakin majalisar a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Jibrin Gwamna ya fitar, ya bayyana rasuwar mataimakin gwamnan jihar a matsayin babban rashi ga jihar da ma Najeriya baki daya.   Sanarwar ta ruwaito shugaban majalisar na cewa rasuwar tsohon sanata mai wakiltar nasarawa ta arewa, mutuwa ce da ta girgiza al’ummar jihar Egu da ma jihar baki daya ba.   “Bishiyar Iroko ta fado, mai taimakon jama’a kuma fitaccen dan siyasa ya je gida ya huta, Allah ya kara masa yarda.” Inji Shugaban Majalisar.   Kakakin Majalisar Danladi Jatau ya bayyana...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ya yi hobbasar gina Xinjiang na zamani mai ra’ayin gurguzu da ke kunshe da hadin kai, da kwanciyar hankali, da samun wadata, da arziki mai albarka, da raya al’adu da kyautata muhallin halittu, inda jama’a za su ci gaba da rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da samun wadata. Yayin da yake sauraren rahoton ayyukan kwamitin jam’iyyar JKS a yankin Xinjiang da gwamnatin yankin a yau 24 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a kafa tubalin samar da albarkatu da masana’antu, da yin nazari sosai a game da turbar samar da ci gaba mai inganci da ta dace...
    Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang. An amince sosai da cewa, tsarin gudanar da mulkin Xinjiang da kasar Sin ta yi amfani da shi ya gano hanyar da ta dace wajen daidaita ci gaba da bangaren tsaro a yankunan kan iyaka, da kara kaimi ga amfani da zamanantarwar kasar Sin a yankin Xinjiang, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa...
    Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine. Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ce Rasha na nan a kan matsayinta na zakanyar kasa, kuma tana cikin kwanciyar hankali ta fannin tattalin arziki. Peskov ya tabbatar wa manema labarai cewa babban kuskure ne a yadda ake cewa Ukraine za ta iya yin nasara wajen karbe ikon yankunanta da ke hannun Rasha. Bayan ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a New York, Trump ya ce Ukraine na iya kwato dukkan yankunan da ta rasa, inda ya bayyana Rasha a matsayin kyanwar Lami. Ya kuma ce tattalin arzikin Rasha na cikin gagarumar matsala. Tun da farko...
    A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Shawarwari biyu na Turai da na Rasha suna gaban Iran, kuma za ta amince da duk wata mafita ta gaskiya da ke kiyaye muradunta Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana ikirarin cewa; Iran ba ta amincewa da tattaunawa, a matsayin “karya” ne, yana mai tunatar da cewa, Iran na cikin wani yanayi na tattaunawa ta fuskanci farmakin soji na wuce gona da iri. Larijani ya ce: Iran za ta amince da duk wata shawara mai ma’ana da adalci da za ta kiyaye muradunta, yana mai bayyana cewa, “Iran tana nazarin shawarwarin Turai da na Rasha da suka gabatar mata.” Larijani ya tabbatar da cewa: Iran ta amince da duk shawarwarin biyu a kan wasu sharudda,...
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
    A yau talata da yamma ce aka yi jana’izar shahidan Bintijbail na kudancin kasar Lebanon, wanda HKI ta kaisu ga shahada a lokacinda ta cilla makamai masu linzami kan motar da take dauke da su a ranar Lahadin da ta gabata. Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, shahidan mutane 5 biyar ne wadanda suka hada da kananan yara 3 da mahaifinsu da kuma sannan mahaifiyarsu ta ji Rauni mai tsanani, da kuma yar’uwassu wacce itama ta ji Rauni. Almanar ta nakalto cewa shahadar da kuma kissan kiyashin bai karawa mutanen garin ba sai karfin giwa na riko da kasarsu da kuma gwagwarmayansu. Ministan kiwon lafiya Rakan Nasiruddeen tare da rakiyar minister watsa labarai Paul mahaifiyar yaran...
    A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia. Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar...
    Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata. Wannan ne ya sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin inganta ilimi da kuma bai wa matasa damar samun kyakkyawar makoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna. Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan. Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka...
    Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF.   A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar.   Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu.   “A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye.   “Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da...
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar. “Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa. “Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani,...
    Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne,  bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta  su yi aikin koyarwa.” Tsarin na ma’aikatar ilimin ya ƙara jan kunne na da akwai buƙatar tabbatar da cewaana amfani da shi tsarin dokar kamar yadda aka bayyna “a kuma samu dama ta wayar da kan duk masu ruwa da tsaki kan lamarin” a duk illahirin faɗin tarayyar Nijeriya”saboda kar abin ya kawo cikas na jarabawar da ta shafi ƴ aƴ an al’umma.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine din. A kudancin ƙasar ma, hukumomi a Mykolaiv sun bayar da rahoton tashin gobara bayan harin da aka kai kan wasu masana’antu. Yankunan yammacin Lviv da Ivano-Frankivsk ma sun fuskanci gobara sakamakon hare-haren da aka kai masu. Suna kusa da iyakar Poland, inda sojoji suka ce sun tura jiragen sama domin tabbatar da tsaron sararin samaniyar yankin.
    Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, tun farkon yaƙinta da wungiyar Hamas a shekarar 2023. Sun haɗa da: Kashe ’yan ƙungiyar, wanda ya janyo musu lahani a jiki da ƙwaƙwalwa; da kuma ƙirƙirar wani yanayi da gangan don lalata ƙungiyar, da hana haihuwa. Rahoton ya ba da misali da kalaman shugabannin Isra’ila, da kuma abubuwan da sojojinta suka yi a Gaza, a matsayin shaida na aikata kisan ƙare dangi. Ma’aikatar...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta yarda da duk wani aiki na siyasa ko matsin lamba na rashin adalci ba Rafael Grossi, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, a yayin wannan kiran, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, da batun maido da takunkuman da aka kakabawa Iran, da kuma matakin ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a kwamitin sulhu na MDD. Araqchi da Grossi sun cimma yarjejeniya a birnin Alkahira kan sabbin hanyoyin hadin gwiwa...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai. Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya. Ya ce: “Maimakon amincewa da...
    Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York. Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar Falasdinu wani bangare ne na cikakken shirin zaman lafiya da ke tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga Isra’ila da Falasdinu. Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi don tabbatar da wannan karramawa a ranar litinin da misalin karfe 3:00 na rana a birnin New York (9:00 na yamma agogon Paris), yayin wani taron da zai jagoranta tare da yarima mai jiran gado na Saudiyya. Fadar...
    Ya ce ma’aikatar ta tsaya a kan tabbatar da ladabi da bin doka don haka babu wani shugaban makaranta da za a bari yana sabawa doka ko karbar kudade a hannun dalibai da iyaye ba tare da an hukunta shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI.   Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su. Domin sauke shirin, latsa nan
    Rundunar Brigade ta 17 na Sojojin Najeriya da ke Katsina ta raba buhunan takin zamani ga manoma a ƙauyuka shida da ke kusa da sansanin Natsinta, cikin Jibia da Katsina. Kwamandan brigade ɗin, Birgediya Janar Babatunde Omopariola, ya ce an yi hakan ne don ƙarfafa dangantakar sojoji da al’umma, tare da taimaka musu wajen noma, lafiya da ilimi. Ya kuma nemi haɗin kan jama’a wajen bayar da bayanai da sintiri domin tabbatar da tsaro a jihar. A madadin al’umma, shugaban ƙauyen Katoge, Malam Abubakar Bala, ya gode wa sojojin, inda ya bayyana cewa takin zai taimaka wajen bunkasa noma, kuma sun dade suna amfana da tsaro da taimakon sojoji a yankin. Kauyukan da suka amfana da rabon takin sun hada...
      A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci jihar Kaduna  ranar Juma’a 19 ga watan Satumban 2025. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaba Tinubu zai halarci daurin auren  Nasirudeen Yari, ɗa ga Sanata Abdul’aziz Yari, da ke wakiltar Zamfara ta Yamma,  da Amaryarsa Shehu Idris. A yayin wannan ziyara, shugaba Tinubu zai kuma ziyarci Hajia Aisha, matar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidansu da ke Kaduna. Ana sa ran shugaban zai koma Abuja a ranar, nan take bayan kammala ziyarar.   Daga Bello Wakili
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai kamar Iran da Rasha, ya tabbatar da cewa zamanin kebe kai a duniya ya kare. Ya kuma jaddada cewa, wadannan kasashe suna iya samun ci gaba da bunkasa ba tare da bukatar ko dogaro da karfi mai amfani da bangare guda. Shugaban na Iran ya bayyana jin dadinsa da ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu, musamman a fannin sufuri, makamashi, da ayyukan samar da wutar...
    Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak. Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyar, inda bangaren Syria ya gabatar da martaninsa kan shawarar da Isra’ila ta gabatar na cimma yarjejeniyar tsaro, inda ta ce an samu ci gaba a tattaunawar. A baya dai bangarorin biyu sun gana a zagaye na biyu da aka sanar, ban da kuma tarukan sirri da suka gudanar a lokuta daban-daban wand aba a sanar ba, da nufin kulla alaka ta siyasa...
    A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
    A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai zama wani mataki mai matukar muhimmanci a wannan kasa ya yammacin Afirka. Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasa a watan Disamba na 2021, an yi dokar da majalisar Mulki ta soja ta amince da ita, wacce ta kunshi cewa; Dukkanin ‘yan majalisar Mulki ta soja ba su da hakkin tsayawa takara a fadin kasa da kuma a matakin yankuna. Sai...
    Ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wani ba’iraniye dan leken hukumar Mossad ta Isra”ila A safiyar yau Laraba ne ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Babak Shahbazi, dan leken asirin Mossad da aka samu da laifin hada kai da yahudawan sahayoniyya a fannin leken asiri da kuma harkokin tsaro da kuma musayar bayanai da jami’an Mossad. An zartar da hukuncin kisar ta hanyar rataya a safiyar yau bayan kammala matakan shari’a kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin. Babak Shahbazi, dan Rahmatullah, ya yi aiki a matsayin dan kwangilar kere-kere da sanya kayan masana’antu ga kamfanonin da ke da alaka da cibiyoyin tsaro, sojoji, da cibiyoyin sadarwa...
    Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.   Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.   Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...