Rashin Tsabta: Za mu rufe Mahautar Akwanga —Gwamnatin Nasarawa
Published: 29th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi barazanar rufe Mahautar Akwanga saboda matsalar rashin tsafta.
Kwamishinar Muhalli da Albarkatu ta jihar, Magret Elayo, ce ta bayyana hakan a yayin ziyar da ta kai mahautar, bisa wakilcin Babban Sakataren ma’aikatar, Husseini Babayayi.
Elayo ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da ayyuka a mahautar cikin rashin tsafta, lamarin da ta ce yana barazana ga lafiyar al’umma.
“Wurin ba shi da tsafta, kuma yana shafar lafiyar al’ummarmu. Gwamnati za ta ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuwar al’ummarmu a Akwanga saboda yanayin wurin bai dace ba da yankan dabbobi,” in ji ta.
Ta ce idan ba a gyara ba nan da wata guda, to gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wajen rufe mahautar gaba ɗaya.
Kwamishinar ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da sa ido kan ayyukan mahautar har zuwa ƙarshen watan Oktoba domin tabbatar da bin ƙa’idojin tsafta.
A wani labarin kuma, an cafke mutane 112 a ƙananan hukumomi biyar na kudancin jihar saboda karya dokar tsaftar muhalli.
Babban Lauyan Hukumar Tsafta, Abubakar Mohammed, ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama su ne yayin aikin tsaftar muhalli na wata-wata a Lafiya da kewaye.
Ya ce an kama mutane 26 a Ƙaranar Hukumar Lafiya da wasu 26 a Keana, 21 a Awe da 21 a Obi, sai kuma 18 a Doma.
An gurfanar da su a gaban kotun tafi-da-gidanka, inda aka hukunta su gwargwadon laifin da kowanne ya aikata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: mayanka Tsaftar Muhalli
এছাড়াও পড়ুন:
El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauka sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa jami’yyar haɗaka ta ADC.
Komawar El-Rufai jam’iyyar ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027.
An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da OlympiacosA wannan Alhamis ɗin ce El-Rufai ya kammala rajistar zama mamba na jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Unguwar Sarki da ke birnin Kaduna, inda ya yi alƙawarin amfani da jam’iyyar ADC wajen fuskantar abin da ya kira rashin ƙwarewa a jagorancin gwamnatin jihar.
“Ina da cikakkiyar rajista a jam’iyyar African Democratic Congress,” in ji shi a gaban manyan jami’an jam’iyyar, ciki har da Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Yamma, Jafaru Sani, da Sakataren Yi wa Mambobi Rajistar Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Sadiq Yar’adua.
A watan Maris na bana ne dai El-Rufai ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP a wani yunƙuri na shirya haɗin gwiwar adawa, sai dai ya ce tattaunawar da suke yi a SDP ɗin ta gaza haifar da ɗa mai ido wajen cimma muradinsu saboda “tsoma bakin gwamnati da kuma cin hanci da wasu shugabannin jam’iyyar ke yi.”
Da yake jawabi kan siyasar Jihar Kaduna, El-Rufai ya yi kira ga jama’a da su yi rajista da ADC domin “maimaita abin da muka yi a 2015,” yana mai zargin gwamnatin APC mai ci da sakaci da jagorancin al’umma.
“Ina kira ga dukkan ’yan Kaduna masu shekaru 18 zuwa sama da su fito su yi rajista. Da ikon Allah, zamu sake kawar da gwamnatin da ta nuna gazawa.
“Mu da muka taimaka muka ɗora su a kujerar mulki, za mu taimaka wajen dawo da su gida… kafin su wuce kotu,” in ji El-Rufai.