Balaguron Fasinjoji Ta Jirgin Kasa A Kasar Sin Ya Kai Matsayi Mafi Girma A Bikin Ranar Kafuwar PRC
Published: 2nd, October 2025 GMT
A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8.
A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya.
Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake yi na kwanaki takwas zai haifar da karuwar bukatun balaguro sakamakon yawan zuwa yawon bude ido da kuma ziyarce-ziyarcen dangi.
A cewar ma’aikatar sufurin kasar, ana sa ran gudanar da balaguro kusan biliyan 2.36 a duk fadin kasar Sin a lokacin hutun, inda aka kiyasta yawan tafiye-tafiyen a kowace rana za su kai miliyan 295, wanda hakan ke nuna karuwar kashi 3.2 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya
Wani tsohon dan majalisar kasar labanon ya bayyana cewa kasarsa ba ta bukatar wata yarjejeniya da zaa kulla kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da hki take yi , kana yayi gargadin cewa makircin da aka kulla kan kasar siriya aka kai ta kasa irinsa ne ake kullawa akan kasar labanon,
Hussain haj Hassan yace babu wani amfani kara tattaunawa kan wata yarjejeniya da isra’ila tun da ta kasa tsayawa ta yi aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan nuwambar shekarar da ta gabata.
Daga karshe ya nuna cewa gwamnatin dake rike da kasar siriya ta haiati tahrir al sham abokiyar Amurka ce don haka har yanzu isra’ila na ci gaba da wuce gona da iri a yankuna daban daban na kasar siriya gaba gadi,
Yace gwargwadon yadda ka bawa makiya dama gwargwadon yadda zaka kara yin rauni a gabansu, don haka hizbullah da hadin kan kasa su ne kawai wanda za su bada garanti kan tsaro da zaman lafiyar kasar labanon
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci