HausaTv:
2025-11-08@10:09:35 GMT

  Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi

Published: 23rd, September 2025 GMT

A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia.

Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Estonia ta bayyana abinda ya faru da cewa, keta hurumin kasar ne a fili, wanda kuma ya sa kungiyar ta Nato ta yi kakkausar suka, tare da bayyan shi a matsayin tsokana daga Rasha.

Rasha dai tana zaman tsami da kungiyar Nato saboda yakin kasar Ukrainiya wanda ya shiga cikin shekaru na 3 ana yi.

A gefe daya Nato tana ci gaba da aike wa da sojojinta zuwa kasar Poland wacce take makwabtaka da Ukiraniya, bayan da ita ma ta zargi Rashan da cewa ta keta hurumin sararin samaniyarta.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A  Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga  MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025   Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya: Ta Sake Jaddada Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar

Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta na yin watsi da ayyata a matsayin kasa mai take hakkokin addinai da Amurka ta yi.

Da yake kare tarihin Najeriya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce “barazanar Trump na ɗaukar matakin soja ba ta da tushe kuma hakan yana a matsayin kawar da ido ne daga ƙalubalen tsaro masu sarkakiya da Najeriya ke fuskanta,” ya ƙara da cewa “duk wani labari da ke nuna cewa Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan hare-haren da ake kai wa mabiya addini ya dogara ne akan bayanan ƙarya ko maganganu marasa tushe.”

A ranar Litinin, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Olufemi Oluwedi, ya bayyana cewa “Najeriya tana fuskantar ta’addanci, ba kai hari ko cin motuncin Kiristoci ba,” kuma “shugabancin Najeriya yana maraba da taimakon Amurka wajen yaƙi da ta’addanci matuƙar tana mutunta haƙƙinta na yankuna.”

Idris ya ƙara da cewa gwamnatinsu ta samu ci gaba mai yawa a yaƙi da ta’addanci tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023, yana mai cewa “kofar gwamnatin Najeriya ta kasance a buɗe kuma tana son yin aiki kafada da kafada da gwamnatin Amurka da sauran ƙasashe da abokan hulɗa don cimma burin kawar da ta’addanci gaba ɗaya a ƙasar Najeriya.”

Idris ya jaddada cewa “ta’addanci ya shafi Kiristoci da Musulmai,” kuma gwamnati ta kuduri aniyar kawo ƙarshen ayyukan masu tsattsauran ra’ayi ta hanyar ɗaukar matakan soja, haɗin gwiwa a yanki, da tattaunawa da abokan hulɗa na duniya.

A makon da ya gabata, Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashen da Amurka ta ce suna take ‘yancin addini. A ranar Asabar, ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaro da ta shirya don yiwuwar ɗaukar matakin soja cikin gaggawa idan Najeriya ba ta ɗauki mataki mai tsauri kan kisan Kiristoci ba. Matakin da Washington ta ɗauka ya kawo cikas ga dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar  Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE  Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi  November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin
  • Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar
  • Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Kwamitin Gwamnonin IAEA
  • Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho
  • Najeriya: Ta Sake Jaddada Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar
  • Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya
  • Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar HDL  Da Taimakon Rundunar RSF
  • Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi
  • Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi