Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba.

 

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata.

 

Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya.

 

Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, ta kuma yi gargadin cewa, duk likitan da ba ya son bin ka’idojin kwararru da na gwamnati, ya kamata ya yi murabus maimakon kawo cikas ga tsarin kiwon lafiyar jihar.

 

“Idan ba za su iya yin biyayya ba, to su yi murabus, ko kuma su fuskanci sakamako daga gwamnatin jihar,” Kwamishinan ta yi gargadin.

 

Ta kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan ladabtarwa a kan ma’aikatan lafiya da ke yin kuskure ko wasa da aiki.

 

Dr Maradun ta jaddada cewa jin dadin marasa lafiya ya kasance babban fifikon gwamnati.

REL/AMINU DALHATU.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kokawa

এছাড়াও পড়ুন:

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

 

Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai  November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
  • Na’im Dassim: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
  • DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu