Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo.

Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.

Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ƙara ƙaimi tare da hadin-gwiwa da hukumomin tarayya na inganta matakan tsaro a magudanan ruwa domin hana sake afkuwar irin wannan bala’i.

Ya yi kira ga jama’a a yankunan da ke gaɓar kogi da su ba da fifikon tsaro a ko da yaushe ta hanyar guje wa wuce gona da iri, da kuma amfani da rigar kariya da sauran matakan kariya a duk lokacin da suke tafiya ta ruwa.

Hatsarin kwale-kwale ya zama ruwan dare a Nijeriya, inda ake yawan samun asarar rayuka saboda hakan, musamman a yankunan da ke bakin koguna.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnati Hatsari kwale kwale

এছাড়াও পড়ুন:

Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Waidu Shuaibu, ya umarni dakarun soji cewa ya zama tilas su nemo sannan su ceto daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Jihar Kebbi.

Janar Waidi Shuaibu ya bayar da umarnin ne a yayin ziyarar aiki da ya kai, Jihar Kebbi, washegarin harin ’yan bindiga suka kai makarantar da ke Karamar Hukumar Danko Wasagu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
  • Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
  • Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA