Hukumar UNRWA Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Kashe Falasdinawa 100 Akalla Kowace Rana
Published: 2nd, October 2025 GMT
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila
Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza.
Lazzarini ya ce ta hanyar dandalin X, “A takaice ana kashe mutane 100 a kowace rana a Gaza, sakamakon farmakin da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa ko kuma harbe-harbe a wuraren rarraba abinci da gidauniyar agaji ta Gaza ke gudanarwa.”
Ya ci gaba da cewa, “A lokaci guda kuma, wasu na mutuwa saboda yunwa ko kuma rashin kula da lafiya”.
Lazzarini ya kara da cewa “yawan adadin wadanda suka mutu yana kara rura wutar halin ko-in-kula,” yana mai jaddada cewa “dole ne a ci gaba da rubuta laifukan da ake ci gaba da yi, a ji irin wahalar da ake fama da su, da kuma kula da su.”
Ya kuma kara jaddada kiransa na tsagaita bude wuta, da hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata laifukan da aka tara, da kuma yin adalci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar Ta Ce: Tana Goyon Bayan Kawo Karshen Yakin Sudan Domin Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasar October 2, 2025 Duniya na tir da farmakin Isra’ila kan jirgin ruwan ‘yan agaji zuwa Gaza October 2, 2025 Colombia ta kori jami’an diflomasiyyar Isra’ila October 2, 2025 DRC : An yanke wa Joseph Kabila hukuncin kisa kan cin amanar kasa October 2, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa 44 a ranar Laraba October 2, 2025 Iran ta bukaci a kakaba wa Isra’ila takunkumi kan kisan kiyashin Gaza October 2, 2025 Mohajerani: Iran ba ta maraba da yaki amma ta shirya don kare kanta October 2, 2025 Sojojin Ruwan Isra’ila sun kai farmaki kan jiragen ruwa na Sumud Flotilla October 2, 2025 Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD October 2, 2025 Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148 October 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza.
Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar.
Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje na wucin gadi don kula da tsaro, tallafawa sake ginawa da kuma kiyaye tsari a yankin. Daftarin ya yi kira ga rundunar ta yi aiki na tsawon shekaru biyu, tare da yiwuwar kara sabunta wa’adin aikinta wanda ya danganta ne da ci gaban da ake samu a kasa.
Kudurin ya kunshi abubuwa da yawa, ciki har da kare iyakokin Gaza, kare fararen hula, kare hanyoyin jin kai, da kuma horar da sabbin ‘yan sandan Falasdinu da aka tantance. Hakanan ya ba da izinin amfani da “dukkan matakan da suka wajaba” don cimma wadannan manufofi, gami da wargaza kungiyoyi masu dauke da makamai da kwace makamai marasa lasisi.
Muhimmin fasali na kudurin shine ƙirƙirar hukumar wucin gadi, wacce wani lokacin ake kira “Hukumar Zaman Lafiya,” wacce za ta yi aiki tare da rundunar kasa da kasa don taimakawa wajen gudanar da harkokin Gaza. Shirin ya kuma yi kira da a shigar da cibiyoyin kuɗi na duniya, kamar Bankin Duniya, don ba da kuɗaɗen ayyukan sake ginawa da kuma kula da gudanar da asusun tallafi na musamman.
Daftarin kudurin ya jawo suka daga ƙungiyoyin Falasɗinawa, waɗanda ke bayayya cewa ya ƙunshi wani nau’i na mulkin mallaka da Rashin ‘yancin kai, daga cikin kungyoyin da suka nuna damuwa kan kudirin har da kungiyar Hamas.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci