Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Mutane Sun Yaba Da Gina “Tsarin Xinjiang” A Turbar Zamanantarwar Kasar Sin
Published: 25th, September 2025 GMT
Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang.
A cikin binciken kuma, masu bayyana ra’ayoyi sun bayyana kalamai masu dadi game da nasarorin tattalin arziki na Xinjiang, tare da la’akari da manyan nasarori biyar da aka cimma wadanda su ne: ci gaba da inganta kiwon lafiya (da kashi 82.1), da tabbatar da damar samun ilimi ga jama’a (da kashi 81.7), da ci gaba da inganta ayyukan ababen more rayuwa (da kashi 80.8), da kuma samun babban sakamako wajen kare muhalli da gudanar da mulki (da kashi 80.6), kana da karuwar samun kudaden shiga na jama’a (da kashi 80). (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
Bugu da kari, Amurka ta bayyana a fili cewa batun sauyin yanayi shi ne mafi girman yaudara da aka yi a tarihin dan Adam, kuma ta fice daga “Yarjejeniyar Paris” sau biyu, wanda hakan ya yi mummunar illa ga kokarin al’ummun duniya na kyautata yanayin duniya, kana ta zama babban cikas ga hadin gwiwar duniya a fannin magance sauyin yanayi.
Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, a kan batun magance sauyin yanayi, abun da al’ummar duniya ke bukata shi ne dunkulewa da hadin gwiwa, ba zargi da dora laifi kan wasu ba. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA