Leadership News Hausa:
2025-11-18@11:02:18 GMT

Murnar Zagayowar Ranar Kafuwar Kasar Sin: Bikin Bana Na Daban Ne

Published: 1st, October 2025 GMT

Murnar Zagayowar Ranar Kafuwar Kasar Sin: Bikin Bana Na Daban Ne

Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane.

Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya.

 

Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli na samun habaka cikin hanzari, inda karfin samar da sabon makamashi ya ninka zuwa fiye da kilowatts biliyan 2. Walwalar al’umma na kara habaka ta fuskar kiwon lafiya da sauran muhimman harkokin rayuwa ciki har da kula da ‘yan fansho da kaso 95%, kuma tattalin arzikin kasar a matsakaicin mizanin shekara-shekara yana bunkasa da akalla 5.5% tare da ba da gudummawar kusan kaso 30% na ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

 

Kazalika, bikin na bana ya zo a shekarar da kasar Sin ta kara azamar sauke nauyin da ke wuyarta a fagen kasa da kasa bisa muhimmiyar shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) da shugaba Xi Jinping ya gabatar, gabanin taron cika shekaru 80 da kafuwar MDD. Wannan shawara tare da sauran muhimmai guda uku da shugaba Xi ya gabatar a baya, ba manufofi ba ne kawai, sun kasance sauye-sauye na falsafa da ke kunshe a cikin hikimar “samar da al’ummar duniya mai makoma ta bai-daya”.

 

Yayin da tsoffin tsare-tsaren da kasashen yammacin duniya suka kakaba wa duniya ke fuskantar hisabi, shawarwarin da kasar Sin ta bayar sun kawo mafita a kan yadda za a dama da bangarori masu yawa maimakon babakeren bangare guda, da yadda ko wace al’umma za ta iya tsara tafarkinta, tare da karfafa mutunta juna da samun ci gaba mai gamewa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP

An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.

Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata.

Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana  a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP
  • Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
  • Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
  • An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing
  • Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30
  • Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
  • Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci
  • Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin