Iran Ta Bayyana Aniyarta Ta Rashin Daina Samar Da Magunguna Ta Hanyar Fasahar Makamashin Nukiliya
Published: 8th, October 2025 GMT
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba
Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa.
Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu a cibiyoyin nukiliya a lokacin yakin kwanaki 12, da matakan da aka dauka na inganta tsaron cibiyoyin nukiliya, da sakamakon ziyarar da ya kai kasar Rasha a baya-bayan nan.
Reza’i ya lura cewa: Shugaban hukumar makamashin nukiliya ya jaddada a yayin taron cewa samar da magunguna daga fasahar nukiliya na cikin gida yana ci gaba da gudana kuma bai taba tsayawa ba kuma ba za a daina ba. Ya kara da cewa a halin yanzu kungiyar na kokarin sauya sheka daga matakin bincike da ci gaba zuwa samar da masana’antu, wanda hakan zai yi tasiri ga rayuwar al’ummar kasa da tattalin arzikin kasa.
Ya bayyana cewa, Islami ya lura cewa kungiyar ta samu kusan nasarori 500 na kimiyya da fasaha a tsakanin shekarun 2022-2024, kuma yawan wadannan nasarorin suna da tasiri kai tsaye ga rayuwar mutane.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jihadul-Islami Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Gwagwarmaya Har Sai Falasdinawa Sun Samu ‘Yancinsu October 8, 2025 Falasdinawa 12 Ne Suka Yi Shahada A Harin Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza A Yau Laraba October 8, 2025 Hamas ta bayyana muhimman bukatunta a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza October 8, 2025 Iran ta yi gargadi game da katsalandan na EU akan tsibiran tekun Fasha October 8, 2025 Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da tattauwanar da ake a Masar October 8, 2025 Gaza : Spain na son gurfanar da Isra’ila gaban ICC kan cin zarafin masu fafutukar kai agaji October 8, 2025 Faransa : Ana ci gaba da kira ga Macron ya yi murabus October 8, 2025 Dubban Mutanen Moroko Sun Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa October 7, 2025 Kamfanin Jirgin Sama Na “Oman Air” Ya Maye Gurbin Isra’ila Da Falasdinu A Cikin Taswirarsa October 7, 2025 MDD Ta Yi Maraba Da Hukunta Mai Laifi Na Farko A Yankin Darfur Da Kotun Duniya Ta Yi October 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta
Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan
Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis.
Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul.
Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kawo yanzu ba a samu hasarar rayuka ba.”
Majiyar leken asirin Afganistan ta shaidawa Al-Araby Al-Jadeed cewa: Shugaban Taliban na Pakistan kuma wani babban kwamandan kungiyar ya tsallake rijiya da baya a harin da Pakistan ta kai kan Kabul.
A halin da ake ciki, wasu kafafen yada labaran Afghanistan sun sanar a cikin wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba, y ace: An kashe Mufti Noor Wali Mehsud shugaban Taliban na Pakistan a wani hari da aka kai ta sama a Kabul a daren yau.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci