Hukumar Samar Da Abinci Ta MDD Ta Yi Gargadin Rage Tallafi n Jin Kai A Kasar Somaliya
Published: 6th, October 2025 GMT
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya “WFP” ta bayyana cewa: Rage agajin jin kai na barazana ga miliyoyin mutane da suke fama da yunwa a Somaliya
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta yi gargadin cewa: Miliyoyin mutane a Somaliya na cikin hadarin fuskantar yunwa da rashin abinci mai gina jiki, saboda tsananin karancin kudade da ya tilastawa kungiyar ta WFP rage yawan mutanen da take tallafawa da taimakon abinci na ceton rai da sama da kashi biyu bisa uku.
A watan Nuwamba, za a tilastawa Hukumar WFP ta rage adadin mutanen da ke samarwa tallafin abinci na gaggawa zuwa 350,000 kawai, wanda ya ragu da miliyan 1.1 a watan Agustan da ya gabata. Wannan yana nufin shirin zai tallafawa ƙasa da mutum ɗaya cikin 10 waɗanda ke buƙatar taimakon abinci don tsira da rayuwa.
“Ana ganin matsananciyar yunwar gaggawa a Somaliya, kuma karfin hukumar ta WFP na raguwa a kullum,” in ji Ross Smith, Daraktan Agajin Gaggawa da Ba da Agaji na hukumar WFP. “Idan ba tare da tallafin gaggawa ba, dubban iyalai za su fuskanci bala’in jin kai.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Janar Pakpour: Duk wani shishigi a kan Iran zai fuskanci martani mai tsanani October 6, 2025 Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yancin Falasdinawa October 6, 2025 Babban mai shiga tsakanin na Hamas ya isa Masar domin tattaunawa da Isra’ila October 6, 2025 Rahoto: A cikin shekaru biyu Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a Gaza October 6, 2025 Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza October 6, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris October 5, 2025 Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya October 5, 2025 HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41 October 5, 2025 Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula October 5, 2025 Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya
Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun. Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye karkashin jagorancin Amity damar ci gaba da iko da wani daga bangaren kasar.
Burhan ya zargi Amurka da goyon bayan yan tawayen a cikin shawarar da ta gabatar, kuma shawarar ba irin zaman lafiyan da mutanen sudan suke so ba. Masana suna ganin gwamnatin Amurka da kawayenta wadanda suke goyon bayan yantawaye a duniya musamman a cikin kasashen Larabawa suna son sake raba kasar Sudan ne, kuma sun gabatar da wannan shawarar ce a dai-dai lokacinda suka fahinci cewa gwamnatin kasar tana samun nasara a kan yan tawaye wadanda suke iko da yankin Darfur na yammacin kasar ta Sudan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci