Shugaban Majalisar Nasarawa Ya Yi Alhinin Rashin Tsohon Minista Da Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Published: 25th, September 2025 GMT
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da labarin rasuwar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Barista Solomon Aku Ewuga.
Kakakin majalisar a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Jibrin Gwamna ya fitar, ya bayyana rasuwar mataimakin gwamnan jihar a matsayin babban rashi ga jihar da ma Najeriya baki daya.
Sanarwar ta ruwaito shugaban majalisar na cewa rasuwar tsohon sanata mai wakiltar nasarawa ta arewa, mutuwa ce da ta girgiza al’ummar jihar Egu da ma jihar baki daya ba.
“Bishiyar Iroko ta fado, mai taimakon jama’a kuma fitaccen dan siyasa ya je gida ya huta, Allah ya kara masa yarda.” Inji Shugaban Majalisar.
Kakakin Majalisar Danladi Jatau ya bayyana Sanata Solomon Ewuga a matsayin maginin gada wanda ya taba rayuwar jama’a da dama, ya kuma jajirce wajen samar da zaman lafiya da hadin kai da cigaba a tsakanin al’umma sannan kuma ya bayar da tasiri da gudummawa sosai a fagen siyasa da sauran al’amuran bil’adama.
Dokta Danladi Jatau wanda ya yaba da kyawawan halayen Solomon Ewuga ya roki Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da ayyukansa na alheri da ya aiwatar.
Rel/Aliyu Muraki/Lafia.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Rasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
Sojojin Guinea-Bissau sun naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban ƙasar na rikon kwarya, kwana ɗaya bayan sun yi juyin mulki tare da kama shugaban ƙasar, Umaro Sissico Embalo.
Sojojin dai sun kwace mulkin ne yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen kasar mai cike da takaddama.
Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi“Na rantsar da kaina a matsayin shugaban Babban Kwamandan Soja,” in ji Janar Horta bayan ya karbi rantsuwar aiki a wani biki da aka gudanar a hedkwatar sojoji a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.
Daruruwan sojoji dauke da makamai sun kasance a wurin rantsuwar.
A ranar Laraba, kwana guda bayan manyan ’yan takara biyu a zaɓen shugaban ƙasa mai cike da takaddama kowannensu ya ayyana nasara, wata ƙungiyar hafsoshin soja ta bayyana cewa ta karɓi “cikakken iko” a ƙasar.
Sojojin sun karanta sanarwa a talabijin, suna bayyana cewa sun dakatar da tsarin zaɓe “har sai an ba da sanarwa ta gaba.”
Sun kifar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo a sabon lamari na rikice-rikicen siyasa da ke yawan faruwa a ƙasar.
Wata ƙungiyar hafsoshin sojoji ta bayyana cewa ta karɓi cikakken iko da mulkin ƙasar, kwana guda bayan manyan ’yan takara biyu, Shugaba Umaro Sissoco Embalo da Fernando Dias, kowannensu ya yi ikirarin samun nasara.
Sojojin sun bayar da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaɓen har sai an ba da sanarwa ta gaba.
Haka kuma sun bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin ƙasa da na sama da ruwa, tare da sanya dokar hana fita da dare.
“An yin min juyinmulki,” in ji Embalo a zantarwarsa da gidan talabijin na Faransa France24 ta wayar tarho, yana mai cewa “yanzu haka ina hedkwatar babban hafsan sojoji.”
Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PAIGC, Domingos Simoes Pereira, ma an kama shi, in ji Haque. “Haka kuma mun ji cewa sojoji na ƙoƙarin katse intanet. An kuma sanya dokar hana fita.”
Shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar, Denis N’Canha, shi ne dai sojan da ke jagorantar juyin mulkin.