Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin A Rage Kudin Aikin Hajjin Bana
Published: 7th, October 2025 GMT
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin.
Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana.
Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na bana, ciki har da tattaunawa game da kuɗin kujera.
“Saboda yadda farashin naira ya haɓaka da kuma sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Najeiya da aka fara gani, shi ne mataimakin shugaban ƙasa ya ce yana ganin idan har maniyyata sun biya tsakanin naira miliyan 8.5 zuwa miliyan 8.6 a bara, yanzu da darajar naira ta ɗaga, ya kamata a ga canjin da aka samu a kuɗin Hajjin bana.”
A nasa ɓangare, sakataren hukumar alhazan, Dr Mustapha Mohammad ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ƙara yawan mahajjatan bana.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…