Shugaban Kasar Faransa Zai Amince Da Kasar Falasdinu A Ranar Litinin Mai Zuwa A Birnin New York
Published: 20th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York.
Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar Falasdinu wani bangare ne na cikakken shirin zaman lafiya da ke tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga Isra’ila da Falasdinu.
Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi don tabbatar da wannan karramawa a ranar litinin da misalin karfe 3:00 na rana a birnin New York (9:00 na yamma agogon Paris), yayin wani taron da zai jagoranta tare da yarima mai jiran gado na Saudiyya.
Fadar Elysée ta ce: “A cewar sabon bayanan da aka samu, Mohammed bin Salman zai yi magana ta hanyar taron bidiyo.”
A cikin wannan mahallin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Pascal Confavro ya bayyana a ranar Juma’a cewa; “Wannan amincewa ba ya wakiltar ƙarshen kokarin diflomasiyya … kuma ba furuci ne na alama ba, amma a maimakon haka wani bangare ne na hangen nesa mai zurfi kuma mafi mahimmanci.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tinubu Zai Dauki Nauyin Gasar Wasanni Commonwealth A 2030 September 19, 2025 Kungiyar Tarayyar Turai EU Ta Mika Bukatunta Ga Kasar Iran. September 19, 2025 Dakarun Sojin Yamen Su Kai Hare-hare A Muhimman Wurare A HKI. September 19, 2025 Isra’ila Na ci Gaba Da Kutsa Kai A Tsakiyar Gaza A Yau Juma’a September 19, 2025 Dangantaka Na Kara Tsami Tsakani Faransa Da Isra’ila Kan Falasdinu . September 19, 2025 Sojojin HKI 12 Ne Suka Halaka Ko Suka Ji Rauni A Gaza September 19, 2025 Amurka Ta Yi Amfani Da Kujeran Veto Don Hana Zaman Lafiya A Gaza September 19, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare Kan Wurare Har 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 19, 2025 Majiyoyin Diblomasiyya Sun Ce Washington Zata Jagoranci Turawa A Tattaunawa Da Iran September 19, 2025 Iran Ta Bukaci Kwamitin Tsaro Na MDD Ta Zabi Diblomasiyya Kan Fito Na Fito September 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Falasdinu
এছাড়াও পড়ুন:
ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.”
“Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar.
A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa.
A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a karkashin kuduri na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1593 (2005), Kotun hukuntan manyan laifuka ta Duniya (ICC) tana da hurumin gurfanar da masu hannu a laifukan da aka aikata a rikicin da ke ci gaba da faruwa a Darfur.
Ta kuma bayyana cewa Ofishin yana binciken laifukan da aka aikata a Darfur tun bayan barkewar rikici a watan Afrilun 2023.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne, Rundunar (RSF) ta kwace iko da garin El-Fasher tare da aikata kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa.
Rikicin da barke a ranar 15 ga Afrilu, 2023, tsakanin sojojin Sudan da RSF ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 20,000 tare da raba mutane sama da miliyan 15 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da majiyoyin cikin gida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci