Aminiya:
2025-11-27@20:50:47 GMT

Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki 

Published: 29th, September 2025 GMT

A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki.

Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.

42 na rana.

Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna.

Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu

Jirgin zai ci gaba da zirga-zirga ne bayan kammala gyare-gyare da sauran tanade-tanaden kula da lafiya da tsaro bayan gocewar da ya yi daga kan layin dogo a ranar 26 ga watan Agusta, wanda ya yi sanadiyar tuntsurewar kusan ɗauƙacin taragoginsa.

Fasinjoji 22 ne aka tabbatar sun samu rauni daga cikin mutum 618 da ke cikin jirgin a lokacin da ya yi hatsarin. Babu asarar rayuka.

Kakakin Hukumar NRC, Callistus Unyimadu, ya ce, hukumar ta tuntuɓa tare da mayar wa mutum 512 daga cikin fasinjojin kuɗaɗensu.

Haka kuma ta tuntuɓi akasarin waɗanda suka jikkata inda ta ziyarci wasu gada cikinsu domin dubiya.

Ya ƙara da cewa hukumar ta tanadi kujera guda kyauta a duk mako ga duk fasinjojin da suka samu rauni a hatsarin, har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2025.

Ragowar fasinjojin jirgin da ya yi hatsarin kuma kowannensu zai samu kujera guda kyauta kafin ranar 31 ga watan Disamba, 2025.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abuja zuwa Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar.

A  jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024.

A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina.

 

Ya jaddada cewa mutanen wadannan yankuna sun daɗe suna bukatar wannan aiki na hanyar.

Malam Umar Namadi ya ce titin zai ba su damar kai amfanin gonakinsu kasuwanni mafi kusa cikin sauki.

Ya kuma ce yawancin wadannan hanyoyi sun kai matakin kammaluwa, kuma nan ba da dadewa ba za a gudanar da jerin bukukuwan kaddamar da su gaba daya.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a karkara domin saukaka samun hanyoyin shiga kasuwanni da birane.

Namadi ya bayyana cewa shirin tuntubar jama’a ya bai wa al’umma damar tattaunawa kai tsaye da gwamnati.

Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo Malam, ya ce titin na daga cikin hanyoyi 48 masu dauke da jimillar tsawon kilomita 977 da aka bayar a 2024 a kan kudi Naira biliyan 304.

Wasu daga cikin mazauna yankin, Malam Abdullahi Musa da Malam Muhammad Gata, sun yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan aiki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu.
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi