Ƴan Bindiga Sun Harbe Wanda Suka Sace Saboda Rashin Isassun Kuɗi A Asusunsa
Published: 25th, September 2025 GMT
Rundunar ƴansandan Jihar Delta ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da wani matashi, inda suka karɓi kuɗin fansa na Naira miliyan biyu (₦2m) amma duk da haka suka harbe shi saboda rashin isassun kuɗi a asusun bankinsa.
Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka (25), da Uche Okechukwu da Somto Chukwuma, waɗanda suka yi garkuwa da wanda abin ya shafa daga gidansa da ke Ogwashi-Uku.
Bincike ya kai jami’an tsaro zuwa jihar Anambra, inda suka cafke Chukwuebuka da Uche tare da ƙwato motar wanda aka yi garkuwa da shi, Toyota Venza. Daga baya kuma an cafke na ukun a ƙauyen Agidiase, Ogwashi-Uku.
Ƴansanda sun ce waɗanda ake zargin sun kai su maɓoyarsu, inda aka gano motar da suke amfani da ita wajen kai hare-hare da kuma na’urar ƙaryar sadarwa. Dukkan su na hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara
Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar ciki har da wani Limami a ƙaramar hukumar.
’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a GombeDan Loto yana cikin yankin Yandoton Daji, unguwar da ’yan bindigar suka kashe masu ibada biyar a ranar 26 ga Satumba, 2025.
Binciken Daily Trust ya nuna cewa, ’yan bindigar sun yi wa ’yan ƙungiyar ta CJTF kwanton ɓauna ne a lokacin da suke amsa kiran da ‘yan bindigar ke yi na tayar da ƙayar baya ga al’ummar garin Dan Loto.
Usman Yusuf Tsafe ya shaida wa Daily Trust cewa an kashe jami’an CJTF ne a lokacin da suke musayar wuta da ’yan bindigar.
“Akwai yuwuwar ’yan binigar sun samu labarin zuwan jami’an CJTF, don haka suka yi musu kwanton ɓauna.
“’Yan bindigar sun kashe su, suka tsere sai dai sun auka wa jami’an CJTF ne, bayan sun kashe biyar daga cikinsu, sai suka koma daji, ba su kai farmaki ga mazauna garin ba,” in ji shi.
Aliyu Danlami, mazaunin unguwar Yandoton Daji, ya ce sun shiga cikin ruɗani sakamakon harin.