Rahoto: A cikin shekaru biyu Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a Gaza
Published: 6th, October 2025 GMT
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar da wani sabon rahoto kan cikar shekaru biyu da fara kaddamar da munanan hare-haren Isra’ila a kan al’ummar zirin, inda rahoton ya bayyana cewa har yanzu ayyukan kisan kare dangi na ci gaba da gudana a kan mutanen Gaza.
A cewar sanarwar da aka fitar a wannan Lahadi, Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a kan al’ummar Gaza, snnan kuma sama da mutane 76,600 ne aka kashe ko kuma suka bata ba a san makomarsu ba tun lokacin da aka fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A cikin shekaru biyu, an tabbatar da kashe mutane 67,139, yayin da kusan mutane 9,500 kuma ba a san makomarsu ba, amma da dama da daga cikinsu ana kyautata zaton suna a karkashin baraguzan gine-gnen da Isra’ila ta ruguza a kansu.
Hukumomin Gaza sun ce akasarin wadanda abin yafi shafa yara da mata da tsoffi ne, inda aka tabbatar da cewa yara dama da 20,000 da mata 12,500 suna daga cikin wadanda suka yi shahida. Rahoton ya bayyana cewa an share iyalai 2,700 gaba daya.
Ofishin yada labaran ya ce hare-haren bama-bamai na Isra’ila, sun lalata kusan kashi 90 na ababen more rayuwa na Gaza, lamarin da ya bar al’ummar yankin a cikin matsanancin hali na rayuwa.
An kiyasta cewa sama da kashi 80 cikin 100 na yankin Gaza a halin yanzu yana karkashin mamayar Isra’ila ne, yayin da sama da fararen hula miliyan 2 aka tilasta musu yin gudun hijira a cikin yankin, wanda adadin mutanen ad ke rayuwa a cikinsa ya kai miliyan 2.4.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza October 6, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris October 5, 2025 Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya October 5, 2025 HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41 October 5, 2025 Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula October 5, 2025 Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London October 5, 2025 Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI October 5, 2025 Masar Ta Zargi Habasha Da karya Dokokin Kasa Da Kasa Kan Rikicin Madatsar Ruwan Kogin Nilu October 5, 2025 Shugaban Hamas Ya Bayyana A Fili Tun Bayan Harin Isra’ila A Kasar Qatar October 5, 2025 Dubban Mutane Ne Suka Yi Zanga -Zanga Nuna Adawa Da Isra’ila A Athens. October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar.
Rahotannu sun bayyana cewa sayyid Ammar Hakim shugaban kungiyar wisdom movement na kasar Iraqi ya kaddama da yakin neman zabe inda yayi kira da hadin kai tsakanin alummar kasar kuma ya gargadi kasashe waje da su guji tsoma baka a cikin alamuran kasar.
Wadannan bayanai suna zuwa ne adaidai lokacin da kasar Amurka take matsin lamb akan kasar Iraqi na ta rusa kungiyar Hashdu shaabi, musamman bayan abubuwa da suka faru a kasashen siriya da kuma kasar Labanon.
An kafa kungiary ta Hshadushaabi ne karkashin umarnin babban malamin Addini na kasar Ayatullah Sisitani domin tunkarar kungiyar ta’adda ta da’aesh
Daga karshe Hakim ya jaddada cewa alummar iraki ne kawai suke da hakkin yanke hukumci ba tare da ingizasu ba, duk da matsain lambar da take fuskanta daga kasashen waje. Yace muna son iraki madaidaiciya mai mututunta akidar alummar da suka fi rinjaye, saboda iraki ta kowa ce, babu wani mutum ko gunguni jama’a da zai yi abu shi daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take October 11, 2025 HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci