Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Published: 23rd, September 2025 GMT
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Kashi 81.8 cikin 100 kuma sun bayyana cewa, “kafa kasa mai cin gashin kanta, mai cikakken ‘yanci ta Falasdinu bisa kan iyakokin da aka shata a shekarar 1967, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta” ta zama wata matsaya da aka cimma a tsakanin kasashen duniya.
A cewar bayanai daga hukumomin kiwon lafiya na Gaza, hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane 65,283 tare da jikkata wasu 166,575 tun bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinu a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023. A kuri’ar jin ra’ayoyin, kashi 90.8 cikin 100 na wadanda suka yi Allah-wadai da ta’asar da Isra’ila ke tafkawa, kuma sun yi imanin cewa, ya kamata Isra’ila ta gaggauta dakatar da hare-harenta na soji a zirin Gaza. Kazalika, kashi 92.1 cikin 100 sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki tare da yin taron dangi wajen taka birki ga farmakin sojojin Isra’ila a Gaza. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Ingila Da Canada Da Kuma Australia Sun Bayyana Amincewarsu Da Samuwar Kasar Falasdinu
Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI ta tattunawa da Falasdinawa don warware matsalar tsakaninsu.
Sauya matsayinda wadan nan manya-manyan kasashen duniya suka yi ya sake bude batun samar da kasashe biyu, wanda kuma zai kara tura HKI zuwa bongo don amincewa da samar kasar Falasdinu da kuma bukatar ta dai kissan kiyashin da takewa al-ummar Falasdinu a Gaz da kuma yankin yamma da kogin Jordan.
Kafin haka Falasdinawa sun bukaci kasashen su amince da samauwar kasa don shi ne mataki na farko na kasa kasar ta Falasdinu.
Ya zuwa yanzu dai kasashen duniya kimani 140 ne suka amince da samauwar kasar Falasdinu, Keir Starmer firay ministan kasar Burtaniya ya yi kira ga HKI ta bude hanyoyi wa kungiyoyin agaji su shigar da abinci zuwa Gaza.
Amma gwamnatin kasar Canada ta bayyana cewa gwamnatin HKI mai ci tana aikin ganin ba za’a taba kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru September 21, 2025 Arakci Ya Kore Cewa Ya Zanta Da Steven Witkoff Na Amurka September 21, 2025 Hizbullah Ta Yi Gayyar Tunawa Da Zagayowar Shahadar Sayyid Hassan Nasrallah September 21, 2025 Hamas Ta Yi Bukaci A Hukunta HKI Akan Rusa Asibitoci September 21, 2025 IRGC: Duk Wani Sabon Kuskuren Abokan Gaba Zai Fuskanci Mayar Da Martani Mai Tsanani September 21, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Wata Mota A Kudancin Labanon September 21, 2025 Iran Za ta Iya Shawo Kan Duk Wani Takunkumi Da Aka Sanya Mata . September 21, 2025 Pakistan:Yarjejeniyar Tsaro Da Suka Kulla Da Saudiya Kamar Kawancen Tsaro Na Nato Ne. September 21, 2025 Matatar Mai Ta Dangote Ta Kawo Ƙarshen Dogon Layin Mai A Nijeriya September 21, 2025 Isara’ila Ta Kaddamar Da Shirin Iko Da Wasu Yankuna A Yammacin Kogin Jodan. September 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci