Guinea: An Tsayar Da Ranar 28 Ga Disamba Domin Zaben Shugaban Kasa
Published: 29th, September 2025 GMT
Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahkuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja.
Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a ranar Asabar din da ta gabata.
Sakamakon kuri’ar raba gardamar da ak ayi a ranar 21 ga watan nan na Satumba, ta nuna cewa kaso 89% na wadanda su ka kada kuri’ar, sun nuna amincewa da sabon tsarin mulkin.
Har ila yau, wata kididdiga ta nuna cea kaso 86% na wadanda su ka cancanci yin zabe ne su ka kada kuri’a.
Jam’iyyun hamayyar kasar ta Guinea sun kira yi mutane da su kauracewa kada kuri’unsu akan sabon tsarin mulkin da su ka kira shi da ‘dodorido,kuma an tsara yadda sakamakon zai kasance.
A karkashin sabon tsarin mulkin, shugaban mulkin soja Janar Mamady Doumbouya zai tsaya takarar shugabancin kasar. A baya,lokacin juyin mulkin da ya jagoranta, Janar Doumbaya ya yi alkawalin cewa ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba.
Har ila yau an kara tsawon wa’adin shugabancin kasar daga shekaru 5 zuwa 7, za kuma a iya sabunta shi sau daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Amurka Ta Rinjayi Turai Kan Sanyawa Iran Takunkumi September 28, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Rashin Amincewa Da Duk Wani Takunkumi Kan Iran September 28, 2025 Kasashe 77 Ne Na Duniya Suka Fice A Lokacin Jawabin Fira Ministan Isra’ila A Taron Majalisar Dinkin Duniya September 28, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Kakabawa Iran Takunkumin Rashin Adalci September 28, 2025 Shugaban Majalisar Shawarwar Musulunci Ya Ce: Iran Ba Zata Kimanta Takunkumin Da Aka Kakaba Mata Ba September 28, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 149 September 28, 2025 Takunkuman MDD kan Iran sun fara aiki September 28, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (A) 148 September 28, 2025 Nijar ta yi Tir da kasashen ketare kan tada zaune tsaye a Sahel September 28, 2025 Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu September 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sabon tsarin mulkin
এছাড়াও পড়ুন:
An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata sun kasa ficewa daga kasar bayan juyin mulkin.
Labarin ya kara da cewa sojojin da suka yi juyin mulkin sun kwace iko da kasar ne a dai-dai lokacinda ake irga kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Kafin juyin mulkin dai yan takaran shugaban kasa a zaben shugaba Umaro Sissoco da kuma Fernando Dias duk sun shelanta cewa su suka lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar.
Sojan da ya jagoranci juyin mulkin Denis N’Canha, wanda kafin haka mai gadin shugaban kasa ne, ya tsare shugaban kasar sannan ya bada sanarwan dakatar da duk wani al-amarin zabe, an rufe dukkan hanyoyin shiga ko fita kasar zuwa illa masha Allah. Jonathan dai ya je kasar ne a matsayin shugaban tawagar kungiyar kasashen yammacin Afirka a zaben shugaban kasa da kuma na majalisar dokokin da aka gudanar a ranar 23 ga watan Nuwamba da muke ciki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025 November 26, 2025 Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza November 26, 2025 Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci