Rasha Ta Kai Hare-Hare A Ukraine Cikin Dare
Published: 20th, September 2025 GMT
Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare.
A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine din.
A kudancin ƙasar ma, hukumomi a Mykolaiv sun bayar da rahoton tashin gobara bayan harin da aka kai kan wasu masana’antu.
Yankunan yammacin Lviv da Ivano-Frankivsk ma sun fuskanci gobara sakamakon hare-haren da aka kai masu.
Suna kusa da iyakar Poland, inda sojoji suka ce sun tura jiragen sama domin tabbatar da tsaron sararin samaniyar yankin.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ukraine
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Kaddamar Da Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan A Birnin Shenyang
A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp