Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD
Published: 2nd, October 2025 GMT
Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.
Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus.
Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumai a kan Iran, duk kuwa da kokarin diflomasiyya mai karfi da aka yi a makonni biyu da suka gabata, da kuma shirye-shiryen da Iran ta yi na neman mafita, saboda kasashen ukun sun yi watsi da duk wata matsaya da aka cimmawa tare da su.
Daftarin kudurin da shugaban majalisar ya gabatar a ranar 19 ga watan Satumba bai cika sharuddan kudurin 2231 ba, kuma sakamakon la’akari da hakan bisa doka ba za a iya maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran ba, amma duk da hakan wasu mambobi na kwamitin sun yi watsi da hakan.
Jami’in diflomasiyyar na Rasha ya ce tun da kwamitin sulhun bai amince da wani kuduri kan tsawaita kuduri mai lamba 2231 na MDD ba, to zai daina aiki daidai da ranar da aka cimma yarjejeniyar JCPOA a ranar 18 ga Oktoba, 2025.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148 October 2, 2025 Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba bindiga a bainar jama’a a 2018 October 2, 2025 Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza. October 1, 2025 Kasar Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara. October 1, 2025 A gobe Ne Ake Sa Ran Tawagar Agaji Ta Sumud Flotilla Za ta Isa Gaza. October 1, 2025 Iran Ta yi Kira Da A Gaggauta Kakabawa HKI Takunkumi October 1, 2025 A yau Najeriya ke bikin cika shekaru 65 da samun yancin kai October 1, 2025 Aragchi: Za’a Fara Tattaunawa Ta Karshe Dangane Da Shirin Snapback October 1, 2025 Tinubu: Na Gaji Rusashen Tattalin Arziki A Sanda Na Karbi Ikon Kasar October 1, 2025 Iran: Dakarun Ruwa Na Iran A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Kowa Don Kare Kasa October 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar watan yuli ya nuna cewa Amurka da kawayenta ciki har da isra’ila suna harin naurorin kimiyya na jamhuriyar musulunci ta iran ne.
Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da gidan talbajin din Al-Masirah na kasar Yamen inda ya jaddada” cewa ba’a taba kai irin wannan harin ba kan nauraron kimiyyar kasar a cikin tarihi, don haka yanayi kai harin yana nuna cewa Amurka da kawayenta sun shiga wani sabon mataki mai hadari, na karuwar tashin hankali kan yakin da suke yi da kimiyyar kasar iran.
A ranar 13 ga watan juni ne isra’ila ta kaddama da yaki kan kasar iran inda ta kashe manyan kwamandodjin sojojinta da masana nukuliya da sauran fararen hula ,
bayan fiye da mako daya kuma Amurka ta shi ga cikin yakin kai tsaye inda tayi ruwan bama -bamai kan tashohin nukiliyar iran wanda hakan keta hurumin majalisar dinkin duniya da kuma yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukuliya NPT ne.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci