Gwamna AbdulRaza ya jajanta wa Oke Ode, da sauran al’ummomi kan hare-haren masu garkuwa da mutane
Published: 3rd, October 2025 GMT
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.
A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.
Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi.
A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo karshen irin wadannan abubuwan.
A yayin ziyarar Gwamnan yana karbar bayanai daga jami’an tsaro da wasu masu ruwa da tsaki daga Oke Ode da Igbaja makwabciyarta, ciki har da shugaban kungiyar ci gaban Oke Ode na kasa, Alhaji Abdulganiyu Ajala; Dattijo Oyin Zubair, da shugaban matasa.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Garkuwa Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza
Rahotanni sun bayyana cewa Craig mokhiber tsohon babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya ya sanar a hukumance yin Allah wadai da kuri’ar amincewa da kudurin Amurka da aka yi a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na aikewa da dakarun kasashen waje zuwa yankin Gaza yace wannan baban abin kunya ne.
Kalaman nasa ya nuna irin suka da kungiyoyin kasa da kasa suke yi ne kan mummunan tasirin da yakin yayi wa yankin gaza, da kuma kasa tsagaita wuta da yadda za’a shigar da kayayyakin agaji zuwa yankin
Isra’ila ta toshe kafar shigar da magunguna da kayayyakin lafiya da kuma hana fitar da marasa lafiya sama da 16500 zuwa wajen don yi musu maganin, bayan da cibiyoyin kula da lafiya suka rushe baki daya ya bar marasa lafiya da dama a yashe ba tare da kulawa ba.
Daga ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 da isra’ila ta kaddamar da hari kan gaza zuwa yanzu Kimanin mutane 68872 ne suka yi shahada akalla 170,000 kuma suka jikkata dubbai kuma sun bace bata sama ko kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci