Laifukan kisan ƙare dangin da Isara’ila ta yi a Gaza — Rahoton MƊD
Published: 20th, September 2025 GMT
Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza.
Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, tun farkon yaƙinta da wungiyar Hamas a shekarar 2023.
Rahoton ya ba da misali da kalaman shugabannin Isra’ila, da kuma abubuwan da sojojinta suka yi a Gaza, a matsayin shaida na aikata kisan ƙare dangi.
Ma’aikatar harkokin Wajen Isra’ila ta ce ta yi watsi da rahoton da kakkausar murya, tana mai bayyana shi a matsayin “karya da kuma juya gaskiya.”
Sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da wani gagarumin yaƙi a Gaza a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda aka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da 251.
Aƙalla mutane 64,964 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza tun daga wancan lokacin, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke yankin, wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ke ganin alƙalummanta a matsayin abin dogaro.
Galibin jama’ar kuma sun yi gudun hijira fiye da sau ɗaya; an rusa fiye da kashi 90% na gidajen; tsarin kiwon lafiya, ruwa, tsaftar muhalli da tsafta sun durƙushe; sannan kwararru kan harkokin samar da abinci da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya sun ayyana yunwa a birnin Gaza.
Kwamitin Kare Haƙƙodin Ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya kafa Kwamitin Bincike na Ƙasa da Ƙasa Mai Zaman Kansa Kan Yankin Falasɗinu da aka Mamaye a shekara ta 2021 don gudanar da bincike kan duk wani zargin keta haƙƙin bil adama na ƙasa da ƙasa.
Kwamitin ƙwararrun mai mutane uku yana ƙarkashin jagorancin Naɓi Pillay, wata tsohuwar jami’ar kare haƙƙin bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ta kasance shugabar Kotun Ƙasa da Ƙasa Kan kisan ƙare dangin da aka yi a Rwanda. Sauran mambobi biyun sun haɗa da Chris Sidoti, lauyan kare haƙƙin ɗan Adam ɗan ƙasar Australia, da kuma Miloon Kothari, wani ƙwararre ɗan ƙasar Indiya kan harkokin gidaje da haƙƙoƙin filaye.
A baya dai hukumar ta bayyana cewa ƙungiyar Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ɗauke da makamai sun aikata laifukan yaƙi da sauran manyan laifukan keta dokokin ƙasa da ƙasa a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, sannan kuma jami’an tsaron Isra’ila sun aikata laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaƙi a Gaza.
Hukumar ta ce rahoton nata na baya-bayan nan shi ne “mafi karfi kuma mafi sahihanci da MƊD ta gano zuwa yanzu” a kan yaƙin. Duk da haka, ba ta yin magana da yawun MƊD a hukumance.
Me sabon rahoton ya ganoRahoton mai shafi 72 ya yi zargin cewa hukumomin Isra’ila da jami’an tsaron Isra’ila sun aikata kuma suna ci gaba da aikata huɗu daga cikin ayyuka biyar na kisan ƙare dangi da aka ayyana ƙarƙashin yarjejeniyar kisan ƙare dangi ta 1948 kan wata ƙasa, jinsi, ƙabilanci ko addini — wanda a wannan karon aka yi wa Falasɗinawa a Zirin Gaza:
1- Kashe al’umma ta hanyar kai hari kan abubuwan da ake karewa da fararen hula da sauran mutanen da aka karewa; da kuma haifar da yanayi da gangan da ke haddasa mace-mace.
2- Illata jiki ko tunaninsu ta hanyar kai hare-hare kan fararen hula da abubuwan da akr karewa; musguna wa wadanda ake tsare da su; tilasta su sauya matsuguni da lalata muhalli.
3- Tsara wani yanayin rayuwa da gangan domin kawo hallaka ga wata al’umma gaba ɗaya ko wani ɓangare — ta hanyar ƙonewa ko lalata gine-gine da wurare masu muhimmanci ga Falasɗinawa; ƙonawa ko hana samun ayyukan kiwon lafiya; tilasta musu yin ƙaura; hana isar agajin gaggawa, ruwa, wutar lantarki da mai ga Falasɗinawa; cin zarafi da ya shafi haihuwa; da kuma yanayi na musamman da ke shafar yara.
4- Sanya matakan da aka tsara domin hana haihuwa ta hanyar harin da aka kai a Disamba 2023 kan babbar cibiyar haihuwa ta Gaza, wanda rahotanni suka ce ya lalata kusan ƙwayayen ɗan adam 4,000 da samfurin maniyyi 1,000 da ƙwayayen mace da ba a haɗa ba.
Domin tabbatar da cikar ma’anar kisan ƙare dangi na shari’a a karkashin yarjejeniyar kisan ƙare dangi, dole ne kuma a tabbatar da cewa wanda ya aikata ya yi aƙalla ɗaya daga cikin wadaɗannan ayyuka da niyyar lalata wani yanki na ɗaya ƙungiyar ko gaba dayanta.
Pillay ta bayyana cewa, “Hujjojin muka fara dubawa. Don haka mun dubi kalaman da mahukuntan Isra’ila da ke nuna aniyar kisan ƙare dangi. Mun kuma duba yanayin ayyukan mahukuntan da jami’an tsaron Isra’ila domin mu nuna cewa aniyar kisan ƙare dangi ita ce kawai manufarsu.”
Shugabannin siyasa da na sojin Isra’ila sun sha bayyana cewa hare-haren da sojojinta ke kaiwa a Gaza ana gudanar da su ne domin kare kai, da fatattakar Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasdinawa masu ɗauke da makamai, da kuma ganin an sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su.
Sun kuma dage cewa sojojin Isra’ila suna gudanar da ayyukansu bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ɗaukar dukkan matakan da suka dace don rage cutar da fararen hula.
Ɓarnar da Isra’ila ta yi a Gaza
Sai dai rahoton na hukumar ya ƙarƙare da cewa, Shugaban Ƙasar Isra’ia, Isaac Herzog, da Fira Ministan ƙasar Benjamin Netanyahu, da kuma tsohon Ministan Tsaro Yoaɓ Gallant, sun tunzura aikata kisan ƙare dangi a jawabansu da bayanansu.
Pillay ya ce, “Tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, Firai Minista Netanyahu ya yi alƙawarin yin…“mummunar ramuwar gayya” kan “dukkan wuraren da Hamas ke jibge, ko ɓoye ko gudanar da aiki, a cikin wannan mugun birni, za mu yi lebur da su.”
“Yin amfani da kalmar ‘mugun birni’ a cikin wannan bayanin na nuni da cewa yana ganin ɗaukacin birnin Gaza (Garin Gaza) a matsayin masu alhaki da kuma hasadin ɗaukar fansa. Kuma ya shaida wa Falasɗinawa cewa su “fice yanzu saboda za mu yi aiki da ƙarfi a ko’ina.”
Gallant ya ce kwanaki kaɗan bayan 7 ga Oktoba 2023, Isra’ila ta ce tana “yakar dabbobin mutane, kuma muna ɗaukar mataki daidai da yadsa suke.” A lokacin ne kuma Herzog ya bayyana cewa “dukkanin al’ummar ƙasar ne ke da alhakin” harin da Hamas ta kai.
Hukumar ta kuma ce “nufin aikata kisan ƙare dangi shi ne kawai fassara mai ma’ana” da za a iya yi wa matakai da abubuwan da mahukuntan Isra’ila da jami’an tsaronta suke yi a Gaza.
Abubuwan da ake zargin sun haɗa da kisa da gangan; da kuma cutarwa mai tsanani ga wani adadi na Falasɗinawa da ba a taɓa ganin irinsa ba ta hanyar amfani da manyan bindigogi; hare-hare da aka tsara masu yawa a wuraren ibada da cibiyoyin al’adu da ilimi; ƙaƙaba wa Gaza ƙwanya tare da kashe al’ummarta da yunwa.
Pillay ya ƙara da cewa, “Shakara muka shafe kafin mu tattara dukkan ayyukan da kuma yin bincike na gaskiya, don tabbatar da ko hakan ya faru … Gaskiyar ita ce kawai za ta jagorance ku. Kuma dole a sanya su a ƙarƙashin yarjejeniyar kisan ƙare dangi idan an yi waɗannan ayyukan da wannan nufin.”
Kwamitin ya ce duk abin da shugabannin siyasa da na soja na Isra’ila suka aikata, “to ƙasar Isra’ila ce”, don haka ƙasar Isra’ila” ce ke da laifin gazawar hana kisan ƙare dangi, da aikata kusan dukkan kiyashi da kuma rashin hukunta aikata kisan ƙare dangi”.
Har ila yau, ta jaddada cewa duk sauran ƙasashen na da alhakin gaggawa a ƙarƙashin yarjejeniyar kisan ƙare dangi su “hana da aikata laifin kisan ƙare dangi”, ta hanyar yin amfani da duk matakan da suke da su. Idan ba haka ba, in ji shi, za su iya zama masu hannu a kisan.
Martanin Isra’ilaA cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta zargi mambobin kwamitin uku da yin aiki a matsayin wakilan ƙungiyar Hamas.
“Rahoton ya dogara ne kacokan a kan ƙaryar Hamas, wanda wasu suka yi ta yaɗawa da kuma maimaita su. Tuni aka riga aka yi watsi da waɗannan ƙage-ƙagen.”
“Saɓanin ƙaryar da ke cikin rahoton, ƙungiyar Hamas ce da ya yi yunƙurin kisan ƙare dangi a Isra’ila — ta kashe mutane 1,200, da yi wa mata fyaɗe, da k’ƙona iyalansu da ransu, tare da bayyana manufarta na kashe kowane Bayahude,” a cewar sanarwar.
Wani jami’in sojan Isra’ila ya yi watsi da rahoton a matsayin “marasa tushe”, yana mai cewa, “Babu wata ƙasa da ta kasance a cikin irin wannan yanayi kuma ta yi abin kirki wajen hana cutar da fararen hula a fagen fama.”
Shugaba Herzog ya kuma yi tir da rahoton, wanda ya ce ya yi wa kalamansa mummunar fassara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Har ila yau ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce bai kamata a maye gurbin mambobin kwamitin ba idan suka sauka daga kan muƙaminsu a karshen wannan shekara, a maimakon haka a soke hukumar da kanta.
A watan Yuli, dukkan mambobi uku na kwamitin sun miƙa takardar murabus ɗinsu ga Hukumar Kare Haƙƙin Bil Adama ta MƊD. Pillay, mai shekaru 83, ta bayyana yawan “shekarunta da rashin lafiya da nauyin wasu alƙawura da dama”, yayin da Sidoti ya ce ritayarta ta nuna “lokacin da ya dace don sake kafa hukumar”.
Ra’ayin ƙwararru da ƙungiyoyiWasu kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa da na Isra’ila, da ƙwararrun MƊD masu zaman kansu, da kuma masana sun zargi Isra’ila da yi wa Falasɗinawa kisan ƙare dangi a Gaza.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ba za ta iya yanke hukunci a shari’a kan ko wani yanayi ya zama kisan ƙare dangi a ƙarkashin dokokin ƙasa da ƙasa ba. Ta ce ba a kiran wani yanayi da kisan ƙare dangi sai bayan wata kotun ƙasa da ƙasa da ta cancanta ta bayyana hakan.
Da manema labarai suka tambaye shi a ranar Talata ko zai yi amfani da kalmar kisan ƙare dangi wajen bayyana ayyukan Isra’ila a Gaza, babban jami’in kare haƙƙin bil’adama na MƊD, Ɓolker Türk ya ce, “Kotu ce ke da alhakin yanke hukunci ko kisan ƙare dangi ne ko a’a, kuma muna ganin shaidun suna ƙaruwa.”
Wani mai magana da yawun gwamnatin Birtaniya ya bayyana cewa hukuncin ya rataya a wuyan kotu, amma ya ƙara da cewa, “wannan ba zai kawar da mu daga matsayinmu na cewa abin da Isra’ila ke yi, abin takaici ba ne.”
A halin yanzu dai Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICJ) na ci gaba da sauraren ƙarar da ƙasar Afirka ta Kudu ta shigar na zargin sojojin Isra’ila da aikata kisan ƙare dangi, amma ana iya ɗaukar shekaru kafin a cimma matsaya.
Isra’ila ta bayyana lamarin a matsayin “mara tushe balle makama” kuma wanda aka yi bisa “ra’ayin son zuciya da ƙarya”.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila kisan ƙare dangi Majalisar Ɗinkin Duniya Palasɗinawa yarjejeniyar kisan ƙare dangi aikata kisan ƙare dangi Majalisar Ɗinkin Duniya kare haƙƙin bil adama kisan ƙare dangi a a ƙarƙashin fararen hula Isra ila sun bayyana cewa Isra ila da Isra ila ta wani yanayi an Isra ila abubuwan da
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wata ganawa da takwaransa na kasar Masar ya bayyana cewa: Iran da Masar sun mallaki wasu al’adu guda biyu masu cike da tarihi masu alfahari da fa’ida, kuma fadada hadin gwiwar da ke tsakaninsu zai kara taimakawa wajen tabbatar da moriyar al’ummomin kasashen biyu da ma sauran al’ummomin yankin.
Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian a yau litinin a ci gaba da tarukan da yake yi a gefen taron gaggawa na kasashen musulmi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a birnin Doha na kasar Qatar ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi. Da take bayyana fatan gaggauta kulla alaka a tsakanin kasashen biyu, Pezeshkian ta bayyana cewa: karfafa hadin kai da hadin kai tsakanin kasashen musulmi, ita ce hanya mafi inganci wajen dakile maimaitawa da ci gaba da laifukan gwamnatin Isra’ila.
El-Sisi, ya bayyana jin dadinsa da taron da kuma yadda dangantakar Iran da Masar ke ci gaba da bunkasa, ya jaddada cewa Tehran da Alkahira na da karfin da za su iya tabbatar da moriyar juna da kuma moriyar sauran kasashen yankin. Haka nan kuma ya jaddada muhimmancin kusanci tsakanin kasashen musulmi da kuma daukar matsaya daya a aikace kan laifukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, wadda ta yi tsokaci kan rikicin siyasa da diflomasiyya na Isra’ila bayan harin da aka kai a birnin Doha, ya bayar da rahoton cewa, Isra’ila na kara zama saniyar ware a fagen kasa da kasa, yayin da Masar, Saudiyya, da Jordan ke kara kusantar Iran. Tashar ta bayyana halin da Isra’ila ke ciki a halin yanzu a matsayin tsunami na siyasa, inda ta kara da cewa warewar Isra’ila a duniya na karuwa kuma kasashen da a da suke daukar kansu aminan Tel Aviv – irin su Saudiyya, Masar, da Jordan – a yanzu suna karfafa alaka da Iran.
Masoud Kazemian wani mai sharhi kan al’amuran yammacin Asiya ya rubuta game da kulla cikakkiyar alaka tsakanin Iran da Masar, inda ya bayyana cewa dangantaka tsakanin Tehran da Alkahira ta zama wata muhimmiyar bukata. Ya yi nuni da cewa, wannan kusanci ba wai kawai yana amfanar tsaron kasa da tattalin arzikin kasashen biyu ba ne, har ma zai iya ba da gudummawa wajen samar da kwanciyar hankali da kwanciyar hankali.
Masanin siyasar ya jaddada cewa, ta fuskar jami’an diflomasiyyar Iran da na Masar, hadin gwiwar da ke tsakanin Tehran da Alkahira na iya zama “sabuwar yanayin kwanciyar hankali” da kuma taimakawa wajen daidaitawa da kawancen kasashen Yamma da sahyoniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Zargi HKI Da Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci