Madagascar : Shugaba Rajoelina ya sanar da korar daukacin gwamnatinsa
Published: 30th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar.
A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa.
Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].”
Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa doka ta 54 na kundin tsarin mulkin kasar, na yanke shawarar dakatar da ayyukan Firaminista da na gwamnati.” “Har a nada sabuwar gwamnati, wadanda ke kan mukaman za su yi aiki a matsayin shugabannin rikon kwarya, nan da kwanaki uku masu zuwa za mu karbi shawarwarin FiraMinista, sannan bayan nadin nasa za a ba shi wa’adin kafa gwamnatinsa.
Rahotanni sun ce a jiya Litinin ma, dubban matasa sun hallara a rana ta uku na zanga zangar nuna adawa da katsewar ruwa da wutar lantarki.
A ‘yan sa’o’i kadan da suka gabata, babban jami’in kare hakkin bil’adama na MDD, Volker Türk, ya ce ya kadu matuka da yadda aka mayar da martani mai tsanani ga zanga-zangar da aka yi a Madagascar, inda “akalla mutane 22 suka mutu, wasu fiye da dari suka jikkata,” a cewar MDD.
Saidai ma’aikatar harkokin wajen kasar ta musanta wannan labarin da kakkausar murya, amma ba ta sanar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi ya gana da sakatare janar na MDD September 30, 2025 Adadin Hada-hadar Kasuwancin Kasashen Waje Ta Iran Takai Dala Biliyan 54 A Cikin Wata 6 September 30, 2025 Janar Safavi: matukan jirgen Isra’ila 16 ne suka a harin makami mai linzami na Iran a lokacin yaki September 30, 2025 Trump: Za mu goyi bayan Netanyahu idan Hamas ba ta amince da kudirinmu ba September 30, 2025 Iran: An zartar da hukuncin kisa a kan wani babban dan leken asirin Isra’ila September 30, 2025 Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha September 30, 2025 Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Takunkumin makamai na Turai ya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin sojojin Isra’ila September 30, 2025 Kungiyar Yan Gudun Hijira Na Kasar Noway Tace Akwai Babbar Damuwa Game Shiru Kan Gaza September 29, 2025 Shugaban Iran: Yunkurin Durkusar Da Alummar Iran Bashi Da Maraba Da Mafarki. September 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran
Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da ake gabatarwa a yau shine yaƙin tunani da yaƙin da aka saba gani.
A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Brigadier Janar Na’ini ya ba da labarin lokutan shaƙatawa da ba zato ba tsammani na barkewar yaƙin da kuma shahadar wasu manyan kwamandojin soja na ƙasar. Ya kuma lura da yadda aka sake gina sansanin umarni a cikin ɗan gajeren lokaci da kuma yadda aka mayar da martani mai ƙarfi. Ya ƙara da bayyana cewa: Wannan shiri mai ban sha’awa ya samo asali ne daga shekaru na tsare-tsare, maimaita atisayen “iko”, da kuma hangen nesa na kwamandojin da suka ɗauki barkewar yaƙi a matsayin “ƙarewar da aka riga aka yi” tsawon watanni.
Hira ta yi magana game da sabon yanayin wannan yaƙin gaba ɗaya: yaƙin fasaha, makamai masu linzami, da kuma yaƙin haɗaka, wanda a cikinsa akwai muhimman wurare na yanar gizo da kuma fagen yaƙi na fahimta ba su fi muhimmanci fiye da fagen daga ba.
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya bayyana rawar da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya taka, ba wai kawai a cikin kula da fagen daga ba, har ma a cikin “sarrafa al’umma” da “sarrafa labarin yaƙi” – rawar da ta sanya amincewa a cikin al’umma.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Na’im Dassim: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci