Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Published: 8th, October 2025 GMT
Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.
Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne kuma ya sa ake amfani da karin jiragen kasa wajen samar da hidimar sufuri ga fasinjoji, inda ake sa ran ganin aiki ya gudana da karin jiragen kasa 2,189 a yau, a wurare daban daban na kasar Sin. (Bello Wang)
ShareTweetSendShareMASU ALAKA
কীওয়ার্ড: jiragen kasa a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe.
Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar.
Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan.
Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun domin maniyyatan da za su sauke farali.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, yayi nuni da cewar, a duk fadin kasar nan jihar Jigawa ce kadai ta sami ranar 24 ga watan gobe sakamakon karamci da Gwamna Umar Namadi ya yiwa hukumar na bada lamunin sama da naira miliyan dubu 3 domin kebe kujerun jihar a aikin Hajjin 2026.
Kazalika, ya kara da cewar babu wata jihar da ta sami karamci da tagomashi wajen alkinta kujerun maniyyata fiye da jihar Jigawa.
A don haka, Labbo ya bukaci maniyyata da su gaggauta biyan kudin kujerun su ta hannun shugabannin shiyya ko kuma a shelkwatar hukumar dake Dutse nan da makwanni 4.
Ya kuma kara jaddada kudurinsa na rike kambun hukumar wajen tabbatar da kula da jin dadin alhazai da walwalar su tun daga gida Najeriya har zuwa kasa mai tsarki.
Ahmed Umar Labbo ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa karamcin da yake yiwa hukumar na bada lamunin kudi domin tare kujerun alhazan jihar da sauran ayyukan hukumar domin gudanar da aikin Hajji ingantacce.