Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
Published: 17th, September 2025 GMT
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai zama wani mataki mai matukar muhimmanci a wannan kasa ya yammacin Afirka.
Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasa a watan Disamba na 2021, an yi dokar da majalisar Mulki ta soja ta amince da ita, wacce ta kunshi cewa; Dukkanin ‘yan majalisar Mulki ta soja ba su da hakkin tsayawa takara a fadin kasa da kuma a matakin yankuna.
Sai dai kuma a cikin sabon tsarin mulkin da za a kada kuri’ar raba gardama akansa babu wannan dokar a cikinsa.
Har ila yau, sabon kundin tsarin mulkin ya zo da sabon tsarin tsawaita wa’adin mulkin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa shekaru bakwai,wacce za a iya sabuntawa sau daya. Haka nan kuma a karkashin sabon tsarin mulkin za a kafa majalsiar dattijai,wacce shugaban kasa ne yake da ikon nada kaso 1/3 na mamabobin wannan majalisar.
Da akwai mutane fiye da miliyan 6.7 da za su kada kuri’ar raba gardamar, za kuma a amince da shi, idan rabin wadanda su ka yi zaben su ka amince da shi.
Tun a 2024 ne dai aka tsayar da cewa za a mika wa fararen hula Mulki sai dai kuma sojojin sun saba alkawali. A watan Disamba na wannan shekarar ne aka tsayar za a yi zaben shugaban kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsarin mulkin sabon tsarin kada kuri ar
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya rundunar Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje, da masu goyon bayanta na yankin suka aikata a El Fasher da kuma sauran wurare a cikin Sudan.
Idris ya yi kira ga Kwamitin Tsaro da ya sanya takunkumi mai tsauri ga dukkan kasashe da daidaikun mutane da Majalisar ta sani wadanda ke bayar da kudi ga RSF, samar mata da makamai, ko samar mata da mafaka, sannan a fara bincike kan kisan kiyashin da ake yi wa mazauna El Fasher don ci gaba da kokarin daukar mataki. Ya kara da cewa “‘yan bindiga suna yin barazanar kashe mutane a kullum rana ta Allah.”
Wakilin na Sudan ya yi kira da a tabbatar da an aiwatar da kudurorin Majalisar Tsaro na 2736 da 1591, “kamar yadda shaidu a Darfur suka tabbatar da cewa wasu ƙasashe maƙwabta sun shiga cikin kisan fararen hula don tallafawa ‘yan bindiga.”
Bugu da ƙari, Al-Harith ya yi kira da a goyi bayan taswirar da gwamnatin Sudan ta gabatar wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta dogara ne akan dakatar da yaƙi na dindindin da kuma kwance damarar makamai na ‘yan bindiga, sannan kuma su mika wuya.
Idris ya fayyace cewa ba za a yi tattaunawa da RSF ba har sai sun ajiye makamansu su kuma sun daina kai hari kan al’ummar Sudan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci