Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
Published: 31st, March 2025 GMT
A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin.
Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe akalla Falasdinawa 80 a ranar Lahadi.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kai mutane 53 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci a Gaza a ranar Lahadin, wato ranar farko ta bikin Eid al-Fitr.
Ma’aikatar ta kara da cewa, “har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine, saboda masu ceto ba su iya kai musu dauki.
A ranar 18 ga Maris, ne Isra’ila ta sake dawo da kai farmaki Gaza wanda ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da ta fara aiki a watan Janairu.
Ana kuma tuhumar Isra’ila da laifin kisan kiyashi a gaban kotun kasa da kasa saboda yakin da ta yi da yankin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Ivory Coast Ouattara zai sake takara wa’adi na huɗu
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba.
Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba.
Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliyaA wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki.
Ya bayyana cewa, “Ni dan takara ne saboda kundin tsarin mulkin kasarmu ya ba ni damar sake tsayawa takara a wani wa’adi, kuma ina da lafiyar yin hakan,” inji Shugaba Ouattara.
Sanarwar da ya yi a kafafen sada zumunta, na zuwa ne bayan da jam’iyyarsa ta Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP) ta amince da takararsa a hukumance.
Jam’iyyun adawa sun soki matakin da cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Tun dai gabanin sanar da matsayar sake takara, aka soma tafka muhawara kan soke sunayen ’yan takarar shugaban kasa daga bagaren ’yan adawa.
Tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo, da tsohon Firaminista Guillaume Soro, da kuma tsohon minista Tidjane Thiam duk an cire sunayensu daga rajistar masu zaɓe, lamarin da ya hana su tsayawa takara.
Bayanai sun ce hankali ya ƙara tashi a yau bayan da hukumomi suka haramta zanga-zangar lumana da aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Agusta, ranar bikin samun ’yancin kai na Cote d’Ivoire.
Ƙungiyoyin ’yan adawa ne suka shirya zanga-zangar da nufin neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan jerin sunayen masu kaɗa ƙuri’a tare da mayar da sunayen waɗanda aka hana tsayawa takara.