Ana Share Fagen Gudanar Bikin Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Shigar Da Su Kasar Sin Yadda Ya Kamata
Published: 31st, March 2025 GMT
A yau Litinin, hukuma mai kula da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare, ta bayyana cewa, yanzu haka ana share fagen gudanar da bikin yadda ya kamata, inda yawan fadin shagunan da kamfanoni daban-daban suka kulla kwangilolin baje kolin kayayyakinsu a ciki ya kai muraba’in mita dubu 240, kuma ya kai 2/3 na fadin wurin da aka tanada.
Bikin nan da za a gudanar da shi a karo na 8, zai samu ci gaba a bangarori hudu. Na farko, za a tabbatar da fadin wurin bikin da ya kai muraba’in mita dubu 360, don baje kolin kayayyakin zamani. Na biyu, za a samar da dandaloli masu kyau ga mu’ammalar jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa don kara hadin gwiwarsu. Na uku kuma akwai batun taimakawa matsakaita da kananan kamfanoni wajen kafa karin shirin tattalin arziki na yanar gizo, da makamashi masu tsafta da sauransu. Na hudu kuma, za a kara kokarin tabbatar da ingancin kayayyakin da ake shigar da su, da gayyatar karin kamfanoni a matakai daban-daban da su halarci bikin, ta yadda za a gaggauta samun daidaito tsakanin bukatun dake akwai da bangaren samar da kayayyaki. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa
Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba.
Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da aka gabatar da ke tabbatar da wannan zargi, wanda hakan ya sa binciken ya tsaya.
Kimanin wata biyar ke nan da Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai na Nijeriya suka fara bincike kan zargin, amma har yanzu babu wani sakamako ko rahoto.
Aminiya ta gano cewa tun sama da shekara goma da suka wuce, ake zargin wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da kuma na cikin gida da hannu wajen taimaka wa ayyukan Boko Haram ta bayan fage.
Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓutaA ranar 13 ga watan Fabrairun 2025, ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya zargi USAID da bai wa Boko Haram da wasu ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya kuɗaɗe kimanin Dala miliyan 697 a kowace shekara, daga kuɗaɗen harajin da Amurkawa ke biya.
Ya ƙara da cewa ana tura kuɗaɗen ne ga ƙungiyoyin Boko Haram da ISIS da Al-ƙaeda da kuma ISIS-Khorasan domin horas da mayaƙansu.
Shugabannin siyasa da na soja a Nijeriya sun tayar da jijiyoyin wuya kan zargin na Mista Perry, inda suka danganta jinkirin shawo kan Boko Haram da rashin samun sahihan bayanan sirri, suna masu zargin cewa ƙungiyoyin agaji na tallafa wa ƙungiyar ta ƙarƙashin ƙasa.
Bayan zargin na Mista Perry, Majalisar Dattawa da ta Wakilai a Nijeriya suka amince a yi bincike a kai, amma yanzu kusan watanni biyar sun shuɗe, babu wani rahoto kan sakamakon binciken, lamarin da ke ƙara haifar da zargin yiwuwar akwai matsin lamba daga wani wuri da ke so a kawar da batun.
USAID ta tallafa wa ƙungiyoyi da dama da ke aiki a fannonin kiwon lafiya da noma da tsaftar muhalli da ilimi da kuma wayar da kan jama’a a yankunan da rikicin Boko Haram ya fi ƙamari, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa. A yanzu haka ana kyautata zaton akwai ƙungiyoyin agaji sama da 200 da ke aiki a yankin na Arewa maso Gabas.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ne ya gabatar da ƙudirin binciken a Majalisar Dattawa. Sai dai, a yayin wata hira ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ni na yi abin da ya kamata na yi, na kawo ƙuduri, Majalisa ta amince, amma har yanzu ban ji komai ba game da batun.”
Da aka tambaye shi ko akwai kyakkyawan zato na kawo ƙarshen rikicin, Ndume ya ce, “Ina da yaƙinin hakan zai iya faruwa idan gwamnati ta sa himma a kai. Duk da cewa ana kashe kuɗi, amma kuɗaɗen ba su isa ba.” Ya kuma jaddada cewa jami’an tsaro suna buƙatar horo da kayan aiki da kuma ƙarin ƙwarin gwiwa.
A kan batun USAID da kuma rawar da suke takawa a yankin, Ndume ya ce, “Idan aka ba rundunonin tsaro duk abin da suke buƙata tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi za su iya kawo ƙarshen wannan fitinar kamar yadda aka yi a zamanin Jonathan.”
Majalisa ta dakatar da bincikeA ranar 19 ga watan Fabrairun 2025, Majalisar Dattawa ta amince da ƙudurin Ndume na gayyato dukkan shugabannin tsaro domin su bayar da bayani a asirce. Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya ce, “Idan har aka tabbatar cewa kuɗaɗen USAID na zuwa hannun ’yan ta’adda, to hakan zai shafi dangantakar Nijeriya da Amurka.”
Sai dai har yau babu wani bayani game da sakamakon binciken ba. Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Kwamitin Hulɗa da Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu da Jagoran Majalisa, Sanata Opeyemi Bamidele, a kan lamarin, amma ba su amsa kira ko saƙon waya ba.
Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin mutum 15 ƙarƙashin jagorancin Honarabul ɓictor Obuzor domin bincikar lamarin. Sai dai rahoton da Policy and Legislatiɓe Advocacy Centre (PLAC) ta fitar a ranar 19 ga Maris na 2025, ya bayyana cewa Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen, ya dakatar da aikin kwamitin saboda koken da ƙungiyoyin agaji suka yi cewa kwamitin ya wuce iyakar ikonsa ta hanyar neman bayanan sirri na tsawon shekara 10, wanda suka ce ya saɓa wa doka.
PLAC ta ce, “Shugaban Majalisa ya umarci kwamitin da ya dakatar da binciken kuma ya nemi hanyar da za a yi tattaunawa cikin zaman lafiya da haɗin kai.”
Wannan mataki, a cewar PLAC, nasara ce ga ƙungiyoyin agaji don kare ’yancinsu da kuma kauce wa farmaki daga gwamnati.
Ka da a yi watsi da zarge-zargen — Masana tsaroWasu majiyoyin tsaro da masu nazari sun bayyana ra’ayoyinsu kan batun, waɗanda dukkaninsu sun yi aiki a yankin Arewa maso Gabas a lokacin da matsalar Boko Haram ta yi ƙamari.
Haka kuma, Dakta Kabiru Adamu, wani ƙwararre a fannin tsaro da leƙen asiri, ya bayyana ra’ayinsa game da zargin tallafin kuɗi daga USAID, yayin da Shehu Sani, wani mai nazari da sharhi kan rikicin Boko Haram, ya kuma gana da manyan mutane daga sassa daban-daban na ciki da wajen Nijeriya, ya bayyana nasa ra’ayin.
Shehu Sani ya ce, “Na taɓa shiga yankin da Boko Haram ke iko da shi a da, kuma na ga irin halin da al’umma ke ciki. Akwai buƙatar a tantance duk wata alaƙa da ake zargi tsakanin ƙungiyoyin da ke taimaka wa ’yan ta’adda ko don saboda tsaron ƙasa gaba ɗaya.”
Ya ƙara da cewa, “Amma hakan bai kamata ya zama dalilin tauye ayyukan ƙungiyoyin agaji na gaske da ke ƙoƙarin su taimaka wa waɗanda rikici ya tagayyara ba. Akwai hanyoyin da gwamnati za ta iya bi don tabbatar da sahihancin ayyukansu ba tare da takura musu ba.”
Dakta Kabiru Adamu ya ce, “zarge-zargen da ake yi kan USAID da sauran ƙungiyoyin agaji na buƙatar cikakken bincike na tsaro, wanda zai haɗa da shaidu, bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da hukumomin ƙasa da ƙasa. Ba zai yi wa ƙasa daɗi ba idan aka rungumi zarge-zarge ba tare da cikakken bincike ba.”
Ya kuma buƙaci majalisar dokoki ta ƙasa da hukumomin tsaro su tabbatar da cewa an gudanar da duk wani bincike bisa bin doka da tsarin mulki.
Birgediya Janar Kukasheka Usman (mai ritaya) ya ce, “Yayin da akwai yiyuwar wasu tallafin taimako na iya faɗawa hannun ’yan ta’adda ba da gangan ba, amma hakan ba ya nufin cewa ƙungiyoyin taimakon suna da hannu kai tsaye a lamarin. Mafi yawansu suna aiki ne da niyyar taimakawa.”
Kanar A. Ahmed (mai ritaya) ya bayyana cewa, “Tsaron ƙasa ba abu ne da za a ɗauka da wasa ba. Duk wata alama ko zargi da ke nuna yiwuwar haɗin baki tsakanin wasu ƙungiyoyin agaji da ’yan ta’adda dole ne a bincike shi sosai. Amma dole ne a kauce wa sabbaba tashin hankali ko jirkicewar ayyukan ƙungiyoyi masu taimakawa da gaske.”
Sace ɗaliban Chibok ya bai wa ƙasashen waje damar kutsowaKanar A. Ahmed (mai ritaya) wanda ya yi aiki a yankin Arewa maso Gabas inda ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a lokacin da rikicin Boko Haram ya fi ƙamari, ya bayyana yadda ƙungiyoyin agaji na ƙasashen waje suka shiga yankin Arewa maso Gabas, a matsayin dalilin da ya sa ake zargin su, tare da bin diddigin hanyoyin samun kuɗaɗen Boko Haram tun daga farko.
A cewarsa, “Sace ɗaliban Chibok daga makaranta a ranar 14 ga Afrilu, 2014, ne ya jawo hankalin duniya kan Boko Haram tare da sa ƙungiyoyin agaji na ƙasashen waje suka yi gaggawar shiga domin taimaka wa al’ummomin da rikicin ya shafa. Hanzarin da ƙungiyoyin suka yi ya zo ne daidai lokacin da Boko Haram ke cikin yanayi mafi haɗari, lokacin da ta’addanci na duniya ke kan ƙololuwa a wurare da dama.
“Wannan ne ya haifar da zargin cewa ƙungiyoyin suna taimaka wa ’yan ta’adda ta kowane fanni. Duk da cewa waɗannan zarge-zarge ne, amma suna da nauyi kuma ba za a iya yin watsi da su cikin sauƙi ba.
“Kafin shekarar 2014, lokacin da ba a samu waɗannan ƙungiyoyin a yankunan da rikicin ke faruwa ba, babu irin waɗannan zarge-zargen. Na taɓa aiki a irin waɗannan yankunan tare da ƙungiyoyin agaji, na kama manyan membobin Boko Haram na yi musu tambayoyi da bincike, amma har yanzu babu wata sahihiyar shaida da ke nuna cewa ƙungiyoyin suna taimaka wa Boko kai tsaye da kuɗi.
“Duk kayan aikin da Boko Haram ke amfani da su na cikin gida ne, ko kuma suna amfani da kuɗin da suka samu daga aikata laifuffuka a yankin Sahel da Maghreb, kuma an bincike su, an rubuta su a takardu,” in ji shi.
Amma ya ce muddin USAID da ƙungiyoyin agaji suna aiki a yankunan da ake fama da rikici, kuma muddin zarge-zargen ba su tsaya ba, to Boko Haram za ta ci gaba da cin gajiyar kayan agaji kai tsaye da kuma a kaikaice.
A cewarsa, a farko-farkon kafa Boko Haram a ƙarkashin Muhammad Yusuf, kafin su zama ’yan tashin hankali, kuɗin da suke amfani da su suna fitowa ne daga gudummawar mambobi da noma da tallafi daga wasu masu kuɗi da ’yan siyasa, da kuma sana’o’in da suka shafi sayar da kayan addini.
Kanar Ahmed ya jaddada cewa, babu shakka USAID da sauran ƙungiyoyin agaji suna da babbar rawar da suke takawa a fannin bayar da agaji musamman a fannonin kiwon lafiya da ilimi.
Rashin bayanan kuɗi na haddasa shakku — KukashekaBirgediya-Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya), tsohon Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin ƙasa ta Nijeriya daga 2015 zuwa 2019, kuma kafin haka ya riƙe matsayin Kakakin Rundunar a Maiduguri cibiyar rikicin Boko Haram, ya ce, “Zargin da ake danganta USAID da sauran ƙungiyoyin agaji da tallafa wa Boko Haram yana ci gaba da yawo ne saboda yadda aikin agaji ke da sarƙaƙiya a yankunan da rikicin ya shafa da kuma rashin shaidar da za a iya tantancewa.
“Duk da cewa manyan jami’an gwamnati da sojoji suna nuna damuwa, matsalar ita ce, ba a iya bin bayanan da ke tabbatar da cewa kuɗin da ake bayarwa da hannun jari na ’yan ta’adda ne, saboda galibin kuɗaɗen ana tafiyar da su ne ta hanyar hannu da hannu ba tare da tsarin bankuna ba.
“Haka kuma, kasancewar an hana shiga wasu wurare ya sa da wahala a gano kai tsaye dangantakar agajin da ake bayarwa da ayyukan ta’addanci. A maimakon zargi, hanya mafi inganci ita ce ƙara ƙarfafa amana da nuna gaskiya a ayyukan agaji.
“Wasu ƙungiyoyin agaji suna aiki ne bisa sahihin manufa ta agazawa, kuma suna shiga inda gwamnati ba za ta iya shiga kullum ba, ko da yake wasu daga cikinsu sun kauce daga dokokin da aka shimfica.”
Rashin amanaDakta Kabiru Adamu, ƙwararre ne a fannin yaƙi da ta’addanci kuma Shugaban Kamfanin Beacon Consulting wanda ke sa ido kan matsalolin tsaro musamman a Nijeriya, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ko da yake USAID da ƙungiyoyin da ke tallafawa sun sha musanta zargin da ake musu na taimaka wa ayyukan ta’addanci kai tsaye ko ta wata hanyar, musamman na Boko Haram da wasu ƙungiyoyi, amma zarge-zargen na ci gaba da fitowa daga ’yan majalisar dokokin Nijeriya da na Amurka da kuma binciken da gwamnati ke yi.
“Duk da cewa babu wata sahihiyar shaida da ke tabbatar da cewa kuɗaɗen agaji suna zuwa kai tsaye wajen ta’addanci, zargin yana nuna irin rashin amana da kuma rikitarwa da ke tattare da aikin agaji na ƙasashen waje a yankunan da ake rikici.
“USAID ta sha musanta wannan zargi kuma ta jaddada niyyarta na ci gaba da bayar da taimako cikin gaskiya da adalci, tare da Allah wadai da ayyukan Boko Haram. Haka kuma wasu ƙungiyoyin agajin da ke aiki a Nijeriya sun koka cewa irin waɗannan binciken suna tauye musu damar yin aiki, kuma hakan na iya janyo cikas ga tallafin da suke bai wa mabuƙata.
“Har ila yau, ana cewa Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta dakatar da wani bincike gaba ɗaya kan ƙungiyoyin agaji, saboda tsoron kar hakan ya haifar da cin zarafin ƙungiyoyin fararen hula na gaskiya.”
A cewarsa, abin da ke sa zargin ya ci gaba ya haɗa da rashin bayyana hanyoyin samun kuɗin ta’addanci, kasancewar Boko Haram da sauran ƙungiyoyi suna amfani da hanyoyi daban-daban kamar gudummawa daga waje da karɓar kuɗin fansa da fashi da fataucin mutane da makamai da kuma cin gajiyar kasuwannin kuɗi na cikin gida.
“Wannan yanayin da ke da rikitarwa ya sa da wuya a tantance ta inda kuɗin ke zuwa. Haka kuma tafiyar da aikin agaji a wuraren da ake rikici irin su Arewa maso Gabas yana tattare da ƙalubale masu yawa sosai.”
Dakta Adamu ya ƙara da cewa: “Zargin da ake yi na iya fitowa daga ɓangaren siyasa, ko dai na cikin gida ko na waje. Wasu lokuta ana amfani da irin wannan zargin ne domin kauce wa zargi, ko neman samun ƙarfin siyasa, ko kuma rage darajar ƙungiyoyin agaji na waje.”
A binciki zargin tallafa wa ta’addanci — Janar MusaYunƙuri da dama da aka yi don samun martanin hukumomi daga Hedikwatar Tsaro kan ko shugabannin tsaron sun gana da shugabannin Majalisar Dokoki ta ƙasa ya ci tura. Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Birgediya-Janar Tukur Gusau, ya mayar da wakilinmu ga Daraktan Ayyukan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye.
Alamun saƙon da aka tura wa Manjo-Janar Kangye ta manhajar WhatsApp sun nuna cewa ya karanta saƙon, amma bai mayar da martani ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.
A farkon shekarar nan, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, wanda ya sha jaddada rawar da tallafin waje ke takawa wajen ci gaban ayyukan ta’addanci a Nijeriya.
Janar Musa na ci gaba da tambayar cewa; ta yaya ƙungiyoyin ta’adda a Nijeriya ke iya gudanar da ayyukansu duk da farmakin da sojoji ke kai musu? Ya ɗora alhakin ci gaba da ayyukan ta’addanci kan wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ke samar da kuɗin da kayan aiki ga ƙungiyoyin.
A lokuta da dama, yakan nuna damuwa game da ayyukan wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na
ƙasa da ƙasa da ke aiki a yankunan da ake rikici, musamman yankin Arewa maso Gabas. Ya zargi wasunsu da taimaka wa ƙungiyoyin ta’adda ta hanyar horo da tallafi, wanda hakan ke yin cikas ga kawo ƙarshen hare-haren.
Haka nan ya koka da yadda wasu ƙungiyoyin ke ɗaukar matakai masu ban mamaki kamar biyan haya na shekaru goma a wuraren da ake fama da rikici. Ya tambaya cewa shin ko ƙungiyoyin na da tabbacin cewa rikicin zai ɗauki shekaru goma ne?
Janar Musa ya ce, “A yanzu haka, sama da ’yan Boko Haram 120,000 sun miƙa wuya, kuma mafi yawansu sun zo da maƙudan kuɗi. Daga ina suka samo kuɗin? Su waye ke ba su kuɗin? Ta yaya suka sami horo da makamai?”
A wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera a watan Janairu 2025, Janar Musa ya roƙi Majalisar ɗinkin Duniya da ta gudanar da bincike kan hanyoyin samun kuɗaɗe da horon Boko Haram. Wannan kiran ya biyo bayan bayanan sirri da ke cewa Boko Haram da ISWAP sun fara amfani da jiragen leƙen asiri marasa matuƙi domin sa ido kafin kai hari ga jami’an tsaro.
Ya ce, “Majalisar ɗinkin Duniya (MDD) ya kamata ta shigo cikin wannan lamarin domin mu gano asalin kuɗaɗen. Aiki ne na duniya, mu ba mu da ikon daƙile hakan.”
Zargin USAID a Majalisar AmurkaBinciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa kamar yadda lamarin yake a Nijeriya, babu wata sahihiyar bincike da gwamnatin Amurka ta fara kan zargin da ɗan Majalisar Dokokin ƙasar, Perry, ya yi cewa USAID na tallafa wa Boko Haram da ISIS.
Maimaikon haka, amsar hukumomin Amurka ta fi karkata ne ga musanta zargin da kuma faɗar cewa ana da tsari mai kyau na kula da yadda ake amfani da kuɗin agaji ba tare da soma wani sabon bincike ba.
Wata majiyarmu a Washington, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce, “Ina zaune a Amurka, kuma zan iya tabbatar maka cewa gwamnatin ƙasar na kallon furucin Perry a matsayin hayaniya kawai daga ɗan adawa.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa jim kaɗan bayan zargin da Perry ya yi, Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fito fili ya ce akwai tsare-tsare na duba yadda ake gudanar da tallafin, kuma za su binciki duk wani amfani da kuɗin da aka samu hujja a kansa.
Jakadan Amurka, Richard Mills, ya ce, “Babu wata shaida da ke nuna cewa USAID na tallafa wa Boko Haram.” Ya ƙara da cewa duk wata hujja mai inganci za ta sa a fara bincike nan da nan tare da haɗin gwiwar hukumomin Nijeriya.
Masu horon ’yan ta’adda daga ƙasar wajeA wata tattaunawa da Zagazola Makama, ƙwararre kan yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas, ya bayyana cewa wasu majiyoyi sun tabbatar masa da cewa akwai mayaƙa daga ƙasashen waje ’yan Ƙungiyar ISIS-Khorasan (ISIS-K) da ke aiki tare da ISWAP. Ya kuma wallafa abin da ya rubuta dangane da haka: “A watan Disamba 2024, aƙalla mutane tara daga ƙasashen waje, ciki har da fararen fata biyu da wasu bakwai, sun bayyana a ƙananan hukumomin Monguno da Marte a Jihar Borno.”
“Mayaƙan da ake zargin sun fito ne daga Pakistan da Afghanistan, sun zo ɗauke da makamai da jirage marasa matuƙa da kyamarori da na’urorin naɗar sauti da kundin rubutu, suna tattara bayanai a yankunan da ISWAP ke iko da su. Suna magana da harshen Ingilishi da Larabci, tare da fassarar wani ɗan ISWAP da ya iya Kanuri da Hausa.
“Makonni uku bayan haka, a ranar 3 ga watan Janairun 2025, da misalin ƙarfe 7:44 na yamma, ƙungiyar ta dawo tare da rakiyar mayaƙan ISWAP da ke kan babura. A wannan ziyara, an ga suna tambaya kan yadda ISWAP ke karɓar haraji da yadda suke iko da noma da kamun kifi da kasuwanci.
“An gano cewa kafin su kai kowane hari, suna tura jirage marasa matuƙa domin duba yankin. Sun shafe kwanaki suna leƙen asiri kafin a mayar da su Kusuma, hedikwatar ISWAP da ke Marte, da daddare cikin tsauraran matakan tsaro.
“An ruwaito cewa sukan bi ta cikin ruwa da safe suna zagayawa yankin tafkin Chadi kafin su koma da dare. A yayin ziyarar, mayaƙan na waje suna ɗaukar hotuna da rubucerubuce wanda ya nuna ko dai suna shirya kayan yaɗa labarai ko kuma suna nazarin dabarun ISWAP domin wasu ayyuka a gaba.
“Wani sabon bidiyo da ISWAP ta saki ta hannun AMAQta tabbatar da cewa mayaƙan ISIS daga waje na horar da abokan aikinsu na yammacin Afirka a yankin Tafkin Chadi,” in ji shi.
Zarge-zarge daga ’yan siyasar NijeriyaJaridar Aminiya ta kawo wasu zarge-zarge da aka taɓa yi wa wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a Arewa maso Gabas.
A shekarar 2019, bayan dawowa daga Borno a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ndume ya zargi wasu ƙungiyoyi da haɗa baki da Boko Haram. Ya ce, “Wasu ƙungiyoyin agaji a yankin na haɗa kai da ’yan ta’adda, suna ba su bayanai da makamai da sauran abubuwa.”
Haka kuma, wani jami’in tsaro a wancan shekarar ya ce wani kwamandan Boko Haram da aka kama ya amsa cewa suna samun tallafi daga ƙungiyoyi. “Wanda aka kama ya tabbatar mana cewa suna samun abinci da magunguna daga ƙungiyoyi masu zaman kansu,” in ji jami’in.
Har ila yau a 2019, a zaman Majalisar Wakilai, Honarabul Mohammed Tahir Monguno, wanda yanzu shi ne Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, ya nemi a gudanar da bincike kan ƙungiyoyin da ake zargin na tallafa wa Boko Haram.
ɗan majalisar ya ce, “Ya kamata mu binciki duk ayyukan ƙungiyoyin agaji da ke aiki a ƙasar nan dangane da yiwuwar alaƙarsu da Boko Haram.”
Haka nan, Honarabul Gudaji Kazaure a lokacin da yake wakiltar mazablɓarsa a Majalisar Wakilai ya yi kira yayin zaman Majalisa cewa, “Abu mafi muhimmanci shi ne shugaban ƙasa ya gane cewa akwai ƙungiyoyin agaji da ke bai wa ’yan ta’adda magani da tallafi da abinci da sauransu. Idan ba mu dakatar da su ba… ba za mu iya cin nasara a wannan yaƙi ba.”
A baya-bayan nan, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya buƙaci a gudanar da bincike bayan an kama wata ƙungiya da ke koyar da dabarun amfani da makamai a cikin wani otal.
Wani bayani daga gwamnati ya ce, “Gwamna Zulum ya bayar da umarnin rufe otal ɗin tare da dakatar da ACTED daga duk wani aikin agaji a jihar har sai an kammala binciken da ’yan sanda ke yi,”
Aikin USAID a Arewa Maso GabasKafin dakatar da tallafinsu da Shugaba Donald Trump ya yi, Hukumar USAID na daga cikin manyan masu bayar da agajin jin ƙai a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya tun daga lokacin da rikicin Boko Haram ya fara.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar tana bayar da fiye da kaso 50 cikin 100 na abinci ga yara masu fama da matsanancin rashin abinci. Haka kuma, tana tallafa wa ayyukan kiwon lafiyar mata da na haihuwa a sansanonin ’yan gudun hijira da kuma karkara.
USAID ta kuma bayar da tallafi wajen gina matsuguni, samar da ruwan sha da kuma ayyukan tsafta ga al’ummomin da rikici ya raba da muhallansu.