Dalilin da muka soke Hawan Bariki — Masarautar Zazzau
Published: 31st, March 2025 GMT
Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah.
A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi dakon wadanda ke haye-hayen dawakan a gefen titi su ma suna yi wa Sarki gaisuwar ban girma.
Sarki yakan jagoranci tawagar masarautar ta Zazzau inda zai ratsa ta cikin garin Zazzau sannan ya shiga unguwar Sabon Gari inda zai ziyarci Gwamna a gidan da aka tanada tun zamanin turawan mulkin mallaka.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar, ya ce an soke hawan sakamakon dalilai na aikin gyaran titi da shimfida sabuwar kwalta da ake yi a kan hanyar Kofar Doka zuwa kwanar Agoro.
Ya ce wannan aikin hanya da ake kan yi zai kawo cikas ga masu haye-hayen dawakai da kuma al’umma baki daya.
“Saboda haka wannan shi ne dalilin da Masarautar Zazzau ta soke Hawan Barikin da ake gudanar a washegarin Sallah karama” a cewar sanarwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hawan Bariki masarautar zazzau Masarautar Zazzau
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.
Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Ukuwannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan