Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
Published: 31st, March 2025 GMT
Nijar ta fice daga rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Tafkin Chadi da ke yammacin Afirka yayin da take ƙoƙarin inganta tsaro kan albarkatun mai a cikin gida.
A shekarar 2015 ce Nijeriya da Chadi da Kamaru da Nijar suka sake farfaɗo da rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), wacce aka ƙirƙira a shekarar 1994 don yaƙi da ƙungiyoyin jihadi a kewayen Tafkin Chadi.
Sai dai har yanzu ana ci gaba samun rarrabuwar kai da matsalar rashin daidaito na hana rundunar samun nasara sosai, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin cin karensu ba babbaka.
Kamfanin Dillancin Labaran Reuters da ya ruwaito sanarwar gwamnatin ƙasar Nijar ɗin ya ce kawo yanzu MNJTF ba ta yi tsokaci game da ficewar Nijar ɗin ba, yana mai ƙarawa da cewa babu tabbas game da yadda matakin zai yi tasiri kan aikin rundunar a nan gaba.
Yankin Tafkin Chadi yana fama da hare-haren ‘yan bindiga ciki har da ‘yan kungiyar ISWAP da Boko Haram, waɗanda suka ƙaddamar da yaƙi a arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2009 kuma sun kashe dubban mutane.
A bara, Chadi ta yi barazanar ficewa daga MNJTF bayan an kashe sojojinta kusan 40 a wani harin da aka kai wani sansanin soji.
Nijar tana rage hulɗa da wasu maƙwabtanta tun bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamantin Shugaba Mohamed Bazoum a shekarar 2023. Tare da Burkina Faso da Mali – ƙasashe maƙwabta, inda sojoji suka karɓe kwanan nan – ta janye daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a shekarar 2024.
Sojojin da ke mulki a Nijar, da suka yi shelar tsarin miƙa mulki na shekara biyar, sun yi alƙawarin tabbatar da tsaro a ƙasar, wadda ‘yan ci-rani da masu safarar mutane ke ƙetarewa ta cikin gagarumar hamadar arewacinta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Nijar
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Dakatar Da Bai Wa ‘Yan Kasar Nijar Bisa Shiga Cikin Kasarta
Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba.
Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli.
Wannan matakin na Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba da ya shude ne dai Amurka ta kammala dauke sojojinta daga kasar Nijar bayan da gwamnatin sojan kasar ta umarce su, su fice daga kasar.
Da akwai sojojin Amurka da sun kai 1000 a cikin jamhuriyar Nijar, da janye su yake a matsayin kwankwasar kan Amurka da rage tasirinta a yammacin Afirka.
Gabanin juyin mulkin da aka yi a kasar dai Amurka tana amfani da wannan cibiyar a abinda take kira fada da ta’addaci a yammacin Afirka. Sai dai kuma hakan bai hana ci gaba da yaduwar ayyukan ta’addanci a cikin kasashen na yammacin Afirka ba.