Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
Published: 31st, March 2025 GMT
A Bikin Yawan Sallah na Jafi da aka yi a fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna.
Sarkin ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, kuma haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya zai hana rikice-rikice da ke barazana ga jihar.
“Ina roƙon manoma da makiyaya da su zauna lafiya don guje wa rigingimu.
“Kowa yana da haƙƙin tabbatar da zaman lafiya domin hakan na kawo ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma,” in ji Sarkin.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa masarautar Gombe za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa.
Sarkin ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma da ɗaukar matakan tsaro, musamman samar da motocin aiki ga jami’an tsaro.
Bikin hawan sallah na Jafi ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Gwamnan Jihar Gombe da wasu manyan jami’an gwamnati, inda aka jaddada buƙatar haɗin kai da zaman lafiya a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Makiyaya sarki Zaman lafiya manoma da makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu.
Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa.
“Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke cikin daji,” in ji shi.
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasuSanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin da ya wuce tunanin dan Adam.
“Ko jiya ma, na samu kiran gaggawa cewa an kashe sama da ’yan banga 10 a wani yankin da ke tsakanin Karamar Hukumar Hawul ta Jihar Borno da garin Garkida a Jihar Adamawa.
“Al’ummata na fama da munanan asara ba tare da wani faɗa ba. A cikin wata guda da ya gabata kaɗai, an kashe sama da mutum dari a hare-hare da dama yankunan Sabon Gari da Izge da Kirawa da Pulka da Damboada Chibok da Askira Uba da wasu da yawa da ba zan iya lissafawa ba,” in ji Sanata Ndume.