Pezeshkian: Iran Ba Za Ta Yi Tattaunawa Kai Tsaye Da Amurka Ba
Published: 30th, March 2025 GMT
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye.
Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian ya tabbatar da cewa an isar da martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump ta hanyar Oman.
Ya jaddada cewa, yayin da Iran ta yi watsi da tattaunawar kai tsaye, ba ta taba rufe kofar yin shawarwarin kai tsaye ba matukar dai aka cimma wani abu da bai yi karo da manufofin Iran ba.
Ya kara da cewa, “Kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba toshe hanyoyin yin shawarwari kai tsaye a baya ba, amsar wasikar ta kara tababtar da hakan, tare da tabbatar da cewa sakamakon tattaunawar da za a yi wadda ba ta kai tsaye ba, it ace za ta fayace yiwuwar yin tattanawar ta kai tsaye ko akasin hakan.
Shugaban na Iran ya alakanta kalubalen da ake fuskanta a tsarin tattaunawar da rashin matsaya guda daga bangaren Amurka, yana mai jaddada cewa dole ne Amurka ta gyara kura-kuran da aka yi a baya tare da maido da aminci da gaskiya da kuma cika alkawali.
Pezeshkian ya yi nuni da cewa, “Wannan zai zama gwaji a kan n yadda Amurkawa za su iya tabbatar da ci gaban tattaunawar.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo janar Musawi ya ce, ko kadan Iran ba ta yarda ko gaskata alkawullan Amurka,balle kuma zancen ‘yan sahayoniya.
Babban hafsan hafsoshin sojan na Iran ya kuma kara da cewa, sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar duk wan igigi na abokan gaba.
Manjo janar Musawi ya bayyana hakan ne dai a lokacin da ya yi tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Tajikistan Manjo janar Imam Ali Sabir Zadeh.
A nashi gefen, ministan tsaron kasar ta Tajikistan, ya fara da yi wa janar Musawi murnar zabarsa sabon hafsan hafsoshin sojan kasar ta Iran, sannan kuma ya nuna bakin cikinsa akan rashin kwamandojin sojan Iran da su ka yi shahada a sanadiyyar harin ta’addancin HKI.
Manjo janar Imam Ali Sabir Zadeh ya kuma kara da cewa, al’ummar kasar Tajikinstan sun yi bakin ciki, don haka suna isar da ta’aziyyarsu ga al’ummar Iran.
Har ila yau minstan tsaron kasar ta Tajikistan ya yi ishara da tarayya akan harshe da al’ada da kasashen biyu su ka yi, haka nan kuma tarihi.
Haka nan kuma manjo janar Musawi ya yi wa Tajikistan godiya akan yadda ta kasance a tare da Iran a lokacin yakin kwanaki 12, lamarin da ya kara karfin alakar kasashen biyu.