Aminiya:
2025-06-15@18:05:33 GMT

Azumin Sitta Shawwal a Musulunci

Published: 31st, March 2025 GMT

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, a ranar Asabar ce muka kawo karshen azumin watan Ramadan mai albarka na bana.

Saudiyya ta kama wasu ’yan Najeriya da suka daga hotunan ’yan siyasa a Harami An kai hare-haren ta’addanci fiye da dubu 5 cikin shekaru 3 a Yammacin Afrika

Yanzu kuma za mu duba wasu batutuwa da suka shafi Azumin Sitta Shawwal, musamman a Mazhabar Malikiyya wadda muke bi a nan Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka.

Wani lokaci akan samu wadansu cikinmu har ma da malamai su soki azumin da sunan bai inganta ba a Mazhabar Malakiyya, don haka ne muka bijiro da fatawoyin malaman wannan mazhaba.

Azumin Sitta Shawwal a tsakanin mustahabbanci da karahanci Ibn Jaziy ya ambaci cewa azumin Sitta Shawwal na daga cikin mustahabbai, inda ya ce: “Mustahabbi ne azumtar watanni masu alfarma da kwana shida a watan Shawwal.”

Shi kuma Sidi Khalil ya sanya azumin Sitta Shawwal a cikin makaruhai inda ya ce: “An ki baragurbi kamar Sitta Shawwal.”

To amma abin da ya fi zama daidai a wurin akasarin malaman Mazhabar Malikiyya shi ne mustahabbi ne a azumci kwana shida a cikin watan Shawwal (Sitta Shawwal), saboda fadinsa (SAW): “Wanda ya azumci Ramadan sannan ya bi shi da Sitta Shawwal kamar ya yi azumin shekara ce.” Muslim ya ruwaito.

Wannan saboda kowane aiki yana da lada goma, azumin watan Ramadan yana daidai da wata goma, na kwana shida na Shawwal kuma wata biyu.

Masu dogaro da karahanci suna yi ne kawai don ka’idar nan ta toshe kafar auka wa barna (Saddul Zari’a).

Wato Imam Malik (Rahimahullah) ya karhanta bin Ramadan da Sitta Shawwal ne don kada jahilai su mayar da hakan wajibi idan zamani ya yi tsawo, ta yadda za su kara a cikin addini abin da ba ya cikinsa.

Wato yana kiyaye nassin shari’a kada a yi tawili mutane su shar’anta wa kansu wajibcin abin da ba a wajabta musu ba.

Amma idan mutum ya san addini ya san cewa azumin Sitta Shawwal ba wajibi ba ne, ya halatta ya azumce shi a kashin kansa saboda hukunci yana juya ne tare da illarsa da kyautata shi ko rashinsa.

Don haka malamanmu suka ce: “Karhancin an kayyade shi ne da sadar da shi da Ramadan ko kuma a yi su a jere, ko kuma mutum ya rika nuna wa mutane yana yin azuminsu idan ya kasance wanda ake koyi da shi.

Don haka idan aka rasa wadannan babu karhanci a ciki.”

Alkhidabi ya ce: “Malik (Rahimahullah) ya karhanta haka (azumin Sitta Shawwal) ne tsoron kada a riskar da Ramadan da abin da ba ya cikinsa daga bangaren jahilai da masu kekasar zuciya. Amma mutum a kashin kansa ba a karhanta masa azumtarsu ba. (Mawahibul Jalili na Khidabi, Mujalladi na 2 shafi na 414).

Shi kuwa Ad-Dardiyar ya ce: “An karhanta wa wanda ake koyi da shi ya sadar da shi (Sitta Shawwal) da Ramadan a jere kuma ya bayyana hakan yana mai kudirta Sunnah ce a sadar da su.” (As-Sharhul Kabir Mujalladi na 1 shafi na 51).

Al-Khurshiy ya ce: “Wannan (karhancin) idan ya azumce su ne yana mai sadar da su da Ramadan kuma ya yi su a jere kuma yana bayyana hakan tare da kudirta sunnacin sadar da su. Idan bai yi haka ba, babu karhanci.” (Mukhtasar Khalil na Alkhurshiy, mujalladi na 2 shafi na 243).

Da wadannan hujjoji ya bayyana cewa babu tufka da warwara kan abin da Ibn Jaziy ya tafi a kansa na sanya wannan azumi a cikin mustahbbai da abin da mai Mukhtasar Khalil ya tsayu a kansa na sanya azumin a matsayin makaruhi.

Maganar mai Mukhtasar Khalil ta tafi ce a kan idan aka yi azumin Sitta Shawwal a jere tare da sadar da su da Ramadan, wato ana kare Ramadan mutum ya zarce da su kuma ya yi su a jere.

Kuma maganar Ibn Jaziy tana nufin idan aka azumce su a kwanaki daban-daban kuma ba a sadar da su da Ramadan ba.

Wannan daidaito a tsakanin maganganun biyu sun samu ne don kiyaye abin da ya fi shahara a mazhabar.

Kuma za a iya daukar Ibn Jaziy ya zabi mustahabbantawar mudalaki bisa tafiya a kan cewa maganar Imam Malik ta faru ne saboda Hadisin da ya gabata bai riske shi ba, kamar yadda malamai da dama suka ambaci haka, (akwai maganganu cewa wannan Hadisi bai riski Malik ba).” Allah ne Mafi sani.

Fatawar Sheikh Al-Iydu bin Zaddah Aljaza’iriy.

Shin ya halatta a yi azumin Sitta Shawwal a wuni na biyu bayan Idi?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah. Azumin Sitta Shawwal da lokacin fara shi Ya halatta ga Musulmi ya fara azumin Sitta Shawwal bayan Idi, ma’ana a rana ta biyu na watan Shawwal.

Wannan saboda abin da Imam Muslim ya ruwaito ne a sahihinsa daga Abu Ayyub Al-Ansari (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya azumci Ramadan sannan ya bi shi da shida daga cikin Shawwal kamar ya yi azumin shekara ne.”

Fadinsa (SAW) “Daga cikin Shawwal” manuniya ce da ta kunshi daukacin ranakun watan Shawwal in aka cire ranar Idi, saboda tabbatar hani a kan azumtar ranar Idi.

Idin Fidir kuwa rana daya ce ba ranaku ne masu yawa ba kamar Layya wanda aka hada masa da hanin Ranakun Tashriki guda uku, wadanda a kansu (SAW) ya ce: “Ranakun Tashriki-Ranaku ne na ci da sha da ambaton Allah.”

Bisa ga abin da ya gabata: “Babu laifi ko karhanci a fara azumin Sitta Shawwal a rana ta biyu na watan Shawwal, hakika haka ma na iya zama mafi falala saboda abin da ke cikinsa na gaggawa da rigegeniya zuwa ga yin ayyukan alheri.

Kuma da abin da ke cikinsa na tabbatar da bin abin da ke cikin fadinsa (SAW): “Wanda ya azumci Ramadan sannan ya bi shi da shida daga cikin Shawwal kamar ya yi azumin shekara ne.”

Kuma isharar da ta fi a kan wanda ake bin sa azumin Ramadan, ya fi kyau a kansa ya gabatar da biyan a kan azumin nafila, domin Musulmi bai hakke cewa ya yi azumin Ramadan sai ya biya bashin Ramadan da ke kansa.

Bai hakkake ya bi bayan Ramadan da Sitta Shawwal har sai ya azumcin farilla daga farko.

Wannan saboda samuwar hadisan da suka yi bayanin ma’anar azumin shekara kuma lallai hakan na cikin babin aiki daya lada goma a madadinsa.

Misali Hadisin da Imam Ahmad da wadansu suka ruwaito daga Sauban (RA) cewa “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Azumin Ramadan daidai yake da – azumin wata goma, azumin wuni shida a bayansa na daidai da wata biyu, wannan ne cikar shekara.” Allah (SWT) ne Mafi sani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ramadan Sitta Shawwal azumin shekara ya yi azumin sadar da su

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta zargin da wasu ke yi cewa ta karɓo sabon bashi na dala miliyan 6.6 daga watan Yuni zuwa Disamba 2023, tana mai cewa wannan zargi ƙarya ne marar tushe da aka ƙirƙira domin ɓata mata suna. Wannan na zuwa ne bayan wata ƙungiyar siyasa mai suna APC Patriotic Volunteers ta yi zargin cewa gwamnatin NNPP mai ci a jihar ta karɓo bashi daga ƙasashen waje ba tare da bayyana hakan ba.

Darakta Janar na Ofishin Gudanar da Basussuka a jihar, Dr. Hamisu Sadi Ali, ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta hau mulki, ba ta karɓi wani sabon bashi ko na gida ko na waje ba, balle a ɓoye shi daga idon jama’a. Ya ce duk wani bashi da gwamnatin jihar ke aiki da shi a halin yanzu an gada ne daga gwamnatin da ta gabata.

Kocin Kano Pillars Usman Abdullahi Ya Ajiye Aikinsa Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano

Dr. Ali ya kuma ƙalubalanci tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Alhaji, wanda ya jagoranci ƙungiyar da ta yi zargin, yana mai cewa duk wanda ke da hujjar wannan zargi ya fito da takardun da ke tabbatar da hakan – ciki har da sunan mai bayar da bashin, kwafen yarjejeniyar, dalilin karɓa, da tsarin biyan bashin.

A cewarsa, akwai doka mai ƙarfi da ke kula da basussuka a jihar, wadda gwamnatin APC ta gabata ta kafa a 2021. Wannan doka ta bai wa ofishinsa ikon karɓar bashi cikin tsarin doka da cikakken sahihanci, kuma ba wani bashi da aka karɓa tun bayan 2023. Ya ce gwamnati na gudanar da harkokinta cikin gaskiya da rikon amana, kuma ba za ta lamunci ƙarya da siyasar ɓatanci ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Kakkabo Jiragen Yakin Isra’ila Biyu Kirar F-35
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci
  • Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Nada Sabbin Kwamandojin Soja Da Dakarun Kare Juyin Musulunci
  • Kwamadan Sararin Samaniyar Iran Na Dakarun Kare Juyi Haji Zadeh Yana Cikin Wadanda Su Ka Yi Shahada
  • Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
  • Gwamnan Gombe Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Daba Suka Yi Wa Amadi Kasiran
  • Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)
  • Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna
  • Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India