Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya
Published: 11th, November 2025 GMT
Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake yi na cimma matsaya ta siyasa.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Masar, Tamim Khallaf, ya bayyana cewa Minista Abdel-Aty ya tabbatar a lokacin taron cewa matsayin Masar kan rikicin Libya, ya dogara ne kan bin tsarin siyasa da Libya take a kai ba tare da wani umarni ko tsangwama daga waje ba, a matsayin hanya daya tilo ta dawo da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.
Abdel-Aati ya sake nanata cikakken goyon bayan Masar ga kokarin Wakilin Musamman na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na aiwatar da taswirar Majalisar, yana mai jaddada muhimmancin “ci gaba da aiwatar da ginshiƙanta, wanda ya fi muhimmanci a cikinsu shi ne kafa sabuwar gwamnatin kan kasa wadda za ta shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa a lokaci guda, yayin da yake jaddada buƙatar bin ƙa’idar da aka sanar domin kiyaye sahihancin tsarin siyasa da kuma cimma burin al’ummar Libya na samun kwanciyar hankali da ci gaba.”
Ministan Harkokin Waje ya kuma jaddada muhimmancin janye dukkan sojojin kasashen waje, mayakan kasashen waje da sojojin haya daga yankin Libya ba tare da wani sharaɗi ko jinkiri ba, bisa ga kudurorin kwamitin Tsaro, yana mai la’akari da wannan a matsayin muhimmin sharaɗi don cimma daidaito mai ɗorewa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya November 11, 2025 Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10 November 11, 2025 An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali November 11, 2025 Trump Ya Yi Wa Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama Barazana November 11, 2025 Donald Trump Na Amurka Ya Karbi Bakuncin Shugaban Rikon Kwaryar Kasar Syria Ahmad Shar November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5
Nijeriya da Saudiyya sun Rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna ta shekaru biyar (MoU) don karfafa hadin gwiwar tsaro a tsakanin kasashen guda biyu.
Yarjejeniyar, wacce aka sanar a ranar Talata a cikin wata sanarwa da Ahmed Dan Wudil, Mataimaki na Musamman kan Yada Labarai ga karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya fitar, ta bayyana cewa, hadin gwiwar ta shafi dabarun horar da sojoji, raba bayanan sirri, samar da tsaro, da ayyukan hadin gwiwa.
An sanya hannu a yarjejeniyar ne a Riyadh ta hannun Ministan Tsaro na Nijeriya, Matawalle, da Dr. Khaleed H. Al-Biyari na Saudiyya, ana sa ran yarjejeniyar za ta zama tsarin ci gaban tsaro mai dorewa a fadin kasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin December 10, 2025 Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama December 10, 2025 Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci