2025-10-13@18:08:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 384

«da tazarar haihuwa»:

    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa. Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu. ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a. Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai. Jami’an hukumar daga...
    Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar.   “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem.   A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.   “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
    Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
    Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
    BICTOR IKPEBA – 1997 Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin wadanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997. ADEMOLA LOOKMAN – 2024 A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake buga wasa a kungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar. Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, inda ya zura kwallo uku rigis a raga, sannan ya taka rawar gani sosai a...
    A kan zaben 2027, Abdullahi ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sun yarda za su goyi bayan duk wanda ya lashe zaben fid da gwani. “Dukkan ‘yan takarar shugaban kasarmu sun yarda za su goyi bayan wanda ya ci zaben fid da gwani da jam’iyyar za ta gudanar,” in ji shi. Ya kara bayyana cewa nan gaba kadan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar zai sanar da ranakun zaben fid da gwani a Osun da Ekiti kafin zaben gwamna a kowace jiha. Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Dabid Mark da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da sakataren jam’iyyar na kasa, Ogbeni Rauf da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai da tsohon gwamnan...
    Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya  sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun. An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya  zube a kan titin Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagamu a  daidai  wurin musayar hanyar. Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Kakakin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce lamarin ya janyo tashin gobara. Ya kuma ɗaura laifin haɗarin a kan gudun wuce ƙima...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba. Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci. Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin kai kayan agaji Gaza An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Kwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya faɗa wa BBC Hausa cewa zai bai wa matashi damar tsayawa takara. Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta. Amma hadiminsa, Paul Ibe, ya ce ba a yi wa maganganun Atiku kallo na tsanaki ba, an fahimce su ba daidai ba. Ibe, ya...
    Gwamnaton shugaba Donal Trump na Amurka ta amince da bawa gwamnatin kasar Lebanon dalar Amurka miliyo 190 don sayan makamai da kuma wasu dalar Amurka miliyon 40 don hukumar tsaron cikin gida na kasar Lebanon saboda shirin kwance damarar kungiyar Hizbullah da ke kudancin kasar. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Kamfanin dillancin labaran reuters na fadar haka. Wata majiya a birnin Washington ta fadawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa gwamnatin Trump ta amince da bawa hukumomin tsaro na kasar Lebanon, dalar Amurka miliyon 230 don taimaka mata wajen kwance damarar kungiyar Hizbullah wacce ta hana HKI mamayar kasar. Jami’an gwamnatin kasar Lebanon sun tabbatar da labarin. Majiyar ta kara da cewa wadan nan kudade zasu...
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya.   Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.   “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama wani mahaifi yana yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Mai magana da yawun hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi Sanarwar ta ce mahaifin na daga cikin aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane waɗanda aka cafke a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. TRT ya ruwaito Adekoye na cewa an kuɓutar da mutum 24 a yayin aikin bisa jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello wanda...
    Jami’ar Tianjin wadda aka kafa a shekarar 1895 a matsayin jami’ar Peiyang, ita ce jami’ar zamani ta farko ta kasar Sin kuma ta yi na’am tare da amsa sunanta na yanzu ne a shekarar 1951. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja. Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello....
    Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama akalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja. Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar diyarsa zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraq. Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar safarar...
    Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya. Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki? Wannan shine batun...
    Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi. Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar da suka yi da Lesotho, inda Teboho Mokoena ya taka leda a ranar 21 ga Maris, 2025. FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace...
    Yau Litinin ofishin ‘yan jarida na kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai don bayyana nasarorin da Sin ta samu a fannin ban ruwa a lokacin “shirin raya kasa na 14 na shekaru biyar” . Minista mai kula da harkokin ban ruwa Li Guoying ya bayyana cewa, tun daga farkon shirin, Sin ta fara samun ci gaba mai yawa a fannin gina kayayyakin ban ruwa. A shekarar 2022, kudaden da aka kashe wajen gina ayyukan ruwa sun kai sama da RMB yuan tiriliyan 1 a karon farko, kuma sun ci gaba da kafa tarihi har tsawon shekaru 3. A shekarar 2024, kudaden sun kai tiriliyan 1.3529 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 190. Kuma ana sa ran yawan kudaden da za...
    Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan. Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar...
    Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno. Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom. PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata a kamfanin Dangote Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa An same shi da kwalabe 23 na man fetur da ya ɓoye cikin jaka a lokacin da yake tafiya daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala. Bincike ya gano cewa yana yi wa Boko Haram safarar man fetur, sai dai wannan karon an yi nasarar kama shi. Wanda dai ba shi ne...
    Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ba shi da tushe balle makama, inda ta bayyana shi a matsayin mai cike da ruɗu da rashin inganci. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar “Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar bana, Premium Times ta tabbatar...
    Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899. Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na ƙasar Amurka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan...
    Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na Amuka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da...
    A wani labarin kuma, Jami’an NDLEA sun kama wata ‘yar kasuwa mai shekaru 38, Okolonkwo Ebere Theresa, a ranar Lahadi, 14 ga watan Satumba, bayan da jami’an tsaron jiragen sama na hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Nijeriya tare da hadin gwiwar jami’an hukumar NDLEA suka gano 1.40kg na methamphetamine da ta boye a cikin rigarta domin shiga jirgin saman Katar. A tashar NAHCO da ke filin jirgin saman Legas a ranar Litinin, 15 ga Satumba, NDLEA ta kama wani kayyakin abinci mai kunshe da dauri 40 na methamphetamine mai nauyin kilogiram 2.30 wanda ya nufi Hong Kong ta hanyar jirgin saman Turkish Airlines. An kama wani da ake zargi mai shekaru 59, Umelo Ifeanyi Benatus,...
    Rahotanni daga ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati a sararin samaniya na kasar Sin, sun ce da misalin karfe 1 da minti 35 na sanyin safiyar yau Jumma’a 26 ga wata, bisa hadin-gwiwar dan sama jannati Chen Dong dake cikin kumbo, sauran ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 guda biyu, wato Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da ayyuka har na tsawon sa’o’i 6 a wajen kumbon, inda suka kammala ayyukansu bisa shiri. Ya zuwa yanzu, Chen da Wang sun riga sun koma sashin gwaje-gwaje na Wentian lami lafiya, al’amarin da ya shaida babbar nasarar da suka samu wajen gudanar da ayyuka a wajen kumbon. Yayin da suke wajen kumbon, ’yan sama jannatin biyu sun...
    Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci gaba da cewa, sabon sauyen da aka samar a kasar nan a karkashin dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 ta samar da sabon sauyi, a bangaren gudanar da shugabanci na gari. Shugaban ya kara da cewa, Hukumar musamman a karkashin shugabancin shugaba Tinubu, ta kara zagayewa wajen sanya ido sosai a fannin na sarrafa Mai da Iskar Gas. Ya ce, Hukumar kusana a cikin shekaru...
    Sai kuma fannin fadada dazuzzuka da zai karu zuwa sama da kyubik mita biliyan 24, da mayar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi kan gaba, cikin jimillar ababen hawa da kasar za ta rika sayarwa, da fadada kasuwar carbon ta kasar Sin, ta yadda za ta game dukkanin manyan sassan fitar da hayakin carbon, tare da kafa al’umma mai ingancin rayuwa yayin da ake tunkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985.   A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar Sojoji da Ma’aikatan Kwalejin Horasda Kananan Hafsoshin Soji Ta Jaji Sun Tsara Shirin Samar Da Fahimta Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula.   Rundunar Sojoji da ma’aikatan kwalejin su ta Jaji, ta kammala wani shiri na musamman wanda ke nuna wa ‘yan jarida da sauran masu halartar atisaye, sani da gogewar al’amuran yau da kullum a irin salon rayuwar sojan da ke cikin rukunin.   A wata sanarwa da kakakin kwalejin, Laftanar Kanar Victor Olukoya ya fitar, ya ce an shirya wannan horon ne da nufin samar da kyakkyawar fahimta da hadin gwiwa tsakanin sojoji da masu ruwa da tsaki na farar hula domin samun kyakkyawar alakar aiki wadda a karshe za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron kasa cikin...
    Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi. Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta India (NCB), reshen Chennai, suka kama wasu fakiti guda uku a ofishin aika sakonni. An kama ɗan sandan bogi a Kano Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa A cikin fakitin, an gano tabar wiwi mai nauyin kilo 1.195 da methaqualone giram 200, wanda darajarsa ta haura kimanin Dalar Amurka 240,000 a kasuwar duniya. Bincike ya gano cewa fakitin na da...
      Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai.   Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu ƙwarewa kan harkar ciyar da ɗalibai.   Taron ya mayar da hankali ne wajen duba nasarorin da aka samu cikin watanni goma tun lokacin da aka fara shirin a Ladduga, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.   Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana cewa shirin ya shafi makarantun makiyaya kawai a jihohin Jigawa da Kaduna.   Ya...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gungun wasu mutane da ake zargi da safarar mata zuwa kasar Saudiyya. Hisbah ta dakile yunkurin mutanen ne a yayin da suke kokarin safarar wasu mata hudu daga jihohin Kano da Jigawa da Yobe, ta hannun wakilansu da ke sassan kasashen Yammacin Afirka? Mataimakin Babban Kwamnand Hukumar, Dakta Mujahideen Aminudeen, ya ce masu safarar matan sun yaudarin matan da aka ceto cewa za su yi musu biza zuwa kasar Ghana inda daga nan za su wuce da su zuwa Saudiyya domin sama musu ayyukan yi. An kana daya daga cikin mutanen ne a ranar Lahadi, wanda hakan ya kai ga cafke shugabansu da ake kira Bashir Sani Ibrahim. Ballon d’Or: Wa zai lashe...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula, inda suka kashe mutane 5 da suka hada da yara 3 a kudancin kasar Lebanon Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da mutuwar wasu ‘yan kasar 5 da suka hada da yara uku sakamakon wani hari da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin birnin Bint Jabeil. Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya watsa rahoton cewa: Wani jirgin sama mara matuki na makiya yahudawan sahayoniyya ya kai hari kan wani babur da wata mota dauke da makamai masu linzami a garin Bint Jabeil, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkata. Wannan harin wuce gona da iri ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila...
    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da hana su faɗar albarkacin baki. A cikin wata wasiƙar da suka aike wa shugaban ƙasa ranar 20 ga Satumba, 2025, SERAP da Amnesty sun bayyana cewa ƙarar da DSS ta shigar bisa zargin saƙonnin da ake cewa sun na adawa da Tinubu ya zama wani SLAPP (ƙarar da ake amfani da ita don toshe bakin masu suka). Sun ce irin waɗannan suna haifar da tsoro...
    A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar da Masar ta bayar? Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin haɗe ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji. Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu. Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta...
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar. “Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa. “Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani,...
    Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
    Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi. A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27,...
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana. Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano inda ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyoyin biyu suka shaidi wasan. Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa Kafin yanzu ƙungiyar, mallakar gwamnatin jihar Kano ta yi rashin nasara biyu sannan ta buga canjaras ɗaya a wasanni uku da ta buga a wannan kakar, wannan nasarar da Sai...
    Masanan sun yi gargaɗi yayin da Shugaba Bola Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na sake fasalin ɓangaren lafiya na Nijeriya, inda ya bayyana cewa babu wani ɗan ƙasa da ya kamata ya rasa rayuwarsa saboda rashin wutar lantarki a cibiyoyin lafiya. Yayin da yake jawabi a Taron Tattaunawar Masu Ruwa da Tsaki na Ƙasa kan Wutar Lantarki a Ɓangaren Lafiya, a Ladi Kwali Hall na Continental Hotel, Abuja, Shugaban ƙasa, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya lura cewa rashin wutar lantarki da ke ci gaba a asibitoci na rage ingancin kulawa da kuma jawo asarar rayuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa.   Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar. Domin sauke shirin, latsa nan
    Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba da fifiko kan hadin kai da karfafa jam’iyyar a fadin jihar. Ya ce, “Ina godiya ga daukacin shugabanni da ‘yan jam’iyyar NNPP na Jihar Kuros Riba, ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode muku da kuka karɓe mu, muna matukar farin ciki da shugabancin jam’iyyar a jihar, ina kara baku kwarin guiwa da ku yi aiki tukuru don ganin an samu...
    “Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.   Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba.   “Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Rundunar ’yan sanda ta Jihar Gombe ta samu nasarori a yaƙi da masu aikata laifuka, inda ta kama wata mata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi ’Yan bindiga da masu ɗaukar musu bayanai ba su da bambanci — Gwamnan Sakkwato Ya ce jami’an sashen kwantar da tarzoma na Anti-Violence Squad sun kama matar mai suna Rakiya Ahmed mai shekaru 53 a unguwar Barunde, inda aka same ta da ƙunshi takwas na ganyen wiwi. A cewarsa, an cafke matar ce bayan samun sahihan bayanan sirri daga jama’a, kuma...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwanan baya, kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun mai da matukar hankali kan bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, wanda aka yi a birnin Beijing na kasar Sin a ranar 3 ga wata. Kana, kafofin watsa labarai da dama na kasashe daban daban sun rika amfani da kalmar “Zaman lafiya” a lokacin da suke watsa labarai kan wannan gagarumin biki. Yakin duniya na biyu ya bakanta ran bil Adama, kuma kasar Sin ta cimma nasarar yaki da mamayar dakarun kasar Japan bayan al’ummomin kasar sun shafe tsawon shekaru 14 suna yaki, lamarin da ya ba da muhimmiyar gudummawa ga...
    Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin yaki da zalunci da danniya da Jama’ar Sinawa suka yi, ya sa kasar ta kudiri aniyar yaki da zalunci da danniya a duniya ta rungumi manufar tabbatar da zaman lafiya, inda ta nuna wa duniya cewa, lokacin wariya da danniya, tsarin rayuwar dabbobi (na sama ya buge na kasa), ba zai dore ba amma samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, na sama ya yi...
    Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta. Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12 A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar mutane (wanda aka sakaya sunansa) a wani wurin garejin motoci tare da wasu mata 12 da ake zargi da safarar mutane da ke shirin tafiya Legas. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen. Ganawa da Tinubu: Buƙatun Gwamnonin Arewa maso Gabas Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an rundunar sun kama mutumin ne a wani garejin motoci da ke kan titin Zariya. Hukumar ta bakin mataimakin ta bayyana cewa, jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin OC Muhammad Bashir na garejin motoci sun kama wakilin safarar wanda aka ce ya fito daga Jihar...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar mutane (wanda aka sakaya sunansa) a wani wurin garejin motoci tare da wasu mata 12 da ake zargi da safarar mutane da ke shirin tafiya Legas. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen. Ganawa da Tinubu: Buƙatun Gwamnonin Arewa maso Gabas Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an rundunar sun kama mutumin ne a wani garejin motoci da ke kan titin Zariya. Hukumar ta bakin mataimakin ta bayyana cewa, jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin OC Muhammad Bashir na garejin motoci sun kama wakilin safarar wanda aka ce ya fito daga Jihar...
    Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da...
    Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu.   Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare...
    A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya.   An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa.   Babale ya ce, ana ci gaba da kokarin damke wasu da ake zargi da hannu wajen safarar mutanen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba. Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya. Wannan ya nuna niyyarsu ta hada hannu wajen tunawa da tarihi da kiyaye zaman lafiya da adalci.   Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil...
    Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya yi sanadin ambaliya da lalata ɗaruruwan filayen noma. ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara Daily Trust ta gano cewa ruwan ya fara ƙaruwa a kogi a ’yan kwanakin da suka gabata, kuma a yanzu kogin ya yi ta malala a gefan koguna inda ya haddasa ambaliya a faɗin jihar. Ambaliyar...
    Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta kan rushe kasuwar Alaba Rago mai ɗimbin tarihi a Legas, inda ta bayyana hakan a matsayin babban koma baya ga dubban ’yan kasuwa. A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, ɓarnata kasuwanci da dukiyoyi ya jefa wasu iyalai da dama cikin ƙunci. Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rushe kasuwar mai ɗimbin tarihi ya haifar da asarar kasuwanci da dukiyoyi, tare da kawo cikas ga hanyoyin rayuwar jama’a...
    Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi Ruftawar katanga ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 2 a Zariya El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke...
    Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027. A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance. Damagum wanda ya shafe fiye da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Isra’ila ta kaddamar da wani farmaki ta sama a kan babban birnin kasar Yemen Sanaa a jiya Lahadi, inda ta kai hare-hare a yankin kudu maso gabashin birnin San’a. Wakilin tashar Almayadeen ya bayyana cewa, Isra’ila ta kai harin ne kan wani gidan mai  a kudu maso gabashin birnin San’a mallakin kamfanin mai na kasar Yemen da ke kan titin Al-Sitteen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane  tare da jikkata wasu da dama a lokacin da suke shan mai a motocinsu da sauran ababen hawa a wurin. Kamfanin mai na kasar Yemen ya kuma tabbatar da cewa al’amura sun daidaita an kuma shawo kan gobarar da ta tashi a wurin, tare da kwantar da hankalin ‘yan kasar, kamar yadda wakilin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II.   Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta kara da cewa, “Da isar rundunar, ta fara artabu da ‘yan bindigar, inda ta samu nasarar kashe Uku, tare da kwato bindiga kirar AK-47,” in ji sanarwar.   Kwamishinan ‘yansandan jihar Kebbi, CP Bello M. Sani ya yabawa babban jami’in da jami’ansa bisa wannan namijin kokarin da suka yi. Ya bayyana nasarar a matsayin shaida na kudurin rundunar na kawar da masu aikata munanan laifuka a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jakadann Amurka na musamman a kasar Lebanon Tom Barrack ya bayyana cewa ya yarda da matakan da gwamnatin kasar Lebanon take dauka don kwance damarar kungiyar Hizbulla ta kasar, Shafin yanar gizo na Alarabia na kasar Saudiya ya bayyana cewa Barrack ya shaidawa gwamnatin kasar Lebanon kan cewa yana kirin kungiyar Hizbullah da kuma kasar Iran wadanda dukkaninsu mabiya mazhabar shia ne da sun a cewa su yi aiki da gwamnatin kasar don sasantawa. Kafin haka dai a ranar 7 ga watan Augusta da muke ciki ne gwamnatin kasar Lebanon ta yanke shawarar kwance damarar kungiyar Hizbullah, sannan ta bawa sojojin kasar umurnin wannan aikin. Kuma ta bawa sojojin kan cewa su kammala wannan aikin zuwa watan satumma mai zuwa....
    A yau ake gurfanar da wani majinyaci mai shekaru 40, zai gurfana a kotu, bisa zargin cin zarafin wata likita mai suna Fatima Umar Gamsa a asibitin Ƙwararru na tunawa da marigayi Janar Sani Abatch da ke Damaturu Jihar Yobe. Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Yobe, Dakta Umar Aji, ya ce kungiyar ta kai ƙara gaban ’yan sanda kuma tana jiran hukuncin da kotu za ta yanke. “A yanzu shari’ar tana gaban kotu, kuma ƙungiyar ba za ta ce komai ba har sai ta ji sakamakon hukuncin kotun,” Aji ya jaddada. Wanda ake zargin, Ahmed Usman mazaunin rukunin gidajen Abba Ibrahim da ke Damaturu an tsare shi  a gidan yari na Potiskum har zuwa lokacin da za a saurari...
    Jam’iyyar NNPP wato New Nigeria Peoples Party, ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da ke Jihar Kano. Babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Hassan Adamu ne ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 12:36 na daren Asabar wayewar gari Lahadi. Farfesa Hassan Adamu Shitu, ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 16,198, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC —All Progressives Congress — wanda ya samu ƙuri’u 5,347. Dokta Ali Hassan Kiyawa na jam’iyyar NNPP shi ne ya yi nasara a kan Ahmad Muhammad Kadamu na jam’iyyar APC bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar
    Shin kun san, a lokacin da Sinawa suka hadu da juna, gaisuwar da suke yi ita ce, “Shin ka ci abinci?” Wannan gaisuwa mai sauki tana nuna damuwar mutanen dake rayuwa bisa aikin noma, wato ma’ana, tambaya ce a kan ko ana da isasshen abinci? A halin yanzu, wannan gaisuwa mai cike da nuna damuwa, tana samun sauyi mai ban sha’awa a yankunan karkarar kasar Sin. Dai Yihui, wadda ba ta wuce shekaru 30 da haihuwa ba, ta koma garinta na lardin Jiangsu, domin kula da gandun noma na iyalinta, inda ta yi kokarin kara yawan amfanin gona da kashi 35 bisa dari ta hanyar amfani da injunan noma na fasahar zamani, sai dai kuma mazauna garin sun canza gaisuwar...
    Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma taimaka wajen renon wasu ‘ya’yan Ronaldo guda uku – Cristiano Jr., wanda aka haifa a watan Yuni 2010, da tagwaye Eva da Mateo wadanda aka haifa ta hanyar dashen kwayoyin halittta a watan Yunin 2017.   Ronaldo, mai shekaru 40, ya na cikin kakar wasa ta hudu tun bayan komawarsa kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia, tsohon dan wasan Real Madrid, Manchester United da Juventus...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas. NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi...
    Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
    Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar duniyar wata da aka raba ma wasu hukumomin bincike 7 na kasashe 6. Kana bisa gudanar da bincike kan kasar da na’urorin binciken duniyar wata na kasar Sin, wato Chang’e-5, da Chang’e-6, suka dawo da ita, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na sauran kasashe, sun gabatar da sakamakon bincike fiye da 150. An ce, tsarin da ake bi wajen neman samun...
    A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin ya sauya sheƙa zuwa ADC, ya koka kan yadda gwamnatin Kaduna ba ta kula da haƙƙoƙin ma’aikatan jihar da rashin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu da ƙalubalen rashin tsaro wanda hakan ke hana manoma zuwa gonakansu. Ya soki tsarin rabar da takin zamani na gwamnatin jihar ke gudanarwa ba tare da ta magance ƙalubalen rashin tsaro ba daga tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya, don sayarwa”, in ji Ibrahim. Kazalika, Ibrahim wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ya jaddada cewa; idan aka samu goyon bayan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma goyon bayan sauran hukumomin, hakan zai bayar da damar gyara Gandun Dazukan da ake da su, musamman wajen kare su daga kwararowar hamada. Shugaban ya ƙara da cewa, akasarin noman...
    Kungiyar Hizbullah da Amal na kasar Lebanon sun bayyan amincewar gwamnatin kasar Lebanon wajen kwance damarar kungiyar hizbullah wani abu ne wanda kasashen waje suka fada masu su yi haka, wanda ya yi watsi da diyaucin kasar Lebanon da kuma cikekken iko a kan kasar. Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kasar ta Lebanon sun yi babban kuskre kuma ba zasu taba samun biyan bukata a wannan makircin a suka yiwa mutanen kasar ba. Sun bayyana cewa manufarsu itace, kawarda daga daga cikin kungiyoyi masu kare kasar Lebanon daga HKI da kuma makiyan kasar wato Daesha daga gabacin kasar. Sun ce raunta kungiyar Hizbullah zai mada kasar Lebanon mai mai saukinm mamaya. HKI ta mamaye yankuna masu yawa a kasar...
    Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara. Daga cikin adadin, darajar mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 15.31, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.1, adadin da ya karu da kashi 7.3 cikin 100, yayin da mizanin shigo da kayayyaki shi ma ya kai yuan tiriliyan 10.39, kwatankwacin dalar Amurka triliya 1.44, adadin da ya ragu da kashi 1.6 cikin 100.   A watan Yuli, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta...
    Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba.   Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.   Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da tabbatar da adalci, ladabtarwa, da yakar laifukan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke addabar matasa da al’umma jihar Kano. Gwamna ya kuma yi gargaɗi ga duk masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amuran da suka shafi jama’a, tare da neman izini daga hukuma kafin su shiga irin waɗannan harkoki marasa daɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
    Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544.9. Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi...
    Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi. Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.” Mallam Yunusa ya ce, “Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a  da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata. Ya bayyana cewa makwabta da zuwan jami’an sun taimaka an aka fitar da motar da ke  garejin zuwa waje, amma an tafka asara. Sa’in yace “Muna addu’ar Allah Ya Maida...
    Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki, Barrister Aminu Hussain, ne ya mika rahoton ga Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim. Barrister Hussain ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci, da kuma bin hujjoji, ba tare da son rai ba. Ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinan Sufuri domin karin bayani, inda ya kuma gabatar da rubutaccen jawabi ga kwamitin. Sauran da aka tattauna da su...
    Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai kai jihar ga tudun mun tsira.   Lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Honorabul Aminu Sani Jaji, ya gode wa al’ummar Zamfara bisa nuna kauna da yarda da suka yi mishi, inda ya sha alwashin yi musu sakayya akan haka.   “Dukkanin abubuwan da muke yi muna yin su ne domin al’umma, kuma jama’ar nan ita taga dacewa...
    Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe kiyama. Ya nuna gamsuwa da nasarorin da Gundumar ta samu wajen tattara zakka a masarautar sa. Daga bisani ya karrama Hakimin Yayari, Alhaji Garba Muhammad da Dagaci da kuma Mai Unguwar cikin garin Yayari. A jawabin sa, Sa’in Dutse, Mallam Mahmud Yunusa yace gundumar Yayari ce ta zo na 1 a tattara zakkar kudi yayin da Gundumomin Gantsa da Fagam suka zo na...
    Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’, wato lashe kofin a karo na 10 a tarihi kuma ta ci gaba da jan zarenta na tawagar mata wadda babu kamarta a wannan nahiyar. Nijeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya. A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Nijeriya...
    A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari. Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa da kasuwar Ɗan Magaji saman gadar da ke kan hanyar  Zariya zuwa Kaduna. Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya   An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Awaki kusan sama da 100  suka mutu da kuma kaji kusan ɗari 500 ne aka ƙeyasta sun mutu. Sai dai ba a sami asarar rai ko ɗaya...
    “Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida.  A jawabinsa na fatan alkairi, mai riƙon muƙamin wakilin hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) a Nijeriya, dakta Aleɗ Gasasira, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen yin na mijin ƙoƙari kan cutar hanta, yana mai cewa cutar tana shafar miliyoyin jama’a a ƙasar nan.  Gasasira, wanda ya samu wakilcin dakta Mya Ngon, a faɗin ofishin WHO da ke Nahiyar...
    Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi. Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a garin Agatu da wasu sassan Ƙaramar hukumar Guma da ke Jihar Benuwe. Galma ya kuma yi zargin cewa, ɓarayin shanu da ke afkawa jama’a a Ƙaramar hukumar Agatu sun faɗaɗa hare-harensu zuwa sassan Jihar Kogi. “A ranar 19 ga Yuli, 2025...
    Gwamnatin kasar Amurka ta umurci gwamnatin kasar Lebanon ta kwance damarar kungiyar Hizbullah a kudancin kasar ko kuma ba zata sake maganar tattaunawa da gwamnatin kasar kan samuwar sojojin HKI a wurare 5 a kudancin kasar ba, ko kuma maganar HKI ta dakatar da hare hare a kan kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayyana cewa dole gwamnatin kasar Lebanon ta kwamce damarar hizbullah . A kwanakin baya gwamnatin Amurka ta bawa gwamnatin kasar Lebanon zuwa karshen wannan shekarar ko ta kwance damarar kungiyar Hizbullah ko kuma HKI na da damar yin abinda taga dama da kasar Lebanon. A wani bangare kuma shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabi Beri ya tabbatar da cewa matukar...
    Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
    Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza. Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin. Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza. Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don...
    A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi. Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan. An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka. Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki,...