Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or
Published: 4th, October 2025 GMT
BICTOR IKPEBA – 1997
Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin wadanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997.
ADEMOLA LOOKMAN – 2024
A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake buga wasa a kungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar. Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, inda ya zura kwallo uku rigis a raga, sannan ya taka rawar gani sosai a gasar cin kofin Afirka.
FINIDI GEORGE – 1995
Finidi George danwasan Nijeriya ne da ya yi tashe sosai a shekarun baya a Nijeriya da kungiyoyin Turai. Ya samu shiga cikin zaratan ‘yankwallo na duniya ne a shekarar 1995 bayan nasarar da ya samu a kungiyar Ajad ta Holland, inda ya samu shiga cikin jerin bayan an fadada karramawar zuwa kasahen da ba na turai ba.
A gasar Champions League ta shekarar 1995, Finidi ya zura kwallo tara, sannan ya bayar aka zura kwallo 11 kuma a shekarar ne Ajad ta lashe gasar Champions League da gasar Eredibisie ta kasar Holland da wasu kofuna uku. Amma a shekarar dan wasa Finidi ya kare a mataki na 21 a shekarar 1995.
BICTOR OSIMHEN – 2023
Danwasan kwallon gaba na Nijeriya wanda a yanzu haka yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Galatassary ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Napoli wajen lashe gasar Serie A karon farko a shekara 33, sannan ya lashe wanda ya fi zura kwallo a shekarar ta 2023.
A shekarar ce Osimhen ya zo na takwas a duniya sannan kuma duka a shekarar dan wasa Bictor Osimhen shi ne ya lashe gwarzon dankwallon Afirka mafi kwarewa a shekarar 2023.
NWANKWO KANU – 1996 DA 1999
Shahararren dan wasa Nwankwo Kanu na cikin zaratan ‘yankwallo kafa ‘yan Nijeriya suka dade suna jan zarensu a harkar tamaula. A shekarar 1996, Kanu ya samu kuri’a 14, inda ya zo na 11 bayan ya lashe kofin Olympic da aka buga a Atlanta, da kuma rawar da ya taka a kungiyar Inter Milan ta Italiya.
Haka kuma a lokacin da ya koma Arsenal, tsohon kyaftin din na Nijeriya ya sake samun shiga, inda a shekarar 1999 ya zo na 23 a duniya. Sanan tsohon danwasan na Arsenal ya lashe karramawar gwarzon dankwallon Afirka sau biyu a shekarun 1996 da 1999.
ASISAT OSHOALA – 2022 DA 2023
Mace mai kamar maza, Asisat Oshoala ita ce ‘yarkwallon Nijeriya mace da ta fi lashe kambun gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka. Sannan ita ce mace ta farko daga Nijeriya da ta fara shiga jerin wadanda aka karrama a Ballon d’Or ta mata. Bayan lashe gasar Champions League ne ta zama gwarzuwa ta 16 a duniya a shekarar 2022, sannan ta sake zuwa ta 20 a shekarar 2023.
CHIAMAKA NNADOZIE – 2025
A bikin karramawar ta bana kuma, mai tsaron ragar kungiyar Brighton & Hobe Albion ta Ingila, Chiamaka Nnadozie ce ta samu tagomashi, inda ta zo ta hudu a cikin masu tsaron raga mata a duniya, wanda shi ne matsayi mafi girma da Nijeriya ta taba samu a karramawar. Chiamaka Nnadozie ta lashe kofin gasar cin kofin Afirka na mata sau biyu a 2018 da 2024.
A Afirka dai an samu dan wasa George Weah, dan kasar Liberiya wanda ya taba lashe kyautar Ballon d’Or a duniya, kuma tun daga wancan lokacin har yanzu ba a sake samun wani dan wasa daga nahiyar Afirka ba da ya sake lashe kyautar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ya samu shiga lashe gasar zura kwallo
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000.
Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakaduHaka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ’yan sandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka wato Dakarun Gandun Daji ta Forest Guard.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ’yan ta’adda da ’yan fashi daga dazuka.”
“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewar, za a sake horar da jami’an ’yan sanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗan sandan gada-gadan.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika da ke Jihar Neja.
Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.
Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ’yan sanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.
Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Majami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.
Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.