Aminiya:
2025-11-18@14:04:51 GMT

Mun kama wani mahaifi kan yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa Iraƙi — NAPTIP

Published: 2nd, October 2025 GMT

Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama wani mahaifi yana yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.

Mai magana da yawun hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi

Sanarwar ta ce mahaifin na daga cikin aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane waɗanda aka cafke a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

TRT ya ruwaito Adekoye na cewa an kuɓutar da mutum 24 a yayin aikin bisa jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello wanda aka gudanar bisa bayanan sirri da aka tattara.

Ya bayyana cewa a cikin waɗanda ake zargin akwai wani babban jami’in tsaro, wanda ke cikin masu safarar mutane a Kudu maso Yammacin Nijeriya.

Adekoye ya ce waɗanda aka kuɓutar ɗin yara ne da matasa waɗanda shekarunsu ke tsakanin shekara 15 zuwa 26 waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano da Katsina da Oyo da Ondo da kuma Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi da Sudan da Masar da Saudiyya da Bahrain da kuma Afghanistan.

Ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin cewa sai ta tabbatar an gurfanar da mahafinta a gaban kotu kan yunƙarin safararta da ya yi zuwa iraƙi, in ji jami’in.

Ya ƙara da cewa, wata cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta ce mahafiyarta ce ta rinjaye ta ta yarda da cewa za ta tafi Turai domin yin aiki ta samu daloli.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalar safarar mutane, musamman a lokacin da ake samun yawan ‘yan Nijeriya ke barin ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: safarar mutane safarar mutane waɗanda aka

এছাড়াও পড়ুন:

Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin tana mai ƙaryata labarin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta.

Adeh ta ce babu wani lamari da ya faru ko aka rubuta a koda ɗaya daga cikin wata ƙaramar hukumar da ke cikin birnin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe. Ta ƙara da cewa irin waɗannan labaran karya na iya tayar da hankalin jama’a da haddasa tashin hankali ba tare da dalili ba.

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

Rundunar ta kuma shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan wajen yaɗa bayanan da ba su tabbata ba, tare da samar da sahihan hanyoyin samun bayanai idan wani abu ya taso. Ta ce kare lafiyar jama’a da tabbatar da zaman lafiya shi ne babban aikin da rundunar ta sa a gaba.

ADVERTISEMENT

A ƙarshe, rundunar ta buƙaci mazauna Abuja da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suka ga ya saɓa wa tsaro ga ofishin ƴansanda mafi kusa, ko kuma su tuntuɓi shalƙwatar rundunar ta hanyar layukan gaggawa: 08032003913 da 08068587311 domin samun kulawa cikin gaggawa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025 Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshe 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
  • Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka
  • Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda
  • Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh Gumi
  • Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
  • Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato
  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran