Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina.

A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin ladabi daga magoya baya. “Za mu zartas da dokoki duk lokacin da irin wannan hali ya faru,” in ji Davidson Owumi, shugaban aiyuka na NPFL.

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa

An ci tarar Pillars ₦1m saboda gazawa wajen samar da tsaro, da ₦1m saboda rashin shawo kan magoya baya, da ₦1m saboda jifa a cikin fili da abubuwa masu haɗari, da ₦2m saboda kai hari ga ƴan wasan Shooting Stars da jami’an wasa. Haka kuma, Pillars za ta biya ₦2m a matsayin diyya ga ƴan wasan Shooting Stars da ₦1.5m don jami’an wasa da suka ji rauni.

NPFL ta kuma nemi hukumar ƙwallon kafa ta Nijeriya (NFF) da ta sake duba cancantar wasu jami’an wasa daga wasannin Pillars da Shooting Stars, da na Nasarawa United da Rangers. Duk da haka, Kano Pillars na da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin, sai dai za a iya ƙara musu wani hukuncin idan ba su yi nasara ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano October 13, 2025 Wasanni Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or? October 12, 2025 Wasanni Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka October 12, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Shooting Stars jami an wasa Kano Pillars

এছাড়াও পড়ুন:

Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo

Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko biyu masu zuwa.

Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro

“Eh, tabbas wannan shi ne Kofin Duniya na ƙarshe da zan halarta. Zan kai shekara 41, kuma ina ganin wannan ne lokacin da ya dace na ajiye takalmi,” in ji shi a wata tattanawa a Saudiyya.

Ronaldo, wanda yanzu ke bugawa kulob ɗin Al-Nassr ta Saudiyya, ya ce yana fatan cimma burin zura ƙwallo 1,000 kafin ya yi ritaya gaba ɗaya daga tamaula.

Tsohon ɗan wasan Manchester United, Real Madrid da Juventus, shi ne kan gaba a tarihin cin ƙwallo a matakin ƙasa, inda ya zura ƙwallo 143 a tawagar Portugal.

Ronaldo ya fara buga Kofin Duniya a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta kai matakin kusa da na ƙarshe amma ta sha kashi a hannun Faransa.

A halin yanzu, zaƙaƙurin ɗan wasan bai taɓa lashe Kofin Duniya ba, sai dai ya taimaka wa ƙasarsa ta lashe Gasar Euro ta 2016 da kuma UEFA Nations League har sau biyu.

Yanzu haka, tawagar da Roberto Martínez ke jagoranta tana daf da samun gurbin shiga gasar ta 2026 da za a gudanar a Amurka, Kanada da Mexico, idan ta doke Jamhuriyar Ireland ranar Alhamis.

Ronaldo wanda ya zama ɗan wasan farko da ya ci ƙwallo mafi yawa a tarihin cancantar Kofin Duniya da ƙwallo 41 ya ce ritayarsa ba za ta zama abu mai sauƙi ba.

“Zai yi wuya sosai. Zan iya kuka ma, domin ni mutum ne mai buɗaɗɗiyar zuciya. Amma lokaci ya kusa,” in ji shi a wata hira da ya yi a shirin Piers Morgan Uncensored.

Ronaldo ya koma Saudiyya daga Manchester United a ƙarshen shekarar 2022, inda rahotanni suka nuna yana samun kusan euro miliyan 200 duk shekara.

A watan da ya gabata, mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa samun kuɗi a duniya, yayin da jaridar Bloomberg ta tabbatar da cewa ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya zama biloniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
  • Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
  • Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe
  • Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
  • Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25
  • Wata Gidauniya Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mata A Nasarawa
  • Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
  • Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo
  • Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan  Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari
  • DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma