Aminiya:
2025-11-27@21:17:17 GMT

Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram safarar man fetur a Borno

Published: 28th, September 2025 GMT

Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno.

Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom.

PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata a kamfanin Dangote Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa

An same shi da kwalabe 23 na man fetur da ya ɓoye cikin jaka a lokacin da yake tafiya daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala.

Bincike ya gano cewa yana yi wa Boko Haram safarar man fetur, sai dai wannan karon an yi nasarar kama shi.

Wanda dai ba shi ne karon farko da ake kama waɗanda ke da alaƙa da Boko Haram ba.

A baya jami’an tsaro a Jihar Borno, sun sha kama masu yi wa ’yan ta’addan safarar makamai, abinci da sauransu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram

এছাড়াও পড়ুন:

Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.

Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya.

Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya

Lamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana.

Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar.

Sun kuma sanar da dokar hana fita da kuma kama manyan jami’an da ke da alaƙa da zaɓen.

“An hamɓarar da gwamnatina,” in ji Shugaba Umaro Sissoco Embalo cikin wata tattaunawa ta waya da gidan talabijin na ƙasashen waje.

Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum (WAEF) domin sanya ido kan zaɓen.

Ya ziyarci wasu rumfunan zaɓe a ƙasar kuma ya wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kafin juyin mulkin.

Mutanen da ke tare da shi sun ce yana cikin ƙoshin lafiya, amma ba shi da damar barin ƙasar.

Sojojin suna kuma ƙoƙarin katse Intanet, lamarin da ya sa ake samun tangarɗa wajen sadarwa a ƙasar.

Hakan ya sa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka fara nuna damuwa kan tsaron manyan ’yan siyasa da jami’an zaɓe.

A cikin wata sanarwa, Jonathan da wasu shugabannin Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

“Mun yi Allah-wadai da wannan yunƙuri na daƙile tsarin dimokuraɗiyya, kuma muna kira ga Tarayyar Afirka da ECOWAS su ɗauki matakin dawo da tsarin mulki,” in ji su.

Sun buƙaci mutanen Guinea-Bissau su kwantar da hankalinsu, tare da kira ga sojoji su saki dukkanin jami’an da suka kama domin a ci gaba da gudanar da zaɓe cikin lumana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000