Aminiya:
2025-11-19@07:21:49 GMT

Ana fargabar mutuwar mutane a gobarar tankar mai

Published: 3rd, October 2025 GMT

Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya  sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun.

An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya  zube a kan titin Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagamu a  daidai  wurin musayar hanyar.

Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo

Kakakin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce lamarin ya janyo tashin gobara.

Ya kuma ɗaura laifin haɗarin a kan gudun wuce ƙima da kuma rashin kula daga ɓangaren direban.

Akinbiyi ya ce, har yanzu ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba, amma ana ci gaba da aikin ceto kan gobarar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Al’amarin tashin gobara da wata tankar mai ɗauke da man fetur lita 30,000 ta faɗi man cikinta kuma ya zube da tsakar daren yau da misalin ƙarfe 0100 (1 na tsakar dare), a kan hanyar Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagam a musayar hanya ta babban titin PMB, sakamakon gudun wuce gona da iri da aka samu.

“Sakamakon abin takaicin ya kuma shafi ƙona wata babbar mota da wata mota a gefen hanya, da kuma lalata wata wayar wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga Mowe da kewaye.

“Duk da cewa ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu a halin yanzu ba, jami’an agajin gaggawa na hukumar kashe gobara ta TRACE, a jihar Ogun da Nestle PLC, da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa FRSC da ‘yan sanda suna nan a ƙasa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan kashe gobarar da tada hankula.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abeokuta zuwa Sagamu Gobarar tankar mai

এছাড়াও পড়ুন:

Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba.

Ya bayyana haka ne yayin da yake duba aikin gyaran Filin Wasanni na Jolly Nyame da ke Jalingo a ƙarshen mako.

Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa

Yayin da yake magana da ’yan jarida, Gwamna Kefas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda nemo hanyar da zai amfanar da al’ummar Taraba.

Ya ce: “Zan sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC a ranar 19 ga watan Nuwamba. Wannan sauyi zai amfanar da al’ummar Taraba.”

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiyen bikin tarbarsa.

Da aka tambaye shi ko akwai wani sharaɗi da aka gindaya masa kafin ya sauya sheƙa, ya ce babu ko ɗaya.

Mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar sun nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnan.

Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Muslim Aruwa, wanda ya yi magana a madadin sauran kwamishinoni, ya ce dukkanin muƙarraban gwamnan za su bi shi zuwa APC.

Ya ce: “Gwamna shi ne shugabanmu, duk inda ya je muna tare da shi.”

Aruwa, ya bayyana cewa shiga jam’iyyar da mulkin tarayya zai samar wa jihar ci gaba.

Ya ƙara da cewa: “Wannan sauya sheƙa na mutanen Taraba ne baki ɗaya, kuma muna tare da shi ɗari bisa ɗari.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe
  • Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS
  • An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano
  • Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
  • Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka
  • Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
  • Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba