Aminiya:
2025-10-13@17:56:39 GMT

Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar

Published: 28th, September 2025 GMT

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899.

Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na ƙasar Amurka.

Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara

Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan da suka aikata” a Nijar tun daga shekarar 1899.

A cikin jawabinsa, Lamine Zeine ya zargi Faransa da amfani da ƙungiyoyin da ya kira “na ta’addanci” domin tayar da zaune-tsaye a ƙasarsa da maƙwabtanta na yankin Sahale, inda ya buƙaci mahukunta a Paris da su “tuna tare da ɗaukar alhakin laifukan da suka aikata” tun daga shekarar 1899.

“Tun lokacin da muka fatattaki sojojinsu daga [Nijar] a 2023, gwamnatin Faransa take kitsa wani shiri na ƙarƙashin ƙasa domin wargaza ƙasata,” in ji Ali Lamine Zeine.

Kazalika ya zargi Faransa da “bayar da horo da kuɗi da kuma makamai ga ’yan ta’adda” tare da yunƙurin haifar da “rikicin ƙabilanci” a Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel.

Firaministan na Nijar ya ƙara da cewa mahukunta a Paris sun ƙaddamar da wata gwagwarmaya ta watsa “labaran ƙarya da haddasa husuma” da zummar ɓata ƙasarsa da shugabanninta da hukumominta a idon duniya.

Lamine Zeine ya shaida wa taron UNGA cewa Faransa tana rura wutar rikicin “siyasa tsakanin ƙasata da kuma wasu maƙotanmu,” inda ya ƙara da cewa Faransa tana hana Nijar aiwatar da muhimman ayyukan ci-gaba tare da hana hukumomin kuɗinta sakat.

“Wannan ya haɗa da ƙiyayyar da Faransa take nuna mana wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba ta hanyar hana masu son zuba jari na ƙasashen duniya irin su ADB da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a ƙasarmu,” in ji shi.

Tun dai bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum da sojoji suka yi a shekarar 2023, dangartakar diflomasiyya tsakanin Faransa da Nijar ke ci gaba da tsami.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faransa Nijar daga shekarar 1899 zargi Faransa da

এছাড়াও পড়ুন:

Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice  

Kotun daukaka kara ta Marseille ta tabbatar da soke dokar da ta bayar da umarnin rufe makarantar sakadare ta Musulinci da ke birnin Nice.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, lauyan makarantar, Sefen Guez Guez, ya yaba da nasarar ta uku a jere” tare da bayyana fatan cewa “za a daina tsananta wa wannan makaranta gaba daya.

Takadammar data shafi makarantar ta hana da Rashin haske kan kudadenta, wanda hukumomjin yankin ke zargin makarantar da ta ina take samun kudadenta kamar yadda doka ta tanada.

” An bude makarantar ne a cikin shekarar 2016 a gundumar Ariane, kuma makarantar mai zaman kanta a halin yanzu tana da dalibai 130.

Rahotanni sun ce makarantar, wadda wata kungiya ce mai alaka da kungiyar Musulman Alpes-Maritimes (UMAM) ke tafiyar da ita, ta yi ikirarin cewa tana neman ta bi duk ka’idojin da aka shimfida.

Ana kallon wannan hukuncin da kotun daukaka kara ta dauka a matsayin wata alamar kwantar da hankali a muhawarar da ake yi kan rawar da makarantun da ba su da alaka da addini suke takawa a Faransa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter  A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice  
  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta
  • Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran
  • Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
  • Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka  Rusa A Arewacin Yankin