A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Published: 27th, September 2025 GMT
Rahotanni daga ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati a sararin samaniya na kasar Sin, sun ce da misalin karfe 1 da minti 35 na sanyin safiyar yau Jumma’a 26 ga wata, bisa hadin-gwiwar dan sama jannati Chen Dong dake cikin kumbo, sauran ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 guda biyu, wato Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da ayyuka har na tsawon sa’o’i 6 a wajen kumbon, inda suka kammala ayyukansu bisa shiri.
Yayin da suke wajen kumbon, ’yan sama jannatin biyu sun gudanar da ayyuka da dama, ciki har da saka na’urar kandagarkin tarkacen sararin samaniya a jikin tashar binciken sararin samaniya, da gudanar da bincike kan na’urorin dake wajen kumbon. Kawo yanzu, sau hudu ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 suka kammala ayyuka a wajen kumbon, al’amarin da ya sa suka zama daya daga cikin rukunonin ’yan sama jannatin kasar Sin guda biyu da suka gudanar da ayyuka mafi yawa a wajen kumbo. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: gudanar da ayyuka yan sama jannatin a wajen kumbon
এছাড়াও পড়ুন:
Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya.
Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar.
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun TuraiThompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba.
Gasar nuna ƙarfin ta duniya tana da tsauraran ƙa’idoji, inda ake bai wa ’yan takara damar fafatawa ne kawai bisa jinsinsu na asali domin tabbatar da adalci.
A gasar bana, Thompson ta ƙare a matsayi na biyu bayan kammala fannonin wasanni guda shida da suka haɗa da ɗaga nauyi da sauran gwaje-gwaje a rukunin mata.