2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi
Published: 3rd, October 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.
Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci.
Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin kai kayan agaji Gaza An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin AkkoKwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya faɗa wa BBC Hausa cewa zai bai wa matashi damar tsayawa takara.
Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Amma hadiminsa, Paul Ibe, ya ce ba a yi wa maganganun Atiku kallo na tsanaki ba, an fahimce su ba daidai ba.
Ibe, ya bayyana cewa Atiku yana nufin zai girmama tare da goyon bayan duk wani matashi da ya kayar da shi a zaɓen fidda gwani.
Ya jaddada cewa Atiku bai taɓa cewa zai janye wa kowa ba.
A cewar Ibe, Atiku yanzu ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar jam’iyyar ADC.
Ya ce Atiku na halartar taruka tare da sauran manyan ’yan siyasa, kuma yana bayar da gundumawa don ganin sun yi nasara a zaɓen 2027.
Ya kuma ce Atiku na ganin cewa abin da ’yan Najeriya suka fi buƙata shi ne shugabanci na gari, ba batun yanki ko asalin ɗan takara ba.
A cewarsa abin da ya fi muhimmanci a yanzu, shi ne samun shugaba mai ƙwarewa da zai magance matsalolin ƙasa.
Atiku, ta bakin hadiminsa, ya yi kira ga matasa da mata da su shiga harkar siyasa sosai.
Ya yi alƙawarin cewa haɗin gwiwar zai bai wa matasa da mata muhimmiyar dama wajen tsara makomar Najeriya.
Ibe, ya ƙara bayyana Atiku a matsayin ɗan siyasa na gari wanda zai amince a yi takara ta gaskiya.
Ya ce Atiku ba zai taɓa hana kowa tsayawa takara ba, domin shi ma zai fita filin zaɓe ya gwada farin jininsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Takara
এছাড়াও পড়ুন:
Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba.
Ya bayyana haka ne yayin da yake duba aikin gyaran Filin Wasanni na Jolly Nyame da ke Jalingo a ƙarshen mako.
Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasaYayin da yake magana da ’yan jarida, Gwamna Kefas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda nemo hanyar da zai amfanar da al’ummar Taraba.
Ya ce: “Zan sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC a ranar 19 ga watan Nuwamba. Wannan sauyi zai amfanar da al’ummar Taraba.”
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiyen bikin tarbarsa.
Da aka tambaye shi ko akwai wani sharaɗi da aka gindaya masa kafin ya sauya sheƙa, ya ce babu ko ɗaya.
Mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar sun nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnan.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Muslim Aruwa, wanda ya yi magana a madadin sauran kwamishinoni, ya ce dukkanin muƙarraban gwamnan za su bi shi zuwa APC.
Ya ce: “Gwamna shi ne shugabanmu, duk inda ya je muna tare da shi.”
Aruwa, ya bayyana cewa shiga jam’iyyar da mulkin tarayya zai samar wa jihar ci gaba.
Ya ƙara da cewa: “Wannan sauya sheƙa na mutanen Taraba ne baki ɗaya, kuma muna tare da shi ɗari bisa ɗari.”