Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha
Published: 3rd, November 2025 GMT
Kungiyar likitocin kasar ta Sudan ta kara da cewa; Har ya zuwa yanzu mayakan RSF suna ci gaba da garkuwa da dubban fararen hula a cikin birnin Al-Fasha, sun kuma hana su fita daga ciki.”
Har ila yau kungiyar likitoci ta ce, mayakan na RSF sun kwace motocin da ake amfani da su domin jigilar ‘yan hijira, kuma ta tilastawa wadanda suke kokarin ficewa komawa.                
      
				
Daga cikin wadanda aka tilastawa komawa cikin birnin na Alfasha alhali da akwai albarusai a cikinsu,wasu kuma suna fama da yunwa.
A ranar Asabar din da ta gabata gwamantin Sudan ta bakin ministar ma’aikatar kula da rayu’ar al’umma, Sulaimi Ishaka tana cewa: Mayakan a RSF sun kashe mata 300, sun kuma yi wa mata 25 fyade.
Haka nan kuma ta kara da cewa; mayakan na RSF suna daukar hotunan laifukan da suke aikatawa suna kuma daga ‘yan yatsu alamar samun nasara.
Ishak ta kuma kwantanta laifin da RSF su ka aikata da cewa ya yi daidai da laifukan “Jinenah’ a 2023 da mutane fiye da 10,000 su ka kwanta dama.
MDD kuwa ta bayyana cewa; Dubban mutanen garin na Al-fasha ne suke gudu a kafafunsu, zuwa wani wuri mai nisan kilo mita 60,cikin yunwa da kishiruwa da kuma cin zarafinsu da ake yi.
A garin Qulu dake yammacin Al-fasha ma mutane sun fada cikin mawuyacin yanayi saboda rashin abinci.
Gwamnatin Sudan da wasu kungiyoyin fararen hula masu zaman kansu,suna zargin HDL da cewa ita ce take taimakawa mayakan na RSF da makamai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza November 3, 2025 Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher.
Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waray tarho da takwaransa na Sudan Mohiuddin Salem a ranar Juma’a.
Na farko ya nuna damuwa musamman game da hare-hare da kisan gillar da aka yi wa fararen hula a birnin El Fasher da ke kudu maso yammacin Sudan.
Duniya ta damu matuka a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar tashin hankali a Sudan.
A ranar Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya bayyana matukar damuwa game da rikice-rikicen makamai da ake ci gaba da yi a El Fasher, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula a birnin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci