Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC
Published: 8th, October 2025 GMT
Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025.
Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban.
Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25.
kazalika, NERC ta ce abokan ciniki sun gaza biyan naira biliyan 190.64 na kuɗin wutar da aka lissafa musu, wanda hakan ya sa kamfanonin suka yi asarar naira biliyan 357.89 sakamakon rashin biyan kuɗin wutar.
A cikin rahoton zango na biyu na shekarar 2025, NERC ta ce jimillar wutar da dukkan kamfanonin suka samu a zangon na biyu ta kai ta naira biliyan 909.59, yayin da jimillar wutar da aka lissafa ta kai naira biliyan 742.34.
Rahoton ya ƙara da cewa a cikin kamfanonin, na Eko ne ta yi kowa wajen lissafin kuɗin wutar da kaso 96.67 cikin 100, yayin da na Yola ne ya fi kowanne yin ƙasa da kaso 58.38 cikin 100.
Kamfanonin sun fi ba ’yan kasuwa wutar lantarki
Rahoton ya kuma nuna cewa kamfanonin rarraba lantarkin sun fi karkata wajen baiwa abokan ciniki na kasuwanci wuta a cikin zangon, inda suka fi tura wuta zuwa waɗannan rukunan fiye da masu amfani da ita a gidajensu.
Sai dai rahoton ya ce kamfanin na shiyyar Fatakwal ne kaɗai ya rarraba wutar daidai da yadda hukumar ta amince a lokacin.
Rahoton ya ce kamfanin shiyyar Eko da na Kano sun fi tura wuta zuwa layukan da ke da tsarin kasuwanci, wanda hakan na iya haifar da samun ƙarin ingancin amfani da wuta a waɗannan layukan, yayin da na Benin, Kaduna da Ibadan suka fi tura wuta zuwa layukan da ba su da riba sosai.
Gwamnatin tarayya ta bashin tallafi na Naira biliyan 514.35
Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin biyan bashin tallafi na Naira biliyan 514.35 da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin ta.
“Abin lura shi ne, saboda rashin farashin da ya dace da ƙimar kuɗin samar da wuta a dukkan DisCos, gwamnati ta ɗauki nauyin tallafi na naira biliyan 514.35. Wannan ya nuna raguwar tallafin da gwamnati ke bayarwa da naira biliyan 22.04 (raguwa da kaso 4.11 cikin 100) idan aka kwatanta da zangon farko na 2025 (N536.40bn).”
Duk da cewa adadin tallafin ya ragu a Naira, ya kai kaso 59.60 cikin 100 na jimillar kuɗin da kamfanonin ke bukata, wanda ya fi zangon farko na 2025 da kashi 0.44 cikin 100, inda tallafin ya kai kaso 59.16 cikin 100.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Wutar lantaki na Naira biliyan na naira biliyan wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato
Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al’ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai makura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba.
Ya ce ”Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ‘yar karamar gona ya sayar, mai dan karamin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi kokari su kare mu.
”Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,” in ji Tukur Muhammad Fakum.
Dangane da halin da irin barnar da ‘yan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ”Babu dai abinci, wanda bai taba kwana masallaci ba ya yi, ka tashi ka tafi garin da ba ka taba kwana ba, ka kwana dole. Bala’in ya baci.”
Ya kuma ce lamarin rusa kusa duk wata harkar tattalin arziki a yankin.
BBC dai ta yi kokari jin halin da ake ciki daga bangaren gwamnati da jami’an tsaro, amma hakan ba ta samu ba.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da matsalar ‘yan bindiga ta addaba sosai a shekarun nan, inda suke aikata barna, musamman a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da kuma Kebbe.
Bayan ‘yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji da suke ayyukan su a jihar, an kuma samu bulluwar mayakan Lakurawa, wata sabuwar kungiyar da masu sharhi a kan harkokin tsaro ke gargadin cewa za ta iya zama sabuwar annoba ga jihar da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.
A jihar Kebbi da ke makwabtaka da Sokoto ma wasu ‘yan bindigar sun kai hari a kan jami’an tsaro, a Garin Dirin Daji da ke Karamar Hukumar Sakaba ta jihar.
Wata mazauniyar garin ta ce ”Sun kai hari a kan sansanin sojoji da na ‘yansanda, wanda ke gadi a sansanin sojojin sun harbe shi, kuma nan take Allah ya mashi cikawa.”
Ta kara da cewa ”Daga baya an turo jami’an tsaro, wadanda suka kawo dauki cikin gaggawa, kuma da alama kura ta lafa.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA