Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027.
Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma.

Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya.

Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki?
Wannan shine batun da shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Mutane Suka Dawo Daga Rakiyar Kirifto? DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai

wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya

Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka ya yi watsi da zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana wa Kiristoci kisan kare dangi a arewacin Najeriya.

Da yake jawabi a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, ya ce irin wadannan kalamai kan iya gurbata matsalolin tsaro mai sarkakiya.

Da yake magana tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a ranar Alhamis, Mahmoud Ali Youssouf ya jaddada cewa Tarayyar Afirka ta riga ta fayyace matsayinta kuma ta yi kira da a yi taka tsantsan a cikin harshen da ake amfani da shi wajen bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar.

“Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya,” in ji Youssouf. “Mun fitar da wata sanarwa a fili da ke nuna cewa abin da ke faruwa a arewacin Najeriya ba shi da alaka da ta’addancin da muke gani a Sudan ko a wasu sassan gabashin DRC.”

Musulmai da Kiristoci, dukkansu abin ya shafa inji shi…

Ya kara da cewa tashin hankalin da ake yi a arewacin Najeriya, wanda galibi kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISIS a Yammacin Afirka ke haifarwa, ya shafi Musulmai da Kiristoci.

“Ina ganin lamarin arewacin Najeriya ya kamata mu yi taka tsantsan kafin mu yi irin wadannan kalamai,” in ji Youssouf.

 “Musulmai ne suka fara shan wahala a hannun Boko Haram, ba Kiristoci ba, kuma ina faɗin haka ne bisa bayanai da muke dasu.”

A kwanan baya ne shugaba Trump na Amurka ya bayyana cewa zai doki matakin soji a Najeriya bisa zargin cewa gwamnatin kasar na kauda kai a game da kisan da y ace ana wa Kiristoci a kasar batun da Najeriya ta musanta.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025  Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025  An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana November 15, 2025 Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu. November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi
  • Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza
  • Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan
  • Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  
  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya