Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis.

Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi asarar, sun isa a ɓangaren kasafin kudin kiwon lafiya na shekara a gwamnatin tarayya ko kuma samar da makamashi ga miliyoyin gidaje. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA  October 9, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya.

Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar.

Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau

Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere.

Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar.

Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm.

DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar Funtuwa domin dakatar da motar amma ba a ga motar ba.

Ana zargin direban da fasinjojin motar sun lura da jami’an tsaron da ke kan hanyar, wanda hakan ya sa suka zubar da jakar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yi kira ga jama’a da ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai.

Ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da sintiri da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Ya kuma gargaɗi masu aikata laifi da su guji duk wani yunƙurin tayar da zaune-tsaye, inda ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa
  • Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu.
  • Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba
  • Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa